← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 160

Sashe 34

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jin  motsin  shigowar motocinsu  da  maganar  wasu  daga cikin yaransa   sama  sama  yasa tanweer  lalla'bowa babu takalmi  a ka'fafunta tai hanyar  babban   falon   gidan    tana  bin bango tana  qarasowa bakin kofar falon ta tsaya  a hankali ta bud'e kofar ta shiga  bata   ga  kowa  a falon ba,  kasa  kasa  take jiyo  magangansu  , kawai   ta nufi   wani  dogon  korido  Inda  take  zaton daga  nan sautinsu yake fitowa  , a hankali  ta tsinci kanta acikinsu   kowannensu cikin tsananin tashin hankali , jaguwa  zaune a gaban kamil   cike  da tausayawa  yana k'okarin  cire   masa   harsashi . binsa tayi  da kallon mamaki  qirjinta na wani irin bugawa da matsanacin karfi shafa  idanunta   tai  hade da runtsesu  na second biyu sannan ta bud'e tana sake  sauke idanunta akanshi wanda zuwa   lokacin har yay nasarar  ciro bulet   din  yana kallo sannan  ya  saka acikin  farantin  silver dake rike a hannun jubi, yayinda sauran ke zaune cikin  tsananin tashin hankali gbdy idanunsu ya rufe babu wanda hankalinsa ya Kai Inda take tsaye ."

naunaye ajiyar zuciya  suka sauke lokacin  da jaguwa ya  cire wa kamil bulet  ita Kuwa tanweer zuciyarta ta shiga rawa had'e da tsinkewa  ."me zata  gani  yau ? daman likita ne shi  ko kuwa mafarki  take  ?   yes  wannan ba  mafarki take ba shine tagani  zaune  ya cire  bulet a kafar abokinsa, kasa tayi da idanunta tana kallon bayansa nan  idanunta ya  hango  bindiga pestol  soke a abayan wandon  jaguwa  ,nan   take ta  sake fita  daga  haiyacinta "bindiga ....! ta furta a kasan ranta " me   Kuma yake  yi  da bindiga ? ya  Allah karka sa  abinda  zuciyata ke hasashe  akansa ya zama gaskiya dan bai cancanci haka ba " wani kuka ya kufce mata   ta juya da sauri tana  shesheka   wanda  hakan  yasa  gbdy suka   d'ago suka ganta tana sarsarfa  , cike da matsanacin firgici   suka  tsura ma jaguwa   Ido    dan  jin abinda zai ce  bai yi magana ba haka zalika bai  nuna alamun  damuwa atattare dashi   ba , ya  mike  tsaye yana
furzar da numfashi tare da yiwa kamil sannu" ka kwanta ka huta kafin  akawo maka abinci ya gyada masa Kai  yana cewa" na gode abokina Ina alfahari da Kai ,nima haka   ."

jubi  ya dube jaguwa  yana cewa  "wallahi ban  ta'ba   shiga tashin hankali  ba irin na  wannan  lokacin na tsorata  matuka   na sadaukar zamu rasa  kamil  "ba  kai kad'ai ba inji cewar anas  tafiya  jaguwa  ya  fara a hankali   suka  biyosa   a baya  har gurin   shakatawarsa    "da'ace  sunyi nasara akanmu   zamu  iya rasa rayukanmu gbdy". sai lokacin jaguwa ya motsa lip's dinsa   "ina ai sai dai idan  tawa ta kare sannan zaku iya shiga  wannan  hali  amman muddin Ina tsaye akan kafafuna babu wanda zai yi  nasara  bare har mu rasa rayuka "  ya  karasa maganar  tare da  tsayawa  cak ya  rike  karfen  runfar dake  kafe acikin   gurin  shakatawar , "hakika Nima na karaya  inji cewar jabir  " Karku  ta'ba rungumar  Karaya arayuwarku duk halin da zamu shiga karku karaya saboda    rashin samun nasara  ba namu bane ,a duk lokacin da naga Kun Karaya  sai  naga kamar tun asalin ku din ba jaruman gaske bane, sannan baku ne jarum da mukayi gasar mutuwa dasu  ba  ."

