← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 160

Sashe 144

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  bayan wasu mintuna aka hadashi da dcp  "hello ko zan iya sani da wa nake magana?ba lallai kasani ba amman  ni nasanka da dade wa na kira ne na  nasar maka cewar "mutuwar honorable abdulaziz abokansa guda biyar ne suka hadu suka kashesa suka binne gawarsa a gidan dayan daga cikinsu ."
shiru dcp  yayi domin dai yasan da labarin a halin yanzu ma ana kan bincikensu akan haka sai dai ba'a rigada ansan inda gawarsa take ba "to shi yanzu me zai yi da wannan case din ? shi da yake son ganin bayan jaguwa da tawargarsa me zai sa ya sanya kanshi cikin binciken akan matacce ? dan haka a matukar a fusace yace "shshan banza ni me zanyi to akai da ka kirani ? "Me yasa bazaka kira babban headquarters na abuja ka sanar dasu ba  tunda case ya koma hannunsu idan ka samu labarin inda babban dan fashi da makamin nan  mai suna jaguwa yake ka gaugauta kirana zamu baka lokacin mu har ma mu hada maka da makudan kudade amman akan matsalar mataccen karka sake kiran mu a waya kit ya katse kiran yana gama fadar haka ."

Shiru jaguwa yayi yana tunani abun yi yana duban anas  daya tasa shi gaba da kallo kamar shine dcp din kafin daga baya ya sake Kiran  layin  aka dauka tare da cewa "da me zan iya taimaka maka ?amir ali ne yake magana wanda ya kira yanzu ka sake hadani  da dcp  ,okay ka dan rike waya ya mike cikin hanzari ya sake shiga office din dcp alokacin yana tare da yaronsa suna tautaunawa akan scorpion"yallabai  mutumin dazu ne yake son magana da kai "batare daya dago ya kallesa ba yace "kace masa bana nan okay sir ."ya  dawo yana cewa kayi hakuri a she baya nan" shin ka san ..."kafin jaguwa  yace wani abu dansanda ya katse kiran ya koma mazauninsa  ya cigaba da ayyukan gabansa ."

Dcp kuwa sai faman tsaki yake ja "aikin banza
kawai ko ina ruwana da batun mutuwar honorable abdulaziz, kaje can ka kai rahontonka ga masu bukatar bincike akan mutuwa , ni nan labarin yadda zan kama jaguwa nake nema ba wani mutuwa ba , yaronsa asp isa dake zaune a gabansa  yace "yallabai me yasa zakayi haka ai da ka tsaya kaji a ina yasan batun inda aka binne gawarsa "kai bazan tsaya naji komai ba , da jin wannan maganartasa  kasan wata qullaliya ce akasa ,amman kuma idan gaskiya ce zai yi matukar mana amfani "dan allah ka rufe mana baki babu ruwanka kaji da karamin matsayinka idan ka kai wannan matsayin sai kayi aiki fiyye da wanda mukeyi a yanzu ."

tsit asp isa yayi saboda ya fuskanci mai gidan nasa ya dau zafi da maganarsa dcp ya cigaba da Magana "wani bayani kuka samu a bakin yaron jaguwa "?har yanzu  dai shiru sir yaki  yace  komai "kun matse shi sosai kuwa ? sosai kuwa yallabai daga jiya zuwa yau din nan  ba karamin izaya muka masa ba gbdy mun canza masa kamani amman yaki bamu cikakken bayanai akan jaguwa sai ihun azaba yake ."
"Baku matse shi da kyau ba ,ku matseshi sosai karku masa da wasa idan yaki magana zuwa gobe kusashi  a under ground idan shima yaki magana ku sanar min zan masa izayar da bakinsa zai bayyana mana sirrin komai na gidan jaguwa ai tunda ya shigo hannun magana ta kare sai munga bayansu daya bayan ".
"Okay sir !
Ya fada tare da mikewa tsaye cike da girmamawa
har ya kai bakin kofa dcp ya dakatar dashi ta hanyar  kiran sunansa" Asp isa!"Yes sir ya fad'a tare da juyowa ya Kame agabansa "Kusa ido sosai akan scorpion domin su din barayi ne masu  matukar wayo da dabaru kala kala da zasu iya komai domin kubatar da kansu  dan haka ku maida hankali sosai ku qara matakan tsoro mai karfi yanzu harinmu na gaba cikin manya abokansa ne dama wannann yaron nasa yace wani abu ne da yanzu mun san ta inda zamu fara aiki lallai sai mun kama jaguwa da gbdy yaransa a mace ko araye inshaallahu ma a raye zasu zo hannu sir ya juya ya bar office din ."

Jaguwa  ya furzar da iska yana cizan lip's dinsa da karfi "wannan itace damar da nake son nayi amfani daita, idan  bata samu karbuwa ba bansan me zan  yi ba kuma?  yayi maganar a fili ya zagaye dakin .
anas ya matso shi yana cewa "karka damu zaka yi nasara ka sake yin wani tunani akai  ko kuma ka kira  number office din commissioner kai tsaye  nasan shi bazaiki amsar maganarka ba ,take zuciyar jaguwa ta amince masa da hakan,ya  kira da wani layi ya nemi yayi magana da  commissioner ai kuwa kai tsaye aka hadashi da commissioner wanda shima alokacin yana tare da mataimakinsa A kwantagora ya soma magana  a natse  "ko zan iya sani dawa nake magana"?

