← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 160

Sashe 145

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna cikin  hirar wata awa daya tazo ta wuce karfe shida daidai kenan cikin haka  hally ta kira layin anas ya zaro wayarsa yana dubawa "my princess ."
Ya fada yana dauka "wa'alaikis salam matata fatan kina Lfy?alhamdulillahi kinji shiru ban kiraba ko ?sorry my princess inshaallahu bazan jima ba zan shigo  sukai sallama ya maida hankalinsa ga jaguwa wanda ya dauki sigari ya kai bakinsa "kasan yanzu hatta sigari ina kyamar shanta saboda banason matata taji warinsa ajikinsa ".
Wannan kuma damuwarka ce ni dai ko zan rabu da komai ban da sigari ina mugun qaunarta murmushi Ana's yayi  "wallahi adnan ina maka kwadayin aure da zarar kayi aure gbdy rayuwarka zata canza zaka rage wasu abubuwa tunda ga zahiri na gani akaina idan akace zan daina shan giya da neman mata zan karyata sai gashi hatta sigari ina neman barin ta "kai dan allah tashi  mune garin ma ya sake hadewa da hadari nasan muna kan hanya lokaci zai yi na ajiyeka agida na kara gaba da motarka ."

Mikewa yayi ya shirya kansa sosai tare suka jera har suka karaso haraban gidan babu kowa acikin abokan aikinsu sai mai gadi kadai zaune  akan farar kujera mai zaman mutun daya  dakin ajiye makamansu ya wuce ya dauki bindiga masu lafiya guda hudu da harsashi ya zuba cikin karamar jaka ya fito  inda motar anas take fake ya  nufa Ana's ya ciro keyn mota a aljihunsa ya mika masa sannan kowannensu ya bude murfin bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna jaguwa ya waiga ya ajiye jakar abaya ya sanya key ya tayar da mota suka bar gidan ."
Suna barin gidan cid  ya soma kai kawo a haraban gidan bashi wannan lungu bashi wancan lugun wanda a garin leke lekensa yasan adadin mutanen dake rufe acikin gidan  babu wanda ya bashi tausayi kamar alqali  mutumin dake kan aikinsa shima fa da asirinsa zai tono wannan ne hukuncinsa agurin jaguwa tunda ya fahimci basa kisa sai izaya suka iya ."

A halin yanzu shi kansa ya matsu wa'adinsa ya cika ya tattara ya bar gidan domin yana matukar jin tsoro yana cikin tafiya yana dube dube kamar ance ya daga idanunshi sama ya hangi wata tukunyar kasa yar karama acikin tsakankanin fulawas din dake shuke a gurin ,bai yi sanya ba ya juya zuwa daki ya kira number dcp ya sheida masa ,"okay to shikenan amman ban zan samu damar fita ba  yau dana zo da tukunyar  ,no bai nan yanzu ya  fita tare  da amininsa ."
"Gaskiya bana tunanin suna  zargina ,"okay to shikenan sai dai nayi haka ya fito yana waige waige  babu kowa ata bangaren da yake dan haka ya dauki  kujera  ya kai daidai inda yaga tukunyar ya lallaba ya ajiye ya kara tsayi daita yayi bismillah ya dauko tukunyar ya ajiye yana kallon tukunyar babu komai acikinta sai kahon rago da madubi aciki  sosai tsoro ya kamashi ." amman hakan bai hanashi yayi fitsari acikinta ba  kamar yadda dcp ya fad'a masa ai gama fitsarinsa ke da wuya wani bakin hayaki ya tashi yayi sama ya dauki tukunyar ya mayar inda ya ganta ya lallaba  ya bar gurin  ."

Jaguwa kuwa tunda da suka shiga mota hirar yadda haduwarsa da commissioner zai kasance suke har suka hau kan babban titi ilu peju a lokacin garin ya sake hadewa da hadari "idan ruwan sama ya sauko allah kadai yasan lokacin da zai tsaya ,nima tunanina kenan ga aiki mai girma agabana fatana na samu nasara haduwa da commissioner suna tafiya ruwan sama ya tsinke kamar da bakin kwarya gbdy jikin anas yayi sanyi dan haka ya dif ya daina magana  yana kallon motocin dake falla gudu akan titi ."
wata mota kirar farari baka wuluk ta wucesu da mugun gudu   akan titi ilu peju tafiya kadan motar tai ta tsaya a gefen titi direban dake tuka motar ya waigo alokacin da matan daya tuko suke kokarin tmyrsa   dalilin tsayuwarsa a halin yaga ana ruwan sama  "tayar motar ce ta samu matsala bari na fita na duba na gani ya fad'a yana kokarin fita cikin ruwa ,  acikinsu babu wacce tayi kokarin hanashi fita sai hirarsu da suka cigaba da yi gashi mutumin ya dan manyata ,tsohon  direbansu  ne  minister ma ya so kwarai ya ajiye aiki amman tsohon yaki a cewarsa zai iya kuma tabbas yana kokari idan gurin tuki ne  ."

Boot din motar ya bude ya dauko wani karamin akwati dake dauke kayan gyara ya bude  sannan ya duba tayar  tan take ya gano matsalarta notikan tayar ne suka dan sake abun  daure taya ya dauka ya tsugunna ga ruwan sama na dukansa amman bai damu ba  ya fara aiki."cikin haka motarsu jaguwa ta karaso har ta gotasu kadan ya dawo baya yayi parking yana cewa"Ana's "bari na taimakawa tsohon can ya gyada masa kai kawai ,ya fito yana tare ruwa dake dukan fuskarsa da hannunsa har ya karaso gurin tsohon ya tsaya tsayuwa irinta ingarman namiji mai tattare da natsuwa da Kamala, a hankali ya motsa lips dinsa yana cewa "baba kawo na taimaka maka ka koma cikin mota ,tsohon ya dago yana yarfe ruwan dake dukan fuskarsa ya tsurawa jaguwa ido yana kallonsa yana ji dadi acikin ranshi  yace  "yaro na gode Kwarai da gaske allah yayi maka albarka amman  kayi tafiyar zanyi da kaina ."

