← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 160

Sashe 17

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"waɗan kananun maganganun yasa  nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so  na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote   suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup  ya dauki  wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa  sannan  ya ɗauki wayar  ya soma magana kasa kasa   "ranka ya dade  aka fada  daga dayan bangaren na turo  da kudaden  yanzu haka yarona na bakin get din  estste " oooooo my  god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad "am sorry  sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali   "haka ne   kana da  fahimta dan   a daidai wannan lokacin ina tare da  shi wanda zai saka hannu   "to kagani sai ka  bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa .." shikenan  a gama karkaji komai  " zan bada umarnin a shigo da yaron  yanzu ya fada yana  canza magana "you have to understand that you should  know that what someone like us can do  in this land be left ,ya maida  wayar zuwa dayan kunnenshi  tare da shiga karamin parlou'nsa ya  bude window dining area  "nasani ranka ya dade  nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi" ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo  tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin "cewa  I will call you later  uhm alright "my dear  ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi "darling  har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade  kamar sauran lokuta karka  ɗauki lokaci mai tsawo  bana son ka  dade ka dawo da wuri   duk yau sati ne fa da dawowarka  "uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba   "really ?  ya gyada mata kai "idan zan dawo zan biya ta itly  "kai dan Allah tayi maganar a shagwa'be "dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal  ta soma tafiya tana farinciki  yana biye daita  abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka "hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb"akwai wani yaro  yana ....
"Okay sir gashi nan ma "yauwa ku barshi ya shigo "okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa ",zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara  ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin  d'aga wayar  gabansa yayi wani irin muguwar  faduwa  yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.

Saurin mik'ewa yayi yana kallon parlou'n kansa na juyawa a matukar zabure amaryarsa ta mike "what happened ?  "gabana ke fad'uwa da matsanancin karfi "gabanka ke faduwa ta maimaita tana kallonsa" ina jin kamar takun mutane "how is there tayi maganar tana kallon kofar parlou'n  tayi maganar a tsorace ganin haka yasa ya riko hannunta "colm down never mind  "what  do You mean never mind ?  tayi maganar a tsorace "don't leave the parlou "ban fahimceka ba  ? " Ina zuwa  yayi foring head d'inta kiss "i think  I will back don't leave the parlou   ya  juya ta riko hannunsa da sauri  "karki damu zan dawo yanzu ya sake rungumeta ya mannata mata kiss  ita dai a sanyaye ta bishi da kallo "meke faruwa ne haka daga gabansa na faduwa yace na tsaya anan na jirasa zai dawo  tafiya yake gabansa na faduwa ya biyo dogon coridor da zai kai  mutun wata kofa data fuskanci hagu ya fito a hankali yana dube dube har inda wata motar take parke yana dubawa gabansa na faduwa wanda duk sanda yaji haka  yasan akwai wani mummunar abu da zai samesa    cigaba da dube dube yayi  a hankali ya juyo yabi wani hanya stil bai ga kowa ba bai ga komai ba, ya tsaya yana waige waige hagu da  dama sannan ya sake juyawa ya nufi kofar daya biyo "Alhaji tanko gote.........."
yaji sauti daga bayansa cak ya tsaya tare da juyowa gabansa na wani irin dokawa a hankali Jaguwa yake daga kafafunsa "waye kai ? tambaya kake ko neman sani ? "duka ya fada cike da tsoro , jaguwa yayi murmushin  "colm don Tanko gote  zaka san komai cikin second daya yayi mgnr  haɗe da ciro bindigarsa daga maajinta  ya soma  gyarawa  yana kusanto inda tanko gote yake tsaye a matukar tsorace yake kallonsa  da bindigar hannunsa alama su shiga ciki yayi masa babu mutsu ya juya Jaguwa  na biye dashi har suka shiga parlou'nsa na uku ya tsaya " ba wani abu ne ya kawoka ba illa kudin da'aka ...
"Dakata kafin wannan kamar baka ganeni ba ?ya girgiza masa kai "Jaguwa yayi murmushin "daman mutane irinka basa iya gane mutane abinda yafi haka ma zaka iya saboda mutun azzalumi irinka ba lallai ne ya zamanto mara mantuwa ba well ba wannan ne abinda ya kawoni ba shiga ka fito dan zuwa yanzu ka fahimceni "sosai ai idan kudi ne zaka samu har sai kabari ni Dai ka barni da Raina da lafiyata "ban soma wannan aikin dan na dauki ran wani ba sai dai a rashin sani amman   kai wallahi  zan iya daukar naka  take jikin Tanko gote ya sake ɗaukar rawa ....

"   muje inda kudin suke jikinsa na rawa ya nufi wani daki suna shiga sanyi ac ya ratsasu buhu ne cike da kudade  daban daban na kasar  negeria  da kasashen ke tare ka ɗauki duk wanda yayi maka "Jaguwa yayi murmushin  yana shafa qirjinshi da hannu "ai gaba-daya zan wuce dasu dan haka   ka soma ɗauka  daya bayan daya "ka bari na bada umarni  a  kai maka  su cikin motarka  tana ina  "ance maka ni karamin kwaro ne karka bata min lokaci ka soma abinda ya kamata kafin na fasa maka kwakwaluwa .....

Darling's

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️09

.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe  ya cika zuciyar Alh tanko gote  mutumin daya shahara a cikin fadin duniya  da aikata masha'a bangaren neman mata  cin amana  ,makirci, son abun duniya  ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda  abun duniya  ,idan  kana son ka  kasance dan ta'adda  mai lasisi da  neman gindin zama acikin kasar nan  nemi  tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne  fayde zama dilan kwaya  da sauransu nemi tanko gote  duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............

Duk  wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon   shekaru yana aikatawa adalilin  connection din da yake da acikin yan siyasa   babu  wani mutun ko  ɗan fashin da makamin  daya taɓa kawowa  rayuwarsa farmaki  ,
hasalima yana jin  sign dinsu ajikinsa  kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi  yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa ,  jiki a matukar sanyaye  ya soma jan buhun  kudi  jaguwa na gefensa  "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki  wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... "

"Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin  da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga  yana dauko  buhun kudi   har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e  hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar  jaguwa .

Jaguwa ya manna  gun a gefen brain  d'insa  "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka  Alh tanko gote ya  kalleshi a  matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi  "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan  kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai  kar kwakwaluwarka tayi  maka  wanann banzan  tunani dan nasan  daraja da kimar  dan adam ba irinka ba wanɗa  yake  danne hakin dan Adam domin son  duniya , a  hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a  gaba-daya sansar  jikinsa yana tunanin "waye shi  wannan  ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani    har suka shigo parlou'n  zuciyarsa na cikin frigici  , yayinda har zuwa  wannan lokacin amaryarsa na tsaye  hankalinta a matukar tashe  tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa  yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama  kyarma ..

"kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki  ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni  gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa  "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan  , sai yadda kika so za'a yi dan  tanko gote  mijin tace ne agurinki  sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan  ya kamata ki san  ko waye wanda ke tsaye a gabanki  duk da idanunki a halin yanzu a makance suke  ,"sunana jaguwa  akaro na farko da wani  a duniya zai  san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "
Chapter 17 · 0% Book details