murmushi sukayi gbdy suna sauke numfashi  "uhm wannan fa ba kamar gasar mutuwa bace  ,gasar mutuwa kowa yasan  mun saida rayukanmu ne dan biyan bukatarmu  wannan fa ?"bayan sai da rai har da  tozarci  zamu  janyowa  gangar  jikinmu  idan muka tsinci kanmu a hannun jami'an tsaro ".anas ya karasa maganar yana  dafa kafad'ar  jaguwa  "yanzu dai barkanmu  allah  ya k'ara karemu  ." ameen  jaguwa  ya fad'a acikin zuciyarsa.   "ka zauna    kana bukatar  hutu, jaguwa   ya  zauna  akan d'aya daga cikin kujerun gurin yana lumshe idanunshi " me za'a  kawo maka ka d'an sha ? ya  girgiza  masa  Kai  alamun bai   bukatar komai , zama  anas yayi kamar yadda sauran abokansa sukayi  yana cewa  "ya za'a yi da wannan  yarinyar ta rigada taga komai , koma nace  taji wasu abubuwa akanmu ? ,yana  d'aya daga cikin abinda yasa kaga  banason yarinyar nan agidan nan "."me taji ?."Ko me mu kace ?yay masa  tambayar a dan kufule " idan Kuma taji taji kenan shikenan daman abinda  take bukatar sani kenan  tasan su waye mu " ya k'arasa maganar yana jan  dogon tsaki tare da  jin bakinciki  da takaici, haka nan Kuma ya tsinci Kansa da Jin fad'uwar gaba mai tsanani ".

Koda tanweer ta koma d'aki  ta kasa  tsaye ta kasa zaune sai zariya take  acikin d'akin  ita kad'ai, ta saka wancan ta kwance , kwakwaluwarta ta shiga tunani mai zurfi, babu abinda zuciyarta bata kisama mata ba akansu , abu uku  zuciyarta ta tsayu akansa  shi din  dan fashin ne  ko Kuma jami'in sirri ,ko  likita ,  idan ba haka ba me yake yi da bindiga ajikinsa ?  ta kasa hakuri dan  haka ta sake fitowa tai hanyar boys quarter nan fa hankalinta ya sake tashi ganin yadda yaran jaguwa  ke fitowa  da manya  bindigu suna adanawa a maboyarsu ,mutuwar tsaye tayi har sanda suka kwashe komai  suka  d'auki  katuwar jakar kudin da suka shigo dashi  suka nufi hanyar Inda jaguwa yake tare da abokansa suna tautaunawa ,  cike da matsanacin tsoro ta biyo bayansu  a tare suka k'araso ta ra'be jikin wata bishiya kasancewar yaran jaguwa  suna   gabanta yasa jaguwa da abokansa kasa ganinta ."

