← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 160

Sashe 42

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bamu saba boyewa kanmu komai Daya shafi rayuwarmu ba ,jabir, jubi kamil ,duk tare suka ganmu kana fada min  gaskiyar dake cikin zuciyarka akan komai amman akan wannan yarinyar ne kawai ka kasa fad'a min matsayinta a zuciyarka ,kana tunanin zan hanaka soyayya ne da ita ko me?wallahi kamar yadda kaji na fada maka ni me rungumar komai ne akanka Koda kuwa mutuwa ce, Ina maka soyayyar da zan iya sadaukar da rayuwata akanka, karka manta mu din masoyan juna ne da muka yarda da juna Kuma muke son juna saboda Allah, zuciyata ta yarda ta amince kana son yarinyar nan so me tsanani ko dan tana diyar minister yasa kake gudun fallasa sirrin soyayyarka ?
"ko d'aya  bana  dai sonta ne " kama saukakawa kanka nan kusa ma ammi zata min mata ka san kuwa zuciyata bata da wani zabi daya wuce nata dan haka ka cire wannan tunanin a ranka ya k'arasa maganar still idanunshi na kanta " yana dasa Aya anas ya juya a hankali ransa a matukar bace.

"ta yaya gashi yana kallon tsagwaron qaunar yarinyar a idanunshi amman yake ja inja dashi ? ranar ce rana ta farko da jaguwa yayi masa abinda   har yaji ya tsaya masa arai , Jin motsin Bude  kofar d'akin ya sa jaguwa ya waigo da Kansa anas ya gani zai fita daga d'akin shima kmr ya bar d'akin sai ya tsinci Kansa da kasa aiwatar da hakan yaji bazai iya barinta ita kad'ai ba dan haka ya hau gadon ya janyota ya d'aurata a saman  faffadan qirjinsa, a hankali  yana shafa bayanta, ajiyar zuciya ta fara jerawa tamkar wacce ta sha gudu tsira  ,qara   makaleta jaguwa  yayi   tamkar  wani zai kwaceta a hannunsa "Anya   kuwa adnan  baka  fara  son yarinyar nan ba ?" ya  tambayi kanshi yana shinshina wuyanta" ka fara sonta mana tunda kana tsananin qaunar kasancewa daita zuciyarsa ta bashi amsa da hakan  "Ina  ba  haka bane tausayi ne kawai babu wannan a tsakanina daita ,gyara mata kwanciya yayi sosai ta yadda bazata takura ba ya sauko daga kan gadon zai fita yaji ta riko hannunsa waiwayota yayi zuciyarsa na dokawa da matsanacin karfi ya kalleta sosai bacci take da alamun ma bata san ta aikata hakan ba , ya fito daga d'akin zuwa bedroom dinsa kana ganinsa kasan baya cikin haiyacinsa zama yayi yana neman layin sadiq ya kira sakamakon ganin missed calls  dinsa ya d'auka yana d'auka yace "father komai normal dai ko ka Isa gida lfy ? "Normal sadiq komai  daidai na gode da kulawarka dan uwana , sukai sallama kmr ya nemi layin zahra dan yasan adaidai wannan lokacin idanunta biyu Killa ma tana can yawon ta zubar amman ya share yana zaune  zata zo ta samesa .."

Can  bangaren  IPO  kuwa  yana ganin dawowar jaguwa yasan sun yi missing dinsa wayarsa ya ciro ya shiga neman number dcp baba abare  yana d'auka yace "sir Kuna Ina ne  ? daga can bangaren dcp yace muna kan titi har yanzu bamu ga dawowarsa  ba "gsky kunyi missing dinsa dan ya dawo gida "shit ...." dcp ya furta a fusace sannan ya cigaba da magana "amman a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe "wannan haka ne sir idan kere na yawo zabo na yawo  wata rana zasu  had'u ne ",ai kuwa haduwarmu bazata yi kyau ba dan bazan Kai shi ga office din  hukuma ba bare a samu damar bada belinsa tarwatsa masa Kai zanyi kowa ya huta yana gama fad'ar haka ya katse Kiran a fusace  yana bawa yaransa umarni ."

*****

Washegari da misalin karfe takwas ya fito zuwa falonsa sanye cikin gajeren trouser  baki da riga fara mai hula da ratsin baki ,sanye da takalmi fari mai azaban kyau yayi kyau sosai sai dai fuskar nan tashi a murtuke tamkar jinin sarauta sannan kallo d'aya zaka masa kasan zuciyarsa a dagule take jira kawai yake a tabashi ya hau mutun , ya d'auki remut ya kunna tv ya Kai  chennel  zuwa na labarai  yana ƙoƙarin  zama friends dinsa suka shigo suka zagayesa har kamil Suma cikin shiga ta alfarma atare suka had'a baki gurin cewa"ya lafiyar yarinyar nan ?Kamar bazai ce Komai ba har sun fidda rai da zai Yi mgn suka ji yace "alhamdulillah har yanzu dai tana bacci  ".Shiru sukayi dukkaninsu babu wanda ya sake yin magana sai numfashi da suke fitarwa idanunsu na kan tv yayinda  anas ke son yi magana akan zahra zata zo dan tun safe ya kirata ya sheida mata abinda ke faruwa  sosai ta daga hankalinta  ,amman yadda yaga jaguwa ya had'e rai yasa ya kama Kansa ya ciro kwandala  a cikin aljihunsa ya murza akan center table din dake gabansa  take ta fara juyi a karshe ta kife ya tsurawa kwadalar Ido kawai yana kallonta  ."

