← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 160

Sashe 134

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali suke tafiya acikin mota suna cigaba da hira har suka karaso bakin get din hospital din  tanwer suka shigo kai tsaye cikin haraban hospital din kasancewar makeken get din a bude yake "me kuma zamuyi a hospital?kasa ido mana kaga ikon allah ,
"hope ba wani ne cikin yanuwa bashi da lafiya ba ?
idan wani ne me zai kawo mu nan bayan ga sadiq wata nazo gani ya karasa maganar yana kokarin  parking din motarsa a inda aka tanada domin ajiye motoci ya soma kokarin fitowa yana duba agogon dake daure a hannunsa daya  da rabi adaidai yana gama fitowa lokacin tanwer suka jero tare da doctor muyis da fadela abokiyar aikinta yayinda doctor muyis ke  faman yi mata naci da magiya ."
suka tsaya a bakin motar tanwer fadela na cewa "haba tanwer ki tausaya masa  mana ki dan samar masa gurbi azuciyarki ko babu yawa ne a soyayya baa son ka zurfafa kiyayya "barta kawai fadela só take ta kasheni , tanwer tayi murmushi "haba fadela  wallahi a halin yanzu  bazan iya wahalar da kowa a soyayya ba  ,kai kuma dr allah bazai sa na kashe mutun ba ."da wahalar da zuciyata da kike ai gara ki kasheni zan fi bukatar mutuwa akan wannan rayuwar ko ba haka fadela? "aa bazaa yi haka ba dr ta dai amince cikin sauki da dadin rai mu sha biki ba sai an kai ga haka ba ,ta fada tana juyawa ni zan wuce ana jirana naso ma muje tare da tanwer ne amman yanzu ina cewa muje zata fara dojewa ita dai ban san abinda mutane suka mata ba da bata son shiga cikinsu ? ta nufi gurin motarta tana magana ta bude ta shiga gidan baya ta zauna tanwer taji wani abu acikin maganar fadela wasu kuma sun bi iska  tayi murmushi  har fararen hakoranta suka bayyana tana kokarin sake cewa wani abu kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya harde hannayensa a qirjinsa  rikitattun idanunshi akanta yana kare mata kallo ,kasa magana tayi nan take kuma ta sanyawa jikinta natsuwa ta shiga hankalinta hatta murmushin dake  kwance akan fuskarta ta dauke qirjinta ya shiga bugawa da karfi tamkar zai fasa qirjinta ya fito waje cigaba da kallonta jaguwa yayi fuskar nan nashi babu annuri sam "ya kika yi shiru madam dina inshaallahu ki fadi min  abinda kike son nayi ki soni ,wallahi  ni magana dake ma kadai yanasani farinciki , bata kallesa ba ta furta "dan allah dr muyis kayi shiru na shiga rudani né fadela data shiga motarta kam batasan wainar daake toyawa ba sai dai ta dan leko ta side din da take zaune domin tayi musu sallama direbanta yaja suka wuce .
a hankali  jaguwa ya soma taku cikin isa da izza hannuwansa duka zube cikin aljihunsa yana kokarin karasowa inda take ai nan take zuciyarta ta shiga karkarwa ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️38

......tafiya kawai yake fuskarshi babu annuri kana kallonsa zaka fahimci zallar 'bacin ran dake tattare dashi ,ran nan nashi yayi baki yayi kololuwar 'baci yana gama karasowa inda take tsaye bai kalli dr muyis ba ya kai kyakkyawa hannunsa ya rike tsintsiyar hannunta gam cikin nashi yana tsareta
da rikitattun idanunshi masu matukar firgitawa da hargitsawa mutun lissafi , a qalla ya dauki minti goma yana tsaye yana kallonta zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ,yana tunanin abinda ya kamata yay mata ,wata zuciyar ta bashi shawarar
ya hau dukanta yana yaryarfa mata maruka ko hakan zai sa yaji saukin zugin da zuciyarsa ke yi ,yayinda wata zuciyar ke gargadinsa ba dan jin tsoron abinda zai faru ba sai dan kasancewarta yarinya .
wasu minti goma suka shud’e yana tsaye yana kallon kyakkyawar fuskarsa , kafin daga baya ya jata zuwa gefe wanda tazaransu da dr muyis bai fi taku hudu ba kuma tana da tabbacin duk abinda jaguwa zai fada mata tabbas zai ji ,ita a tunaninta ma gurin da yayi parking din motarsa zai kai ta ko cikin motarsa sai taga sabanin haka, ganin zai soma magana cikin zafin rai tace “muje daga can ta nuna masa nesa da inda suke komai zai fada mata babu me ji ,amman da yake ransa a bace yake uwa uba kuma ga tsabar taurin kai sai cewa yayi “bazaa je
ba anan nayi niyyar magana banga uban daya isa yasa na kara taku daya daga nan ba tukun ma me kike yi tare da wannan mutumin ? qirjinta yayi mugun dokawa da matsanancin karfi har ta kasa bude bakinta,hakan ne ya bashi damar cigaba da magana "bakin san Idan mutane suna ganinki da maza kala dabam dabam ba zasu dauka kmr baki da kamun kai ne ba? “wallahi mutane zasu daukeki useless idan kika cigaba da kulaye kulayen maza “stil shiru tayi ta kasa magana duk da bakinta abinda yake son yi kenan ta tsaida shi daga abinda yake fad'a ."

