← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 160

Sashe 62

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka sausauta yalla'bai wannan ba abun tada hankali bane ya fad'a yana mikewa tsaye ya kakkabe hannunsa "duk wani shirina na rigada nagama tsarawa aikatawa ce kawai ta rage min adadin mutane da zan yiwa fashi   a lisafe suke  ya fad'a tare da yin  tsalle ya rike kerfe yana sama da kasa jikinsa na budewa  " Ku daina bincike da bin kwakwafi akaina dan babu wani abu da zai amfana muku dan  bazaku ta'ba samun komai ba sai darasin rayuwa kawai .
"ka kiyaye kanka dan randa zaka shigo hannunmu zakayi da kasani  ....
"daga murya fa ba komai bane agurinmu, masu laifi ake d'agawa murya Kuma kunsan Inda suke , dcp yayi  shiru yana furzar da iska sannan yace  "me kake bukata zamuyi maka muddin zaka dawo da yarinyar nan ?"murmushin gefen baki yayi nasan karshe abinda za'a  sake tmbyata  kenan "me yasa sai akan diyar minister zaku kasa zaune zaku kasa tsaye ?"oho a she fa ita diyar me kudi ce ko ?
"ba wannan muka tmbyeka  ba abinda kake bukata muke so jin ",ku shiga cikin gari akwai Yara irinta bila'adadin da akayi garkuwa dasu wasu sun mutu wasu suna raye zaku iya zuwa ku taimakawa  wadan da suke raye, sau daya kawai kayi aikin alkhairi idan Kuma zaka had'a Kai dani  ni din simple man ne ya karasa mgn  tare da janyo rigarsa ya saka "kayiwa Allah karka manta  kaifa Muslim ne"
"cikakke kuwa "to ka dawo da yarinyar  nan "naji kubani lokaci na kammala abinda nake a karshe ma ni ne zan nemiku ba sai Kun Sha wahalar nemana ba  yana gm fad'ar haka ya katse Kiran duk ya hada gumi tunaninsa Inda suka samu numbersa  Kai tsaye ya fito cikin tsananin damuwa d'akinsa  ya shigo  ya wuce  bayi ya tsaya cikin bathtube ya Kuna shawa a hankali ruwa ke sauka ajikinsa  sosai ya shiga kogin tunani"Ina suka samu wannan number sosai kwalkwawarsa ta shiga lissafi ya dade ruwa na sauka ajikinsa  sannan ya fito ya goge jikinsa ya zira jallabiyar  deep  blue ya fito falo ya goya hannuwansa duka abaya  yana zariya  ko cikakken minti goma bai yi ba  anas ya shigo yana murmushi "mutumina sarkin soyayya wannan yarinya  fa  tayi win ... tayi galaba akanka yanzu muka hadu da  pretty take fad'a min wai wulakanci kayi musu akanta "ba'a akanta bane  kawai yanzu zinar ce bana so "
"karka wani waske  kana  fa son yarinyar nan   da zarar anyi magana ka kama wani Shan kamshi amman  kullum cike da  yi mata biyayya kake  da tattalinta  "na sha fad'a maka  babu soyayya a tsakanina daita kuma karka dameni da  wannan maganar dan a halin yanzu bashi bane  a gabana ba kwakwaluwata na bukatar tunani dan gano wani Abu me mahimmancin  " "tunanin me zakayi ?Kuma me zaka Gano byn mun gano maka , munyi shekaru sama da goma tare taya zan kasa fahimtar abinda kake so Adnan  ?  tsaki yaja "ka daina  fad'a min haka nace ba  sonta nake ba bana  sonta kawai dai  tausayawa ce , taya za'a yi nayi soyayya daita gbdy zuciyata ta mutu babu wani  abu soyayya bayan ta ahlina ,wallahi Ina balain tausayinta ne kuma ko tabar gidan nan zan cigaba da tausaya mata saboda na amshi  budurcinta wanda yake da wuyar samu a wannan  zamani  yarinyar ta  had'u  ciki da wajenta tunda na Kusanceta na kasa cin kowace mace   ilarta  rashin kunya da  rashin  tarbiya .

"anas! Jaguwa ya kira sunansa  gbdy  yarinyar nan bata da manners  "gaban anas ya fadi sakamakon ganin tanweer a  tsaye a bayan jaguwa rungume da hannuwanta anas ya Kai hannunsa zai nuna masa bayansa jaguwa ya buge masa hannun "Kaine ka kawo maganar dan haka ka bari na gama kafin ka shigo da wata "sam sam yarinyar  bata da tarbiya iyayenta basu koyar  daita yadda ake girmama babba ba  da kace mata cas zatace maka kul , ko da yake taya zatayi tarbiya haihuwa tayis reinon tayis  tashin turai kasan baza'a  sameta da cikakkiyar  tarbiya amman Misali ace  da gaske   zan yi  soyayya da  wata mace  da itace  farko  kodan disvarging  dinta da nayi amman bazanyi ba yana gama fad'ar haka ya juya da niyyar  barin gurin  turus yayi zuciyarsa na karkarwa sakamakon idanunsu da suka tsarke cikin juna."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️20

