← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 160

Sashe 31

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" ya  mike  tsaye yana cewa  "zanyi  nazarin  akan haka  yana gama fad'ar haka ya fita daga d'akin ta kwanta sharaf  akan makeken gadonsa tana kuka tana  tunanin yadda zata bar gidan  ta kowani hali .Kai tsaye d'akin ajiya makamansa  ya nufa Inda ya iske  abokansa  da yaransa suna zaman  jiransa a hankali  ya shiga yi musu bayanin Inda kowannensu zai tsaya da zarar sun Isa  airport ya d'auki sama da awa biyu yana  musu  bayanin har sanda  karfe  goma shabiyu  ta buga  ya d'ago yana duba agogon dake d'aure  a tsintsiyar hannunsa  a natse ya d'auke kyawawan idanunshi ya d'aura akan   Scorpio tare da bashi  umarni  "kaje ka siyowa  tanweer  abinci ya lumshe sexy eye's na second biyu sannan  ya Bude ya  jiyo ya Kalli  eku "Kai  Kuma  kaje ma'ajiyin  kudi ka diba ka  siyo kayan  d'anye abinci da duk abinda kasan za'a bukata na abinci ka tabbatar ka siyo "okay boss ".
gbdy  abokansa suka zuba masa Ido kawai suna kallonsa cike da tsananin mamakinsa " kamil ne yayi karfin halin tambayarsa "me za'a yi da  d'anye abinci  Kuma ?""Wa wannan  yarinyar ne ya bashi amsa atakaice yana furzar da iska , duk da  yaki  yarda da  son yarinyar  yake  amman su sun fahimci  matakin soyayyar  da  yakewa yarinyar , soyayya ce me zafi  da  wuyar bari, soyayya ce da mutun bai Isa ya iya barinta ba  cikin dadin  rai    " jaguwa  amman dai ...." saurin  d'agawa  anas  hannu yayi  saboda yasan  me  zai fito daga bakinsa "ya zaka katseshi ka barshi yayi magana mana ?".bazan barshi ba dan nasan maganarsa  iska ce da shirme  ya fad'a yana runtse idanuwanshi tare da shafa sumar kanshi  . kamil yace "kenan mu din yan iskanka ne sannan mashiririta  ? tsuke bakinsa yayi yana kallonsu d'aya byn daya yana girgiza musu Kai  alamun a'a "haka ne mana jubi ya fad'a "ada Kai din mai son a fad'a maka  gsky ne amman me yasa yanzu  duk ka canza bafa ayi haka damu  ba ,ba'ayi damu zamu d'auko yarinyar mutane mu ajiyeta ba meye ma amfanin rike musu yarinya idan kana son yarinyar why not ka fada mana mu san abunyi ?"no no jubi  Sam babu wannan a raina ta ya ma zan d'aukarwa  kaina soyayya  soyayyar ma da diyar minster Sam Sam hakan ba me yiwu bane ?
"me yasa zaka fadi  haka byn zuciya gareka kamar  kowani  halitta "kunga dan Allah ku bar maganar nan haka, bama zan iya wata soyayya ba a yanzu  kawai dai Ina gudar mata  sharrin wannan mutumin ne  me  Katon ciki  ban San wani tuggu zai sake had'a  mata ba  Ina tausayinta Ina Jin kamar zai cutar daita ne Idan na mayar daita  ",saboda zunzurutun qaunar da kake  mata  ba  shiyasa kake Jin tausayinta ",oh my god jubril wai ya kuke min haka ne ?"idan Ina son yarinyar nan wallahi zan fad'a muku dan bamu Saba boyewa juna komai ba , ku yarda bana son yarinyar nan " shiru sukayi  suka cigaba da kallonsa  ba dan sun yarda dashi ba  har ya juya  ya kusan kofar fitar  sannan yace " eku   Scorpio  "zaman munafurcin  me kukeyi  dan Allah ku tashe kuje kuyi abinda na sakaku bamu da lokaci "  da sauri suka mike suna shafa kansu  ."

