← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 160

Sashe 4

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Misali karfe daya saura
Kwance  minister yake    akan  makeken  gadonsa kirar  itly   yana lumlumshe  idanun alamun jin bacci yayinda    matarsa hajiya zainab ke kwance a gefensa , dif  yaga  wuta   ya ɗauke yayinda  duk wata na'ura  dake aiki a d'akin ya tsaya  cak ya daina aiki  gidan ya ɗauki  shiru, shiru yayi yana mamakin d'aukewa wuta abinda bai taɓa faruwa ba kenan tun kafin ya zamo minister har zuwa lokaci daya zamo minister gidansa bai taba rashin wuta ba ,yana cikin wannan mamakin
ya dinga jin  motsin durowar mutane  da yake dakinsa ta bangaren baya yake kuma daf da katangar gidan  , ya yunkura  ya  mike  zaune daga kwance da yake yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon hajiya Zainab tayi saurin  riko hannunsa cikin nata, a she idanunta biyu  jikinta na rawa tace "ina zaka ? "zan leka window ne  ina jin kamar motsin mutane , "ba kamar kana jin motsin mutane  bane, mutane ne da gaske Allah dai  yasa ba yan fashi bane  ?

"Yan fashi ya maimaita abinda tace  cike da mamaki ?ta gyada masa kai kawai batare da ta sake cewa wani abu ba illa jikinta dake kyarma tsabar tsoro "okay Ki kwantar da hankalinki gidan nan akwai tsaro mai tsanani  bana tunanin akwai  damar da zai  kawo yan fashi gidan nan   , Ki tsaya  anan ina zuwa ya  karasa saukowa daga saman gadon qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi ,da sauri  ta sauko ta biyo bayansa  ,a hankali  ya qarasa bakin window  dakinsa ya  tsaya yana kallon haraban gidan inda  idanunshi ya hango masa wasu mutane sanye da bakaken kaya fuskarsu rufe da face marks  kowanensu rike da bindiga mutun ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin katse wutar data bawa haraban gidan zuwa gurin securitys da wasu bangaren ,  juyowa yayi da sauri hankalinsa a matukar tashe suka ci karo da hajiya zainab dake tsaye a bayansa  ",wayyo Allah yarinyata ta furta haɗe  da yi hanyar fita, yayi saurin kamota jikinsa  ya rungumeta tsam   dan yasan halinta da mugun tsoro  ",dan Allah ki natsu ya zaunar daita ya dauki wayarsa yana ƙoƙarin kiran  number's din  police bai Kai ga samunsu ba yaji an   banko kofar  dakinsa da karfin gaske  wiki  wiki sukayi da idanu ,kamil  ya  harske dakin da wata ƙatuwar fitila mai mugun haske zaka ɗauka wutan lantarki ce jabir ya  saita kan Alhaji Abubakar da bakin  bindiga yayinda Anas   ya saita kan hajiya zainab" move  to the parlou'n  ya furta yana tasa keyarsu , babu mutsu suka runtse idanunsu gam saboda tsabar tsoro  a babban  parlou'n  gidan suka iske jaguwa zaune akan kujera mai zaman mutun ɗaya ya daura ƙafarsa daya  kan daya yana girgizawa  hankalinsa a kwance tamkar  shine mai gidan,  tun kafin su karaso inda yake zaune Jibril yasa bakin bindiga zai dagi keyarsu jaguwa ya dakatar dashi da hannunsa durkushewa ministar da hajiya Zainab sukayi bisa gwiwowinsu tare da kife kansu a kasa  suna rawar jiki sai dai gabadaya  hankalinsu naga kofar dakin tanweer.

Securitys  dake on duty suka taso  ganin wutan gidan ya dauke gabadaya suna tafiya da tochligt  a hannunsu  suna mamaki yadda wutan gidan ya dauke gabadaya ,suna gama karasowa gurin mahadar wutan  suka ji anyi kansu da bakin  bindiga take suka d'aga hannuwansu sama "ku durkusa bama son ganin fuskokiku babu shiri suka yi sujjada ...

a hankali jaguwa  dake zaune ya dubi Anas yana masa alama da hannunsa  take ya fahimci abinda yake nufi dan haka  ya soma motsa lip's d'insa " kayi kokarin   kira police ko ?
da sauri hajiya zainab tayi sigil tace ",a'a..bamu kira police ba tayi maganar tana kallon mijinta " well wannan ba damuwarmu  bane nasan kunsan abinda ya kawomu adaidai wannan lokacin, muna bukatar   bayyanansu  a gabanmu yanzu yanzu bama bukatar bata lokaci"minister ya da'n d'ago ya  kalli jaguwa lura da yayi shine ogansu yace "wallahi babu kudi a gidan nan  shiru jaguwa yayi yana kallonsa  batare daya  sake yin magana ba sai Anas ne yace "babu kudi kace ? minister ya gyada masa kai yana marairaicewa "seach everywhere ka fito min da duk abinda ke cikin gidan nan take Anas da wasu mutun biyu  cikin yaran jaguwa  suka shiga duduba dakunan dake parlou'n     hakan  yasa minister yayi saurin cewa  ", kuyi hakuri karku taɓa min lafiyar iyalina  nasan kudi ne ya kawoku  zan baku duk abinda kuke so muddin zaku barmu nida iyalinna ,gyaran murya jaguwa yayi take suka dawo inda yake  jikin minister na rawa ya nufi dakin da yake ajiyar kudinsa  Anas na biye dashi ghana most go uku suka fito dashi na kudi wani irin tsawa jaguwa ya bugawa minister" lallai ka cika mahainci wanda bai san darajar mahalincinsa ba   ,kace babu pepa a gidan nan ? a rikice yace kayi hakuri wannan tsawar yasa tanwer dake kwance a d'akinta tana bacci ta farka a kidime ta zauna akan gadonta  kafin daga baya ta  sauko ta tsaya a bakin kofar dakin tana leke,  hannuwanta duka tasa ta rufe idanunta jikinta na wani irin rawa saboda ganin bindigu dan parlou'n da haske sam bazakace ba wuta bane   "anas .....

