Sashe 7
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lumshe idanunta tayi da sauri saboda kamshin turarensa daya sake kaiwa hancinta ziyara wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauke tare da bud'e manyan idannunta, ganin ya kusan kai bakin k'ofa yasa ta tab'e kyawawan 'yan lips d'inta tare da d'an cizawa da fararen hakoranta, ta tsurawa bayansa ido qirjinta na wani irin bugu, bata daina kallonsa ba har ya 'bacewa ganinta sake runtse idanunta tayi tana jin wani abu ajikinta wanda bata tab'a jin irin sa ba game da wani d'a namiji a rayuwarta, shiru tayi tana mai haɗe yatsun hannunta guri daya ta tsakesu , take kwakwaluwarta ta shiga tunanin kalmar daya faɗa mata a lokacin daya shigo dakin "dan ubanki zaman me kike yi ? ki fitar min daga d'aki a tsawace yayi maganar ,ta yaya aka yi ya kawota gidansa ita da take hannun d'an fashi ? ta ɗan zauna a gefen gadon tana zurfafa tunaninta "why did he spoked to me in that manner why? Why zaimun magana cikin tsawa da hargagi haka why? Why?!"a hankali take tambayar kanta kasancewar bata da amsa tambayar yasa ta koma ta nad'e agun cike da damuwa dan ta fara tsorata , babu abinda zuciyarta bata saka mata akanshi ba.
Main parlour'n din gidan ya nufa anan ya tarar da Anas zaune shi kadai yana danna waya ganinsa yasa ya d'ago yana kallonsa tare da sakar masa murmushin gefen baki ,zama yayi akan doguwar kujerar dake kusa dashi yana sauke numfashi "jaguwa!". Anas ya kira sunansa a tsanake yana kallonsa ya ɗan tsura masa ido yana kallonsa batare daya amsa masa ba ,bai damu da rashin amsawarsa ba dan idan da sabo ya saba da halinsa ya cigaba da magana "me yasa ka d'auko yarinyar mutane batare da kayi tunanin abinda zai biyo baya ba duk da nasan kana da dalilin d'aukota ?"ko zaka iya faɗa min dalilin da yasa ka d'aukota ? yayi masa tambayar ajere yana mai sake tsura masa ido "babu wani dalili ya fada a takaice yana sauke numfashi da kyar "karka faɗa min haka jaguwa kasan yadda muka taso babu boye boye a tsakaninmu ka sanni kasan halina nima haka nasanka na san halinka nasan kana da dalilin d'auko yarinyar nan ba wai dan marin data maka ba Anas ya ɗan yi shiru yana mai zuba masa ido domin bashi damar fadar albarkacin bakinsa .
"naji zafin marin data min fiyye da komai yayi maganar yana furzar da iska mai zafi "nima naji zafi fiyye da kai data mara,amman da ajiyarta da zamuyi mai zai hana ka ɗauki fansan marin data maka idan kuma bazaka iya ba ka bani ita yanzu na gama maka daita Jaguwa yaja tsaki kana yace "matsalata da kai kenan son mata Allah yasa kar ...."dan Allah karka min baki, maganar bakinka bata da kyau ,yanzu dai ya zamuyi daita? "a gaskiya na daukota da niyyar aiwatar da abubuwa dayawa akanta cikin muzgunarwa da zan mata har da kusantarta sai dai zuwa yanzu zuciyata tayi sanyi, ina ganin zan sa amaidaita kawai "better ! domin ajiyarta babu abinda zai mana mu da kullum yan oya oya ne ,yanzu haka akwai aikin daya taso sannan wannan mutumin daya kawo aikin gidan minster ya iso "jaguwa bai ce komai ba ya mike shima Anas ya mike suka fito tare zuwa bangaren da makamansu suke anan ya iske sauran abokan halkallarsa da yaransa ,yaransa na ganin shigowarsa suka sake gyaran tsayuwa suna sara masa zama yayi yana duban jakar kudaden da suka shigo dashi daren jiya ,yayinda agbako ya fice da sauri domin kawo masa abun ruwan zafi bai dade ba ya dawo hannunsa rike da cup din coffe ya ajiye akan ƙaramin table din dake gabansa sannan jaguwa ya soma magana a natse tamkar wanda akayiwa dole " eku remo ". "yesssss boss!". jaguwa ya gyara zama yana nuna masa babbar jakar ghana most go "ka buɗe wannan jakar muga adadin abinda yake ciki ", babu mutsu eku remo ya mike ya soma fito da bandirbandir din daloli masu yawa wanda baza'a iya fadar adadin su ba ,"ka raba su kashe biyar duk ku ɗauki kashi day day eku remo ya fad'ad'a fuskarshi da murmushin jin dadi ,ya cigaba da firfito da kudi yayi su kashi kashi kamar yadda jaguwa ya bukata sannan ya umarci kowanensu ya ɗauki nashi kason , bayan kowannensu ya dauka suka kama gabansu dan bawa aminan gurin kamar koda yaushe idan sun yi operation .
a hankali ya dube abokan nasa "kamar ya kuka ga za'a sallami wancan mutumin dashi ? "a kamanta a bashi abinda ya dace inji cewar kamil "okay ka kasa abinda ke cikin wannan babbar jakar sai a bashi kashi biyu "an gama nan take kamil da Anas suka raba kudi , jaguwa ya mike tsaye hannunsa rike da cup Wanda ke dauke da ruwan coffer ya kurbi kaɗan "wannan jakar ku raba kudin ciki kashi biyar sauran kudin akai su inda aka saba kaiwa ya k'arasa maganar muryarsa a raunane "Jubi ya kira sunan Jibril da yake haka yake kiransa dashi " ka biyoni da kason Alhaji tahir .