Cikin  takun  Isa  da Jin shi wani ne  ya nufi  haraban   gidan  hannunsa d'aya soke  cikin  aljihun  wandonsa   eku da Scorpio   suka  fice da  sauri  suka nufi Inda  ya aikesu , yana  nan tsaye yaga fitowar   tanweer   tana  karewa haraban   gidan   kallo  fuskarta d'auke da   murmushin  jin dadi ba kamar   d'azu   ba ,  a kallon   da  yake   mata    ya   lura   hankalinta   na   kan   shukokin     gidan    ne  ,yana  kallonta  ta   cigaba    da    takawa    a hankali   har   ta  Isa   Inda   shukokin suke  tana  shafawa   a hankali  tana lumshe idanu , a  natse   ta  karya  kwana  tabi hannunta  na   hagu  ,cike  da natsuwa ya biyo bayanta , bata tsaya koina ba sai  gurin   fararen   fure  dake shuke   cikin  ruwa  har  lokacin  fuskarta da murmushi , ya  k'araso  ya  tsaya  a bayanta   yana  sauke numfashi, saukar  numfashinsa  yasa ta juyo  a  tsorace  har qirjinta na ta'ba  nashi  saurin  d'auke numfashi yayi qirjinsa  na tsananta  bugu ,  ganin  shine  tsaye  yasa  ta sauke  naunauyen  ajiyar zuciya  sannan  ta juya ta cigaba da kallon fararen  fure  muryarta a sanyaye  tace " ina son fararen fure ko zaka tsinko  min? ta fad'a tana duban Inda yake  tsaye  har lokacin  hannunsa na  soke cikin aljihunsa " kina son fure ne haka ? ya tmbyeta  yana  kare  mata kallo  tsab " sosai Ina qaunar fararen  fure arayuwata  ya  qara taku biyu  yayi kusa  daita sosai yana cewa   "yarinyar da nake so itama  tana matukar son fure " qirjinta ne yayi wani irin bugawa da karfi , taji saukar maganarsa  kamar  saukar aradu ,zafi ta dinga ji a qirjinta tamkar ana diga mata ruwan dalma  nan take ta nemi natsuwarta ta rasa    idanunta na kan furen tace "wacece ita yarinyar da kake so ? ta tambayesa  kwayar idanunta cikin nashi ,bai  bata  amsa  ba duk da ya lura da canzawar da tayi a lokaci  daya  sakamakon  jin yana son wata  dariya taso  subuce  masa dan  yadda  ta had'e rai abun babu sauki kace shi din mijinta ne .

ranta a  'bace ta soma tafiya zuwa wani  bangaren "ke   Ina   zaki  ?itama banza  tayi masa kamar yadda yayi mata  "ba dake nake magana ba kina jina ? still banza ta masa " ki   koma  ciki  kar  na   sake  ganin  kafafunki  kin fito  haraban  gidan nan bare nan. "dan   me  yasa bazan fito ba ? ta fad'a a fusace  tana Jin wani irin zafi mara misaltuwa sannan   ta juyo ta fuskancesa  fuskarta a had'e tamakr ba itace take murmushi a sakwanin da suka wuce  ba , ta rasa dalilin wannan so da take masa  , soyayyarsa me  karfi ce  agareta  ,bata ta'ba sanin  tana  da  kishin irin haka ba sai yanzu daya  furta  yana  son wata ba ita ba  yace baya son zahra sannan baya sonta to wacece wannan daya furta da bakinsa ?   Ido  cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun  juna  kamar ta rufesa da duka ko zata samu sausauci ,k'okarin danne kishin tayi ta sanyawa jikinta  jarumta   "ko bazanje koina ba ka barni na dinga  fitowa Ina ganin fararen  fure tayi mgnr kmr zatayi kuka ,bai ce mata Komai ba   ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita bai tsaya a koina ba sai d'akinta ya bud'e kofar ya turata "iya nan na yarda kiyi rayuwa aciki ko falon gidan nan ban yarda ki fito  ba  idan Kuma kikayi kuskuren fitowa zaki  ga abinda zan miki ya k'arasa maganar tare da  ya janye kofar ya rufe garam , ita duk wannan abun  da yayi  bai dameta ba akan zance budurwa da  yayi  mata shi yafi komai ta'ba zuciyarta  da d'aga mata hankali, tsaki taja yafi sau goma ajere  " Allah! Allah !! ka tsi ...." shiru tayi ta kasa tsine masa shi da budurwar da yake so  ta koma karshen gado ta zauna tare da zuba  tagumi  ."

ya  shiga d'akinsa  ya cire kayan jikinsa ya shiga  wanka ya tsaya  shiru cikin bathtube ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa  yana tunanin maganar abokansa  akan yarinyar "duk suna min kallon d'an soyayya alhalin ba haka bane acikin zuciyarsa ," taimako ai  ba soyayya ce?  ya tambayi kanshi  ya  d'an dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d'aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba   byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya  riga blue wanda a gabansa  aka rubuta  polo  1967  yayinda wondon  da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa  yake , tsintsiyar hannunsa  d'aure da agogon  rolex   ya rufe idanunshi da  glass baki  ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai  kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita,  falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d'akin da tanweer  take ."

 tana Jin shigowarsa amman  taki  d'agowa daga kwance da take  dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa  "ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje  wani aiki me mahimmanci  zan dan dade kafin na dawo batare data d'ago ba tace "a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya ". "ki  daina  damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy  idan lokaci yayi  ya juya ya fara tafiya  cikin hanzarin wannan karon d'akin dake gefen  d'akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d'aya  yayi sautin muryar scopio ya fito dashi "boss komai ya kammala "okay kana iya tafiya   ya fad'a d'akin tanweer  yana cewa "   nasa a kawo  komai na kayan abinci muje kiga kitchen  din ". banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba   ya zuba mata Ido har kusan minti biyar  kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa  yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had'ad'd'en kitchen din ."
Chapter 31 · 0% Book details