sky ya ajiye jakar  kudin a gaban jaguwa yana cewa  "boss ga kudin operation din ". operation ? ta furta a kasan ranta zuciyarta  na tsananta bugu kamar zai fasa  qirjinta ya fito waje , tayita  tunanin abinda  manufar operation yake nufi  acikin ranta .
a natse Jaguwa ya d'ago idanunshi  yana ciza lips dinsa na kasa  sai daya d'auki minti biyar sannan ya gyada Kai , yay musu alamun su wuce suka soma k'okarin juyawa  tana ganin haka tayi baya  da sauri ta  la'be dan karsu ganta , gbdy kwakwaluwarta
ta gama tabbatar mata da manufar operation fashi ne ".barin wannan bishiyar tayi ta dawo kusa dasu sosai ta sake makalewa a wata bishiyar ta kasa kunne daga Inda take  boye take jiyo duk abinda suke  cewa  "mun gama da operation din  yau  yanzu dai  a  kasa  kudin   gida  uku nasan inamdi na  nan zuwa  komai dare ya amshi  kasonsa dan bashi da hakuri kmr alhj Tahir  yake "kamar alhj Tahir ta maimaita sunan ?tunanin Inda tasan sunan take gbdy ta kasa tuno Inda ta ta'ba Jin sunan amman tabbas kwakwaluwarta na hasko mata tasan sunan Kuma  na kusa da jikinta ne ".
ko gama rufe baki   jaguwa bai yi  ba sai ga inamdi da eku remo , inamdi ya mikawa jaguwa  da abokansa hannu suka gaisa shi Kuma eku ya juya ya kama gabansa .
guri jaguwa ya nuna masa da hannunsa , ya zauna yana cewa "sannuku Kun sha da kyar lokacin dana ga police sun harbi d'aya daga cikinku naji tsoro matuka, hankalina yayi matukar tashi "sa'anar  armrobber's   akwai dadi akwai saida rai  ,bancin kwarewa irin naka da yanzu kuna hannun police.
"inna lilli wa inna lillahi rajiun" tanweer ta shiga furtawa  tana maimaiwa tasa hannunta duka ta rufe  bakinta dan   kar sautin kukanta ya fito "ya dai  tabbata su din 'barayi ne ........?  " wannan shine dalilin da yasa ya fad'a mata  da tasan shi ko waye shi  da bata kamu da soyayyarsa ba ?wayyohhhly Allah nah ! "wayyohhhly Allah   Adnan me yasa? " me yasa ka zabi wannan sa'anar ?  jikinta banda rawa babu abinda yake  tana kallo  aka kasafta kudin aka bawa inamdi  nasa kason ya ciro  wata karamar jaka a aljihunsa  ya shiga  d'aukar bandir   din daloli yana  zubawa cikin  jakar  har ya gama ya mike  ya sake mimika musu hannu sukayi sallama ya  wuce cikin sauri ."

A hankali ta dinga d'aga ka'fafunta tana takowa  zuwa Inda suke zaune , jaguwa ne  ya d'ago   idanunshi suka  sauka akanta,  cikin  tsananin tashin hankali da damuwa mara misaltuwa  yake kallonta   ,bakinta na rawa ta soma magana cikin firgici  "daman 'yan  fashi ne ku  ?".ta fad'a tana kallonsu d'aya byn d'aya .a rud'e abokan jaguwa suka  had'a baki gurin cewa" no  mu ba 'yan fashi bane armrobber's ne" jaguwa ya mike a natse cike da bakinciki taji sirrinsu  yayinda gbdy  abokansa  suka rud'e  da  ganinta har suka  kasa bambamce tsakanin abinda tace da amsar da suka bata , fuskarsa a murtuke  tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya  kallesu d'aya bayan d'aya  kana ya soma mgn  "babu bambamci  da abinda kuka ce  da wanda tace  duk abu d'aya ne  mu din barayi ne wato armrobber's  ..... ".
ta zaro idanuwanta duka waje da sauri  qirjinta na dokawa da karfin gaske  ,yayinda  numfashinta ke fita da sauri sauri.  ya gyada mata Kai alamun  "eh".wani abu  mai duhu  taga ya gilma cikin idanunta, zuciyarta ce ta tsaya cak  ta daina
aiki na wani lokaci kafin daga baya ta dawo tana bugawa fiyye da kaida , ta rike kanta dake sara  mata kamar zai ra'be  gida biyu ,a hankali ta soma  ganin jiri  tayi  kasa tana dafe da kanta  tana daf da zubewa   kasa yay saurin  tarota zuwa  jikinsa  kwayar idanunshi na kanta , kallon yadda jikinta ya saki  yake adalilin  numfashinta daya  tsaya ya daina aiki take  ya fahimci suma tayi  , bai tsaya jiran komai ba ya mike daita rungume  ajikinsa yana kallon face dinta , Kai tsaye d'akinsa ya nufa daita ya kwantar daita yana k'okarin kulle  kofar  abokansa suka turo suka  shigo d'akin  suka yo kanta  suna tambayarsa  , wani  kallo yay musu gbdy suka ja  baya  tare da barin d'akin  ."
Chapter 34 · 0% Book details