.....juyowa  yayi  ya  Kalli  anas dake   tsaye  a bayansa yana tmbyrsa   da  kwayar  Idanunshi  dake  cike  da matsanacin firgici  ko  taji  abinda  ya fad'a , shima da  kwayar  Idanunshi  ya bashi amsa  alamun  taji  komai daya fad'a  a yanzu  ." ya subhanallah ya   furta  a  kasan  makoshinsa  yana  mai  sake juyowa  Inda take  tsaye ,   tana  nan  tsaye kmr wacce  aka  dasata  agurin sai dai zuwa  wannan lokacin babu komai acikin kwayar idanunta sai  tsananin  firgici  dake  tattare  da  tashin  hankali .
  Muryarta  na  rawa  tace  "me naji  ka  furtawa  abokinka yanzu ? "mafarki  nake
ko  kuwa  karya ne ? "
taku  d'aya  ta K'ara  tana sake  cewa "kace  karya  kunnuwana suka  jiyo  min ba  gaskiya ba ?" shiru  yayi  yana  kallonta zuciyarsa na  wani  irin  rawa  dan  gbdy  ya gama  rikicewa   bai  so  taji  abinda ya shiga tsakaninsu  ba "ka fad'a min gaskiya  Adnan da gaske kayi disvarging  dina  ? ta  fad'a tana wani  irin sheshekar kuka kmr ranta  zai  bar gangar jikinta "idan  gaske ne kayi disvarging dina  a yaushe kenan kayi da  ni ban  san da zaman hakan   ba ?" still  shiru  yayi  qirjinsa na cigaba da  bugawa  da karfin gaske  , sai dai wannan karon yayi  k'okarin  Kai hannunsa jikinta  domin  kamota , tayi saurin  buge  masa hannu "dan Allah  ka  fad'a min cewar karya ne  ba gaskiya bane dan zuciyata bazata  iya d'aukar wannan sabon  tashin hankalin ba ?".
ta  k'arasa  maganar  tana cakumar  wuyar  rigarsa da hannuwanta duka  ta matse  masa  wuya  gam da iyakacin karfinta  tana  fidda  zazzafan numfashi ."

anas  na  ganin  haka ya lalla'ba sun sun ya gudu ya barsu su karata , dan  bai san ta yadda zai shawo  kan  matsalar ba , shi  da yayi  silar amsar budurcinta sai  yasan duk  yadda zai yi  ya  shawo  kanta   ." Ka  fad'a  min cewar karya ne  Adnan bakayi komai dani  ba?  dan  Allah  karka ce min  kayi  disvarging dina...."  wannan  kalmar  kawai
take fad'a  tana  sake  maimaitawa  .  rungumeta  yayi   tsam  ajikinsa  yana  sakin  numfashi  babu  shiri  ta sakar masa wuya saboda ba  karamin runguma yayi mata ba , ya  Kai  bakinsa daidai saitin kunnenta ya soma rad'a mata mgn cikin  sanyayyiyar muryarshi   me  kashe  gabobin jiki   "da  gaske ne tanweer amman  kece  silar   Komai  daya faru ,kece  da kanki kika kawo min  kanki  batare da nayi niyyar aikata  hakan ba".

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun  ta  furta cikin tsanani tashin hankali, zamewa tayi ajikinsa ta kwalla wata razananniyar qara mai  sauti  da tasa gbdy gidan ya amsa  tana  ihu  ta zube kasa warwas  tana  kuka da birgima da  sauri  ya durkusa gabanta ya rikota  gam jikinsa na rawa tamkar  mazari   yace "wallahi ba da  son  raina  nayi ba kece kika bukaci  hakan ".
"ni ....!
Ta  furta a  tsawace tana watsa masa wani mugun kallo ,ya gyada mata Kai alamun "eh !
"na shiga uku na lalace ni surayya  Adnan ka cuceni taya zaka  min haka? "taya ma zan kawo maka kaina wallahi ban san na aikata hakan ba karya kake min wallahi bazan ta'ba aikata hakan ba saboda Ina qaunar  budurcina fiyye da komai dake cikin duniyar nan"  .
kuka  tanweer take sosai kamar ranta  zai fita ya bar gangar jikinta ta mike tsaye ta soma tafiya  cikin tsananin tashin hankali  tsabar gigicewa hanyar special  room dinsa ta nufa har tayi taku uku ya biyota da hanzari  ya fixgota da karfi ya sake  mannata  a faffadan qirjinsa "am  really sorry for....." ai bata bari ya karasa ba ta shiga dukan  qirjinsa da iyakacin karfinta  tana tsine masa tana mai  sake fashewa da wani kuka . kamkameta yayi sosai ajikinsa duk  ya  rud'e  ya gigice sai zufa yake  fitarwa "ka sakar min jiki bana  son  kusancinmu tare ,  tsanarsa  take son yi  irin tsanar da bata  ta'ba  wani halitta ba amman  tsanar  taki sauka acikin  zuciyarta ."

Muryarta cike da kuka tace "a tunanina na tsira daga kaidinka a she ban tsira ba ," me yasa kamin haka  Adnan ? wallahi  nasan bana haiyacina bancin haka babu abinda zai sa na baka kaina , Kuma ko duk  duniya zasu  taru akaina  bazan taba yarda da nice na kawo maka kaina ba  sai  dai  idan wani abu ka bani na sha har kayi nasarar akaina ".
shiru yayi kawai yana sauraronta yana tunanin yadda zai ku'butar da kanshi agurinta take ya tuna da cctv  na bangarensa  dan  haka yay  gauggawar zareta ajikinsa ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita nan fa ta turje tana cewa "babu Inda zani ka rabu dani wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa  "muje !
iya abinda bakinsa ya iya fad'a kenan ya cigaba da tafiya bai tsaya akoina ba sai a d'akinsa ya zaunar daita tana wani irin kuka me ta'ba zuciya ."
Chapter 62 · 0% Book details