hannunta dake cikin nashi ya sake matsewa sosai yana sake tambayarta cikin zafin rai "me yasa kika tsaya dashi ?"Ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "ban sani ba kai ne dai kake ganin kamar bani da kamun kai ,amman kowa agurin nan yasan ni wacece,sai abu na gaba ,adnan am not useless your sister’s your aunty’s I wont put your mother coz I use’s to respect mum, but your sisters are useless , your Aunty’s are useless even the children that you wont to born they wil be useless inshaallahu, in allah yaso ya yarda sune useless banice useless ba idan kaga dama karka kara zuwa inda nake ko yanzu ai ban kiraka ba kona kiraka ne da zaka fada min mgnr banza .”?
Shiru yay yana kallon karamin bakinta da take motsawa a hankali tamkar ba daga cikin zafafan magana ke fitowa ba yana jin wani irin zafi daga cikin kasan zuciyarsa idan yace bai ji zafi da ciwon maganarta ba yayiwa kansa karya "ita kuwa wani sanyi dadi ne mai tattare da farinciki ya lullubeta alokacin daya, duk da taji zafin kalamansa amman kishinta daya nuna qarara yayi mata dadi kamar tayi masa dariya mai hade da kukan zafin furucinsa amman tsoronsa ya hanata ,yanayinsa kawai zaka kallo ya tabbatar maka da abinda ke dawainiya dashi gbdy Kishinsa ya fallasa abinda ke cikin zuciyarsa ,yana mugu mugun qaunarta amman tsabar miskilanci da jin kai ya hanashi fallasa muradinsa .”

“Tanwer I want to ask you a question tayi shiru tana kawar da fuskarta gefe ya kai hannunsa ya dawo da fuskarta garesa “why did you abused my sisters and my aunts ,Since when me and you meet each other which day did i abused you da zaki sako sister’s dina cikin magana?adnan ka kirani da …..”shiiiiii !
Yay saurin katseta qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske "abinda nake so dake wannan ya zamo shine karonki na farko kuma ya zamo na karshe da zaki sake kula wannan mutumin koda kuwa gaisuwa ce bana só idan .."
"Idan na sake kulasa fa me zakayi?" tayi masa tambayar cikin karfin hali tana kallon tsakiyar idanunshi at the same time kuma qirjinta na luguden bugu " wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa "tmbyta abinda zanyi kike ko kuma zaki Kibi  umarnina ?"bazanbi umarninka ba tunda ba aurena kayi ba ,baka aureni ba kaga ai bazaka hanani kula duk wanda raina yake so ba ,ko kai mijina ne ?ta sake jifa masa tambayar datasa zuciyarsa shiga tashin hankali ,magangunanta fa
sun doki zuciyarsa da kunnuwansa sosai sannan sun shiga kai kawo acikin kwakwaluwarsa sai yaji kamar ta sake kunno masa wutar kishinsa ne da yake ta kokarin dannewa acikin zuciyarsa ransa a matukar bace yace "kema a she kamar sauran mata kike da rashin mutunci ?kamar ta girgiza masa kanta alamun aa sai kuma ta fasa tunda tasan tayi rashin mutunci "ko da yake bai kamata nayi mamaki manyan maganganunji ba ,idan dai tsiwa da rashin kunya da rashin mutunci ne gidan nazo ko ba haka ba ?"
"Ban sani ba Karka sake kirana da wadan kalmomin bana.."Bata kai karshen maganarta ba ya dalle mata baki da dayan hanunsa da sauri ta dafe bakinta saboda azabar da taji ya ratsata nan take idanunta ya canza kala ta dan juya bayanta nan taga dr muyis tsaye ya kafesu da idanu yana Kallonsu yanayinsa
da alamun tashin hankali dukkanin alamu sun nuna yaji abinda ke tafiya ,daga can gefe kuma anas ta hango ya harde kafafunsa ya tallabe habarsa da hannunsa daya shima yana kallonsu ,numfashi ta sauke sannan ta dawo da kallonta garesa ta tsura masa idanunta cike da kwalla saboda har lokacin tana jin zafi a abakinta ."
Chapter 134 · 0% Book details