"Kana magana da Amir ali ne batun mutuwar honorable abdulaziz ba hatsari yayi ba kashesa akayi
"taya akayi kai  kasan ba hatsari yayi ba kashessa akayi "? shikenan idan zaka bani dama sai mu hadu zan baka bayanan komai domin ina da hujoji a hannuna commissioner yay shiru yana sauraronsa tare danna record acikin wayarsa "duk naji bayaninka yanzu daga ina kake magana ?"
"daga kano !

"to me zai hana ka sanar da jami'an dake aiki a kano ko  abuja ?"ai gani nayi anan lagos honorable abdulaziz din yake daga nan aka fara bincike kafin case ya koma abuja kuma ni yanzu haka ina airport zan taho lagos daga lagos Australia zan tafi jirgina karfe bakwai zai tashi "to shikenan ka bani  numbarka zan nemeka idan ka shigo ,"Aa yallabai ni ne zan kiraka ka bani number wayarka ,to shikenan ka rabuta commissioner ya karanto ma jaguwa numbersa yana maimatawa anas kuma  na rubutawa  sannna ya katse wayar ."

commissioner ya kalli mataimakinsa yana sake yi masa bayani abinda jaguwa ya fada masa "ya kake gani zamu yi yanzu "kwanta kwata yallabai ni ban yarda da wannna mutamin ba "taya yasan labarin mutuwar honorable abdulaziz da mutanen da suka kashesa da inda aka binne gawarsa byn har yanzu ana kan bincike ne   baa gano inda gawar take ba su kansu abokansa sunki amsa laifin su suka kashesa dan haka ni ban yarda dashi ba karka sauraresa."
“amman kuma gaskiya ya fad'a mana tunda duk abinda ya fada haka ne kuma da alamun zai yi matukar yi mana amfani," nan dai suka cigaba da tautaunawa shi dai commissioner ya yarda da maganar jaguwa kuma idan dai har ya kirasa zai bari su hadu ya bashi bayanai akan komai bayan mataimakinsa ya tashi ya koma office dinsa kira ya shigo wayar hannu ta commissioner yana dauka ya fahimci mai magana "me kuma kake  so daga gareni ?

"so nake idan na shigo mu hadu da kai kai kadai na baka sheidu masu matukar mahimanci idan kuma hakan  bazai yiwu ka  hadu dani kai   kadai ba shikenan  sai na tattara sheidun na watsasu a ruwa daman yanzu adalci yayi wuya ayi sharia a lahira  a inda babu wanda ya isa sai allah ,ya tunhumeku akan abinda kukayi ,ni da zaku fahimceni ma bayan wannan mahiman bayanan akwai wasu akan  masu safar miyagun kwayoyi wanda dayansu polisawa ne duk zan baka amman kai kadai ,dan da kai kadai kawai na yarda ."To shikenan ai kuwa daka taimaka mana yanzu dai  ka  sake kirana nan da awa uku  zan fada maka inda zamu hadu jaguwa najin haka ya dunkule hannunsa yana jin dadi ya katse kiran  ya zauna  yana cewa "shikenan tarkona bai kama dcp ya kama commissioner  ,sai yanzu hankalina ya kwanta"ya karasa maganar yana sakin murmushi.

“ya  yarda zaku hadu kenan ?da alama tunda yace na kirasa byn awa uku zai fada min inda zamu hadu kasan  fa  shi wannnan commissioner din rikitaccen tsoho ne ina ganin ma a karshen shekara nan zai yi  ritiya ,zan bika muje tare ."baka da hankali  bakaji nace babu inda zakabini  ba , ance maka haduwa da commissioner abu ne me sauki ? ka barni kawai naje ni kadai idan ma matsala ce ta tsaya iya kaina ban da kai  ya karasa maganar tare da mikewa ya nufi bathroom dan lokacin sallah laasar yayi ."

Bayan jaguwa ya fito Ana's  ya tashi ya shiga bai bata lokaci ba ya fito alokacin jaguwa ya tada sallah ya karaso ya bishi jim'i byn sun idar  suka sake zama sai lokacin jaguwa ya tuna da jama'arsa dake kofar gida gashi ya soma jin alamun hadari ya kuma san muddin bai bada sakonsu ba anan zasu wuni har sai sun ga fitowarsa "anas kira sky kace ya sallama mutanen dake waje ,numfashi ya sauke "gsky kam dan wasu da wannan kudin daake raba musu kullum suke cin abinci batare da bata lokaci ba ya kira layin sky ya bashi umarnin ."
Suna hira suna duba lokaci a hankali har akaci awa daya acikin awa  ukun  da commissioner ya bayar dan haka  suka cigaba da hirar yadda jaguwa zai hadu da commissioner "tunanina idan na kira shi  zai ce mu hadu dashi  a hotel ko gurin shakatawa ba lallai mu hadu dashi a gidansa ba , nima gaskiya bazan so ku hadu a gidansa ba akwai hatsari gara ku hadu a waje  zai fi ,muna haduwa a yau ina tabbatar maka a yau scorpion zai fito domin bazan sausauta masa ba."
Chapter 144 · 0% Book details