A tsanake yake d'aga kafafunsa Jibril na biye dashi a baya suka nufi bangaren da'aka wa Alhaji tahir masauki ,kofa biyu suka shige sannan ya sadashi da bangaren da alhaji tahir yake zaune jiran karasowarsa ya shigo makaken parlou'n da jikin bangon yake manne da tangamemen hoton mahaifansa da mahaifiyarsa sai wanda suka yi gaba-daya yan gidansu sunyi matukar kyau sosai ,Alhaji tahir na ganin jaguwa ya ɗan fad'ad'a fuskarsa da murmushi haɗe da dan mikewa yana mikawa jaguwa hannu shima Jaguwa ya mika masa hannu suka gaisa a mutunce sannan ya mikawa jubi hannun bayan sun gaisa jubi ya ajiye jakar daya shigo dashi a gefen Alhaji tahir sannan ya samu guri ya zauna tare da yin shiru, jaguwa ya kalli Alhaji tahir batare daya yi magana ba sai Alhaji tahir ne yayi magana yana murmushin "kasona kenan "ya karasa magana yana buɗe kajar da jubi ya ajiye ? ta'be baki jaguwa yayi tare da cewa "eh a takaice, dariya Alhaji tahir yayi yana jinjina kai cikin rawar murya yace "aiki yayi kyau sai dai naji labarin ance kun wuce da tanwer ? " ya gyada masa kai kawai , "me yasa kuka d'aukota bayan bamuyi haka da kai ba duk da naji yaranka sunce marinka tayi ?kayi hakuri dan Allah kasan yara irinsu akwai tsaurin ido dan Allah ka taimaka ka maidaita "ko na baka ita ku wuce tare ne yanzu ?!". yayi masa tambayar yana aika masa da kallon kasan ido saurin girgiza masa kai yayi "Wa?! ka rufa min asiri yanzu haka a matukar tsorace nake saboda jami'an tsaron dake kan aiki ni dai duk runtsi duk wuya karka ambaceni, Kuma kayi ko'k'arin maida Tanweer dan tana da importance sosai agurina, inada plans me kyau a kan yarinyar Alh.Tahir ya k'arasa maganar yana murmushi saboda tuna shirinsa akanta da dukiyar mahaifinta. "Bansan plans d'inka a kanta ba amma sai na kammala tawa buk'atar intakaice maka sai nayi ra'ayi zan maidata" Jaguwa yayi maganar cike da isa sannan a dake yana girgiza k'afarsa daya . Alh.Tahir ya had'iye wani wahalallen yawu sanin waye Jaguwa yasan bai isa yaja dashi ba. "To naji amma komai zaifaru a rufe sunana dan Allah". Jin zancen Alh.Tahir yasa jaguwa murmushin gefen baki irin nasu na marasa mutunci da tsoro. "Hmm, dole kuwa inda alam yayi bolo ka shiga ciki dan informer yafi kowa laifi a cikin halkallar bare ma babu abinda zai faru kaje kawai Alhaji tahir". bai dade ba ya wuce "kaga mutumin nan da shegen wayo inji cewar jubi "shi baya son a saka shi cikin matsala amman ya iya son kudi nifa ya bani mamaki ban ɗauka zai zo da wuri amsar kasonshi ba "manta dashi kawai ya d'auki wayarsa ya kira agbako cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa " kaje ka ɗauki kudi a ma'ajiyi ka siyowa yarinyar nan kayan ka hado da hijab da abinci ya amsa da "angama boss sannan ya juya da sauri , agbako bai fi minti talatin ba ya dawo hannunsa rike da fararen laidodi guda biyu ya ajiye a gefen Jaguwa sannan ya juya har ya fara tafiya ya dawo "boss mutanen daka saba rabawa tallafi duk safiya sun hallara fa , kai Jaguwa ya gyada masa yace "ka bada umarnin buɗe musu get agbako ya sake juyawa adaidai lokacin da Jaguwa ya mike daga zaunen da yake yana kallon jubi "muje na sallami mutane nan ,atare ya suka fito inda suka iske mutane unguwar har ma da makwaftan unguwar tsaye suna jiran fitowarsa tanwer dake zaune a dakin kamar an tsinkareta ta mike ta tsaye a bakin window ta kai hannunta ta ɗan zuge labule nan idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye yana rabawa mutane kudi har sanda daya gama ya juya ya nufi wani ɓangare tana tsaye ,lumshe idanunta tayi sannan ta dawo ta zauna qirjinta na bugawa da matsanancin karfi "wannan mutumin na da tsananin kirki da tausayi , irin mijin da nake muradin mallaka ne a rayuwata , "ina ma zai soni ? tayiwa kanta tambayar tana kallon celling d'akin yayinda take zuciyarta ta bata amsa da" ai naki ...."yes is mine and me alone ta furta tana murmushi haɗe da gyara suman kanta ..
tana nan zaune tana tunani ya shigo d'akin hannunsa rike da white lailon's guda biyu ya cilla mata daya a saman cinyarta ya d'ago a mutukar tsorace ta zuba masa ido gabanta na faduwa tana kallonsa ya karasa gaban mirrow ya ajiye laidar abinci ya juya har zai fita , sai Kuma ya tsaya batare daya juyo ba," ki ci abinci ki canza kaya, i don't want to see you like ....ya katse maganar da cewa "nan da mintuna talatin zan sa a maidake gidanku". yana gama fadar haka yasa kai zai karasa ficewa daga dakin yaji sautin muryarta da duk sanda tayi magana yake kashe masa sansar jiki saboda zakinta da Kuma yadda sautin ke fita"No I am not leaving here, har sai ka faɗa min dalilin daya sa na dawo hannunka daga hannun yan fashi, and if you are the robber man daya d'aukoni daga gidan iyayena ina son sani?