Jaguwa ya kira sunansa "Yesssss   boss d'auko min wacan yarinyar dake lekenmu  ya nuna kofar d'akin da hannunsa kai tsaye ya nufi d'akin , tana ganinsa ta saka wata razananniyar ƙara haɗe da mannewa ajikin bangon d'akin Anas ya karawa   tochligt din dake rike a hannunsa haske  tare da  tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta mai tsananin kyau da ɗaukar hankali  kafin daga baya ya kai hannu zai damkota ta buge masa hannu tana kuka "don't don't ever touch me ta faɗa tana sake mannewa da bango duk yadda anas yaso ya fito daita taki yarda sai buge masa hannu take, ya sake kai hannunsa a zuciye yaji an rike tsintsiyar hannunsa ya juyo a hankali idanunsa ya sauka akan jaguwa "boss gardama take  ko na dauketa da wuta ? girgiza masa kai yayi  "kasan bana son haka  "angama boss ya mika masa hannu dan amsar tochligt din hannunsa babu mutsu ya mika masa,  da hannu jaguwa  ya nuna masa kofar fita  kana ya haske mata fuska da tochligt...
Dam........... qirjinsa yayi wata irin bugawa da matsanancin karfi sakamakon ganin fuskarta ..

Duk ilahirin   jikinta rawa yake ,  sai dai hakan bai  hanata d'ago kyawawan  Idanunta  dan ganin mutumin dake tsaye agabanta ba wanda taji an kira da boss , take idanunsu ya tsarke cikin juna duk da face marks din dake fuskarsa hakan bai hanata ganin kwayar idanunsa mai zagaye da zara zaran gashi ido ba,  runtse  idanunta tayi tana nuna masa hanyar fita da hannunta  murmushi ne ya bayyana akan labbansa cikin natsuwa ya kara taku biyu  zuwa inda take makale da bango ......

DARLING'S

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️03

Matsawa tayi gefe da sauri jikinta na wani irin kyarma yanayin bugun zuciyarta bai saisaita ba , yanayin tsoratanta kuwa ya wuce tunanin mai karatu da kyar take fitar da numfashi qirjinta na kasa da sama ,murmushi ne ya sake bayyana akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri , cike da natsuwa da jin kai da izza ya matsota kamar zai shige jikinta batare daya sani ba , haka nan ya tsinci kanshi da kai hannunsa ya d'ago ha'barta ya tsurawa fuskarta kwayar idanunshi masu matukar kyau da haske cikin nata yana kallon kyakkywawar fuskarta da kwayar idanunta har jikinsu na gugan juna, wani irin kamshi ne na musamman ke tashi a sansar jikinsa tamkar wanda yayi wanka da ruwan turare , hakan yasa ta kasa kawar da idannunta daga nasa ...

Sosai ya tsura mata kyawawan idanunshi yana kallon fuskarta, tunda yake rayuwa bai taɓa ganin halittar data masa kyau ba tamkar hallitar dake tsaye a gabansa , tun daga kan tsiraran lips d'inta, dara daran idannunta, hancinta komai nata ya tsaru ga 'yan yatsunta zara-zara da take nuna masa hanya fita dashi , gaba d'ayabaya ya soma fita hayyacinsa ban da kallon halittar jikinta babu abinda yake ,a hankali idannunsa suka sauka akan saman qirjinta dake cike bam da dukiyar fulanin masu matukar kyau da haske a zahiri yake hango rabin nonuwanta da suka bulluko waje sakamakon rigar baccin dake sanye ajikinta masu matukar kyau ne da budaden wuya dan rigar ta zamo zuwa kafad'anta kamar up shoder " ya Salam !'. ya furta a kasan makoshi yana lumshe sexy eye's dinsa .

a hankali bugun zuciyarsa ya karu tare da k'ara ware idannunsa akanta sannan ya kara matsota ya cire hannunsa dake rike da ha'barta ya cire hanky mai shegen kyau da kamshi daga aljihun wandonsa ya kai fuskarta ya soma goge mata fuska dake kwararar da ruwan hawayen dalilin tsaronsu , kuma har lokacin idanunshi na kan dukiyar fulaninta ya kasa daukesu duk da abinda yake son yi kenan amman ya kasa, rigar baccin dake jikinta sun mata maseefar kyau bayan bayyanar da surar jikinta da suka yi .

A tsanake tanweer ta fahimci inda yake kallo ajikinta ya d'ago idanunshi ido cikin ido suke kallon juna a hankali ya soma ko'karin matsawa daga gefenta saboda ganin irin mugun kallon da take binshi da shi mai ɗauke da zargi iri iri , cikin rashin sa'a itama tana ko'karin da'uke kanta dan gani take kamar tab'atazaiyi, hannunsa ya tab'i qirjinta batare da yayi niyyar aikata hakan ba sai dan ƙoƙarin saisaita kanshi , cike da takaici da zafin nama tattare da bakinciki tanweer ta da'ukeshi da wani gigitaccen marin da bai san sanda yayi mutuwar tsaye agurin rike da gefen fuskarshi yana kallonta cike da tsananin mamaki lokaci daya ranshi yayi mugun baci ,take zuciyar shi ta shiga bugawa da sauri sauri wani duhu ne ya gilma cikin kwayar idanunshi yana jin wani tuttukin bakincikin da takaici mai tattare da "bacin rai..
Chapter 4 · 0% Book details