"karka damu baba ka kawo ya kai hannu ya karbi karfen hannunsa shi kuma tsohon ya shiga cikin mota ya zauna "har ka gama baba ?Aa wani dan albarka na samu zai taimaka min ban taba tunanin har yanzu akwai mutane masu kirki haka a cikin wannan duniyar tamu  ba ,shiru tayi hakan nan taji gabanta ya shiga duka uku uku  bata sake cewa komai ba ,"Jaguwa ya  tsugunna a inda tsohon ya tashi ya kwance tayar motar kadan  ya sake daureta tanwer dake zaune bangaren da tayar ta samu matsala kamar tayi warning din glass  amman ta kasa aiwatar da hakan sai dai ta kasa dauke idanunta daga kallon gurin ga wani faduwar gaba daya dabaibeyeta ."

Bayan ya gama  ya tattara kayan aikin  da yayi amfani dashi ya nufi byn boot nan ma zuciyarta ta bishi da kallo sai dai bata dago ba  ya bude boot din   motar ya mayar masa da akwatin kayan aikinsa ya maida murfin ya rufe yana dagawa tsohon hannu dake kallonsa ta cikin mota sai  alokacin tanwer ta waigo  sosai  ta bayan motar domin taga wanda ya taimaka masu ana tsaka da tsuga ruwan sama byn ga motaci nata falla gudu akan titi karaf idanunta ya sauka akan jaguwa ,gbdy kayan jikinsa ya jike sharkaf  har sun bayyana tsayayyun nipples dinsa."
ta kasa dauke idanunta akanshi shima idanunshi
ya tsaida akanta cike da mamaki yake kallonta dan  tsantsar mugunta da zalumci shine ta bar tsohon mutane cikin ruwa ita tana hakikce abayan  mota lunshe idanunta tayi tana kokarin fitowa daga cikin mota sai dai kafin ta fito har ya juya bata damu ba ta fito cikin ruwan tana kiran sunansa da sauri ruky tabi  bayanta da kallo  ."

Cikin sauri  tanwer tasha gabansa  tana sauke numfashi "haba adnan ka tsaya mana ." ransa yayi mugun baci akan wanda yake ciki " me yasa ta fito cikin ruwa tana kiran sunanshi gashi ta jawo duk jikinta ya jike da ruwa har ya nuna sha shin jikinta ?a kallon da yake mata ta fahimci abinda yake nufi yana da tsanani tausayi da kulawa  ,tausayinsa  ya kamata shi din mutun ne me matukar tausayi ga mutane matsalarsa dai taurin kai idan ya tsaya akan abu babu wanda ya isa ya kawar dashi ko tsaida shi ,tarasa me zatayi domin ta canza shi ya dawo mutumin kirki a idanun duniya ."tsaki yaja  sannan ya riko tsintsiyar hannunta cikin nashi atare qirjinsu ya buga da matsanancin karfi ,ji yayi wani shock ya caki jikinsa da duk wasu jijiyo dake aiki ajikinsa,itama haka taji a sansar jikinta,”
maganad’insun son junansu ne ya shiga yawo a jijiyoyin jikinsu sai dai babu wanda yayi magana acikinsu har sanda  ya soma tafiya daita bai tsaya akoina ba sai ajikin motarsu ya bude murfin motar sai lokaci yaga ashe ba ita kadai bace aciki ita da ruky cousin dinta ne ,ta bude baki ta gaishesa amman yayi mata banza tamkar bai ganta ba da hannunsa ya nuna mata cikin motar sannan ya raba gefenta  ya cigaba da tafiya ya karasa inda motarsu take ya shiga yajata da mugun gudu yana jan tsaki ".

"Lafiya !?Anas ya tmbyesa "wacan motar dana taimakawa tsohon can ashe tanwer ce zaune a bayan motar tsabar rashin Imani da tausayi ta bar tsohon mutane ya fito cikin ruwa ita da cousing dinta  suna hakince abayan mota shiyasa naji motar tayi nauyi ya karasa maganar yana murza sterimg yana jan tsaki ."kai adnan tanwer din da consin dinta guda suke da zasuyi nauyi ?bai sake cewa komai ba dan haushi sannan bai  tsaya ba sai akofar gidan  anas .
“Sauka mana na qara gaba Ana's yace "ka shiga ka sauya wasu kaya mana ."ya girgiza masa kai ya kara  gaba da gudu  shi kuma anas ya shiga gidan  ya zauna a falo sharaf yana jiran princess dinsa ta fito tayi masa sannu da zuwa wacce  lokacin tana can tsaye gaban mirrow tana tsara masa kwaliya."
byn ta gama ta karasa  wordrobe dinta ta dauko daya daga cikin kayan da ammi ta dinka masu ita da shafiq ta saka ,ta  dauko dan karamin akwati dake dauke da sarkokinta  kowanne na cikin gidansa tare da dan kunnensu  ta dauki wanda take son sakawa ta fara saka dan kunne ta dauki sarka wuya zata saka kenan Ana's ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama ."
Chapter 145 · 0% Book details