Suna zaune sai ga zahra ta shigo cikin doguwar riga marun colour tana karairaya tana gama tsayuwa a tsakiyar falon onexpecting taji jaguwa ya mike  ya ɗauketa da wani gigitacen mari da sauri ta dafe daidai Inda ya mareta tana dubansa "ki fita rayuwata  Zahra , ki tsaya matsayinki"  zahra  tace "me yayi zafi haka Adnan ? "dazu anas ya kirani yake fad'a min abinda kake zargina akai amman ka sani ......
"wani marin ya K'ara kifa mata sai data ga taurari masu duhu "amman kasan me din ubanki ?"me zaki fad'a min na yarda dake maci Amana kawai,  daga karunwaci kin koma bin bokaye saboda ke katuwar jahila ce wannan ya zamo Karonki na farko ya Kuma zamo na karshe babu ruwanki da yarinyar nan wallahi muddin wani abu ya sameta sai na kasheki da hannuna , wai ma meye hadinki daita? ni kike wa kwakwa ni Kuma nace banayi ko dole ne  sai na aureki ?ya tambayeta yana sake tsare girar kasa da sama. "duk ta rud'e sai wani gumi take fitarwa cike da matsanacin firgici tace "ka yarda wallahi babu hannuna ci...ciki " ta k'arasa maganar tana in Ina gani yadda yake mata mugun kallo yasa ta soma neman hanyar guduwa dan kallon  fuskarsa kad'ai ya Isa ya tsorota mutu da sa mutun ya shiga hankalinsa sam sam babu alamun wasa atare dashi kafa yasa mata sai gata ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kallonsa cikin muryar kuka tace "ni kad'ai kake bi bare kayi tunanin nice na aikata abinda kake zargina? Ina Jin tsoron Allah Adnan bazan iya ......"shiiiiiiiii ! banason Jin komai d'aga bakin makira irinki ."
"Zahra!
ya kira sunanta muryarsa a tsarke ta zuba masa Ido tana amsawa da" Na'am "babu tsoron Allah"n daya halicceki acikin zuciyarki dan hk nasan zaki iya aikata komai akan cikar burinki ,masu kyakkyawan zuciya da tsoron Allah su suke tsoron aikata mugunta ke Kuma baki da ko daya aciki "yayi shiru yana numfasawa sannan ya cigaba da mgn "daga yau idan kika sake shiga harkata zan mugun baki mamaki kuma dan Allah karki cire hannunki akaina da duk wacce zaki ganni idan Kuma kinki yiwa kanki kiyamul lail zaki hadu da cuuttuka ,sannan zan ganar dake da yaren da zaki gane yana kaiwa nan yace " ki tashi ki bani guri bana son ganin wannnan fuskar taki ".

"naji zan tafi amman kayi hakuri kayi bincike sosai akai muddin aka tabbatar maka  Ina d'aya daga cikin wad'an da suka aikata wannan laifin ka min hukuncin da yafi wannan "wani bincike zanyi bayan nasan babu me shegen naci a rayuwata kamarki ?ya matsota sosai ya cafki makoshinta idanunta suka yo waje "ki fad'a min gsky kece kikayi mata asiri ?ta shiga girgiza Kai alamun a'a "bazaki fad'a gsky ba ? girgiza masa Kai ta sake yi  anas ya taso ya rikesa karka yi kisan Kai Adnan "ka rabu daita  karka kashe yar mutane "kace mata ta fad'a min gsky da bakinta
"me yasa  tayi wa yarinyar mutane  asirin data kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? ya fad'a yana filinging daita sauran kad'an kanta ya bugi bango anas yayi saurin riketa  yana bawa jaguwa hakuri .wani sanyayyayen numfashi Zahra  ta sauke da kyar tana jin dadi aranta burinta ya  cika tunda ya kusanceta rabuwarsu tazo duk nacinsa dole su rabu  ,abokansa kuwa da Ido suka bisa suna mamakin jin furuncinsa ,me yasa kika yiwa yarinyar mutane  asirin da ta kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba?  suka tambayi zukansu suna dubansa  fuskokinsu d'auke da qarin bayani .

"Anas kaji abinda yake fad'a , dan jarabansa ya ciyosa ya kwana  da  yarinyar mutane shine zai d'aura laifina akaina , kasani babu  hannuna  acikin wannan aika aikan  " ,jaguwa  juya mata baya  ya tsuke fuska alamun bai son jin komai daga bakinta muryarsa a tsawace yace "anas ka sallameta daman  Kaine kake gayyatota  zuwa gidan nan " da sauri anas  ya riko hannunta ya nufi kofar fita daita "anas ka sakeni na fahimtar dashi gaskiya "bazai ta'ba fahimtarki ba kije kawai dan Allah nima daga yau karki sake kirana na yanke muamula dake bazan Kara kiranki ba banason na samu matsala da abokina, aminina ,farincikin rayuwata .
fixge hannunta tayi daga cikin nashi adaidai lokacin da suka fito zuwa haraban gidan ta tsaya a hassale tana  dubansa "ka dade baka daina kirana ba ,bazan  kiraka ba shima bazan kirasa ba Amman na rantse sai Adnan ya dawo ya nemeni da kansa ka rubuta ka ajiye a Inda bazai goge ba ..."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️16
Chapter 42 · 0% Book details