← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 160

Sashe 90

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

jikin tanweer a sanyaye ta shiga motar inda zuciyarta ke bugawa da karfi fiyye da kaida  har ya  juya zai shiga motarsa  ya dawo  "idan kinje gida duk abinda za'a ce hakuri ne naki ,hakuri zaki basu dan kinyi  laifi  sosai " yana gama fad'ar hk   ya sake  juyawa ya  shiga nashi  motar itace ta fara fita sannan shi ,yana biye daita  a baya har bakin estate dinsu sai daya ga securities sun bud'e mata  get  din farko sannan ya juya zuwa gida zuciyarsa na wani  irin bugawa da karfi akanta .."
Hon din motarta ya janyo hankalin iyayenta mumy tayo waje da sauri  ta tsaya cikin tsananin tashin hankali har sanda  mai gadi ya bud'e mata
ta shigo da hancin motarta ta Isa gurin da'aka tanada domin ajiye motoci tayi parking ta fito  ganin itace ta juya ta koma ciki bakinciki na sake mamaye zuciyarta  .Tanweer na tafe tana sakar zuci kome zata tarar yau agurin iyayenta?" dan yanayin data hango  fuskar mumy babu sausauci "Ina zan Saka kaina yau ?". tayiwa kanta tmbyr ."

Tana shiga falon ta iske iyayenta zaune har ma da rukayya da damuwar  dady  da mumy ta hanata runtsawa, jiki a sanyaye ta durkusa bisa gwiwowinta a gabansu  ta rushe musu da kuka mai ban tausayi  "kuyi hakuri dan  girman  Allah ku yafe min "
"yanzu  saboda Allah  me kike so damu tanweer ?"
"Tun yamma  tanweer sai yanzu kin ma kuwa  duba lokaci kuwa?" bakya Jin tsoron abinda zai  faru dake ba kya gudun ki had'u da wata maseefar a hanya kina fita  anyhow without security " .
shi kuwa dady zaune yake ya rasa abinda zaice mata gbdy ma ya rasa inda zaisa ransa yaji dadi  bai san yadda zaiyi da tanweer ba .
Dafe qirji mumy tayi saboda ciwon da take jin gurin yana mata   rukayya  ta dafa mumy  tana bata hakuri tana mata sannu ,a hankali hawaye ke fita a idanunta cikin muryar kuka take cewa "bakinciki ki zai kasheni tanweer..."
rukayya cikin tsananin tashin hankali ta d'aga murya tace "kin shiga uku tanweer zaki yi sanadin kashe mahaifiyarki wallahi tun wuri  ki dawo haiyacinki ,so fa ba hauka bane idan so cuta ne ai hakuri magani ne  kina son ki maida kanki yar iska da karfi da yaji wallahi kibi a hankali muddin kika bari bakincikinki  ya kashe mumy zaki  buga babbar hasara .Rukayya kuka mumy kuka tanweer kuka shi kansa minister alhji abubakar  hawaye  yake zubarwa  mai  zafi .

Tanweer ta rarrafo tazo gurin mahaifinta  "dady please kayi hakuri  wallahi bazan sake  ba " sai lokacin yay mgn cikin karfin  hali "karki sake fada min haka, sau nawa kina min irin wannan alkwarin kina sabawa?"
ta sake bude baki zatai mgn
yace " enough  tanweer banason jin komai  daga bakinki tashi ki bani guri " ta yunkura da kyar ta tashi ta shige d'akinta tana yiwa kanta  fad'a "tanweer ya dace ki canza kodan samarwa iyayenki da  kanki kwanciyar  hankali ,ki daina zuwa gurin Adnan  , shi me yasa bazai zo gurinki  ba  sai ke?"
Ta zauna a bakin gadonta  cike da Jin nadama aranta.

tana zaune tana goge hawaye rukayya ta shigo tana cewa"haba tanweer ,dan Allah ki canza wannan rayuwar bata dace dake ba dan ma Allah yasa gidan nan ku kadai ne , ya kike tunanin halin da iyayenki zasu shiga ace akwai  mutane atare daku ?".
Hawaye masu zafi suka zubo mata .
rukayya ta zauna gefenta "Ki daure ki cigaba da addua ".
"Ina yi rukayya wallahi har na gaji da yin  addua "ta fad'a tana kuka "ba'a gajiya da addua sai dai  kina yi kina avoiding din wasu abubuwa ne, ki d'aure ki  koyi hakurin rashin zuwa gurinsa wallahi a hankali kina addua kina rarrashi zuciyarki zaki  rage soyayyarsa.
girgiza kai kawai tanwer tayi a ranta tace "rukayya bazaki gane ba, rukayya soyayyar nan nada wuyar bari ,ita wallahi bancin iyayenta ma da tarewa zatai agurinsa sai dai yasan yadda zai yi daita.
"tanweer!"
Rukayya takira sunanta bata amsa ba sai dai ta d'ago ta zuba mata Ido  tana sauraronta "ki dinga karanta ya hayyu ya qayum ya  zaljalalu wal ikiram sannan da laila ailla anta subhanaka inni kuntu minal zalimin inshallahu zaki samu sausauci da natsuwa kina addua Kuma kina nacewa wadan zikirorin suna matukar yayewa mutun damuwa ."rukayya tafi minti shabiyar a d'akin tanwer tana bata shawara kafin daga bisani ta barta ta koma d'akinta .

Bangaren jaguwa kuwa karfe daya daidai ya shgo gidansa yana shiga falo ya k'arasa gurin fridge ya bud'e ya  d'auki goran ruwa mrs v tare da kafeshi abakinsa ya shanye tasss sannan yayi wurgi da rabon zama yayi akan d'aya daga cikin kujerun falon yana sauke numfashi yana Jin kamar tanweer na kwance ajikinsa  ne , wata irin zazzafa  soyayyarta ne ke ratsashi yana tuno duk abinda ya gudana a tsakaninsu ,bai yi tunanin zai rufta har haka ba, lallai maganr anas ta tabbta koma yace bakinsa ya kmashi   ji yayi an dafashi a zuciye ya juyo da niyyar yiwa kowa ye maseefar katse masa tunani   sai yaga anas ne  "cool down mutumina karka saukemin maseefa ya fad'a tare da zama a gefensa "ya ka maida tanweer ?"um na maidaita wallahi sai naji dama na barta. "bangane dama ka barta ba ?"ka barta ka dinga kwana da yarinyar mutune ko me ?".
tsaki yaja "kai wallahi wani irin mutun ne ko yanzu banyi komai daita ba ,"bayan na farko kana son kace baka sake ci ba ?".
"Naci mana amman sau daya ne daga shine  dai babu kari.
"Shikenan ka dinga kiyayewa please kasan yarinya ce karama ."
"nasani shiyasa ma  kaga banason kusancina  daita wallahi idan tana zuwa zan din cin yar mutane né kawai ,zan ma fad'awa mai gadi  kar ya sake barinta ta shigo idan tazo  "gsky abar wannan relationship din haka  tunda bazai kaiku ga yin aure ba ."
Har yanzu kaki ganin mutumin nan sai faman binka nake ,ka hadashi da wancan mutumin ayi komai a gama ayi musu tsakani zuba masa idanunsa dake cike da giyar soyayya yayi sannan ya mike tsaye ya fara zare jallabiya dake sanye ajikinsa ya rataya akafadanshi ya nufi d'akinsa yana cewa " zuwa yanzu nasan ya horo sai dai ban shirya ganinsa ba sai mun dawo daga abuja mugama da aikin nan da aka kawo ". Yana shiga d'akinsa bathroom ya shiga ya tsaya rike da kugunsa yana tarawa kanshi ruwan wanka babu abinda zuciyarsa ke yi sai faman tunanin tanweer hankalinsa gbdy baya jikinsa tube boxes dinsa yayi ya shiga bathtube anatse yayi wanka ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna tanweer murmushin farinciki ne ya subuce masa a haka yayi wanka ya fito .
Ya goge jikinsa ya bud'e Inda kayan shan iskansa yake ya dauko gajeren wando ya sanya ya shirya tsaf sannan ya kwanta batare daya sakawa cikinsa komai ba.

Washegari  da safe byn fitar dady mumy ta iske tanwer a dakinta kwance ,ta tasheta ta mike ta zauna tana dubanta "ina kwana mumy?" Kin tashi lfiya mamana ?" Lafiya ta amsa atakaice mumy ta kamo yatsun hannunta sannan cike da marairacewa tasoma mata nasiha mai ratsa jiki tana rikonta "ki tausaya min surayya wannan rayuwar nasan qaddara ce amman ki daure ki cinye jarabawar karki kauce hanya ina miki addua zaki samu wanda yafi shi komai take hawye ya shiga turereniyar zubo mata "wannan alfrma ce na nema agurinki zaki min ko kuwa na hakura na cire raina akanki na bar masa ke ya maye mki gurnina "?kanta ta shiga girgiza mata alamun "a'a ".
"Kinyi min alqawarin zaki hakura dashi "?ta gyada mata kai alamun"eh! dan babu yadda zatai amman hakura da jaguwa ma bai taso ba mutumin da duk saukar numfashinta da tunaninsa aciki.
"Na gode allah yayi miki albarka allah yaye miki ".
Chapter 90 · 0% Book details