Sashe 9
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Jaguwa zaune cikin d'akin daya tanada domin tautauna bayanai masu mahimmanci akan aikinsa ,gabansa laptop dinshi ne ,yana faman operating yana sauraron bayanan jubi inda yake bayani akan alhaji tanko gote wanda ya kasance shararraren dan kasuwa wanda duniya tasan da zamansa sannan ya tara tarin dukiya bilaadadin anan gida nigeria da kasashen ketari ,ya mallaki qadarori da dama da companies a kowace jaha dake ƙasar nigeria " bincikenmu ya nuna mana mutumin baya zaman gidansa da daddare sai da rana bayan haka akwai tsaro mai tsanani tun daga bakin get doping estate har zuwa cikin gidansa ta kowani bangare dakarunsa zagaye suke da gidan bayan boyayyun camerori dake lugu da sako na gidansa, me zai hana mu hakura da wannan taget din muyi facing din wani yayi shiru hade da numfasawa sannan ya cigaba da magana "jaguwa a ganina mu hakura da wannan aiki kawai ko me kuka ce yan'uwa ? ya fadi haka yana kallon sauran yan'uwansa dake zaune suna sauraronsa , duk suka gyara "gaskiya mu hakura tun da tsaro yayi yawa inji cewar kamil ,Anas ya numfasa yace " kuna nufin bazamu yi nasara ba akan aikin da muka ɗauki tsawon lokaci muna jiran aiwatar dashi ? a qalla wannan shine karo na hudu da muke rusa budget din aiki akan Alhaji tanko gote gaskiya a ganina bai kamata muyi wasa da damarmu ba kawai mu fara shirin aiwatar dashi kuma a cikin satin nan "dan Allah malam ka natsu kayi nazari akan operation din nan jabir ya katse masa hanzari ta hanyar fadar haka"the best solution mu hakura tunda jubi da kamil suka nuna abar shi , kai koni nayi supporting dinsu mu hakura kawai muyi facing din wani aiki ......
Sai lokacin Jaguwa ya d'ago kyawawan idanunshi masu matukar kyau jere da gashin ido ya tsura musu yana kallonsu daya bayan daya sai daya ɗauki tsawon minti biyar yana kallonsu sannan ya mike tsaye yana rufe laptop d'insa ya soma magana a tsanake kamar ba wannan shararraren tantirin daya addabi manya kusoshin gwanati da manya attajirai ba "duk naji bayaninku daya bayan daya amman kusani wannan aikina ne jiya ba yau ba , da muna saka tsoro a zukatanmu da bamu kawo wannan matsayin ba , matsayin ƙasar nan take bulayin neman Jaguwa ido rufe, burin duk wani dan sanda mai matsayi ya samu nasarar gano inda muke ,ko'ina acikin kasar nan magana ɗaya ne ana son ganin wanene wannan mutumin daya addabi kasa da kasa gidajen radio dana tv , news paper ko'ina magana ɗaya ne amman har yau basu yi nasarar gano mu ba abinda zai faru yanzu shine ni da kaina zan tunkari tanko gote ya karasa maganar a fusace yana dukan table din dake tsakiyar su jabir sannan ya juya musu baya rugume da hannunwansa duka .....
Duk suka zaro ido a frigice suna dubansa gaba-daya jikinsu yayi mugun sanyi da jin furucinsa Anas ya mike ya karasa inda yake ya tsaya a gabansa "kalle ni Jaguwa ya d'ago kyawawan idanunshi ya zuba masa batare da yace uffan ba "bazan barka ka tafi kai ɗaya ba ko kowa yaki binka ni zan bika amman me zai hana mu hakura nima jikina yayi sanyi bamu taba samun saɓanin ra'ayi akan halqallarmu ba sai yau me zai hana mu hakura kawai ....
"Kawai abar aiki saboda tsoro ko me ? yayi masa tambayar yana tsareshi da kyawawan idanunshi ,a hankali Anas ya gyada masa kai "ba saboda tsoro bane "saboda me ye faɗa min Ina jinka ? "me yasa ni ban karaya ba ku zaku karaya ? "me yasa ni bangujewa aikin ba ku zaku guje masa ? wannan karon a tsawace yayi maganar yana dubansu ransa a matukar bace "daman mun tsara haka ne dan wata rana zamu sakawa zukantanmu tsoron aiwatar da qudirinmu ? dukkaninsu suka gyada kai alamun a'a suna dubansa da mamakin karfin halinsa "mun san duk abinda ka faɗa gaskiya amman .... "listing yayi saurin daga musu hannu " banason jin komai zanje Kuma ni kadai zan aiwatar da komai zan nuna muku kwarewata ta wuce yadda suka tsamamnin .....
Duk wannan maganar dake yake yinta cikin isa da izza da rashin kuruciya yake yinta ,dan kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ya mallaki hankalin kansa sannan yasan meye rayuwa babu alamun kuruciya atare dashi , ya sake kallonsu daya bayan daya "ku fito ku faɗa min cewar matsorata ne , " a she ku din kananan yan iska ne iskancinku bai taka kara ya karye ba kuka hau matsayin da masu dakakkiyar zuciya suke hawa ...
"A she akwai abinda zaku ji tsoro bayan kuna dani kuna tare dani ? Zan fita ni kadai raina nayi gaba da gaba da tanko gote ya karasa maganar a tsawace cike da fushi jikin Anas ya dinga kyarma ya shiga rarrashinsa dan yasan halinsa abu kankani ke bata masa rai har yayi nasarar dagula nasu lissafi yana gama maganar bai tsaya ya saurari rarrashin da Anas yake masa ya fice daga d'akin kallon juna suka shiga yi kamil ne yayi karfin hali yin magana "yanzu ya zamuyi da alamun ya hau dokin nakin daya saba ? "Ku bar shi tukunna zuwa anjima mu gani zan san yadda zanyi na shawo kansa, ni kaina na hakura duk abinda mutun ɗaya mutun biyu har uku sukayi magana akanshi mafi alkhairi a hakura dashi inji cewar Anas a hankali suka cigaba da tautaunawa ..
Kai tsaye special room d'insa dake kallon wanda tanweer take ciki ya shiga ya zare rigar jikinsa ya saura daga shi sai vest fari da dogon wando ,ya ɓalle agogon dimond din dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye akan mirrow dinsa tare da wayoyinsa ya dauki remut ya kara karfin ac ,ya karasa inda karamin fridge dinsa yake ya ɗauki kwalban win mai sanyi ya ɓalle ya kafa a bakinsa bai ajiye ba sai daya sha rabi sannan ajiye yana sauke numfashi sannan ya kwanta ruf da ciki akan bed yana tunani yadda zai tunkari gidan tanko gote a safiyar gobe ,kusan minti goma yana kwance sannan ya yunkura ya mike tsaye zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske, sai dai sosai yake jin jarumta a sansar jikinsa sam bai ji wani karaya ba ko sarewa ko jin rashin nasara , kallon dakin yayi sosai kwakwaluwarsa ke sake lulawa duniyar tunani akan lamarin, motsin da yaji a bayansa shi ya sanya shi saurin juyowa , ganin Anas ne ya dauke kansa , zama tayi a bakin gado a lokacin da Anas ya karaso ya zauna kusa dashi tare da kamo hannunsa ya daura cikin tafin hannunsa "kayi hakuri abokina kuma aminina "da'akayi me kenan kake bani hakuri ? yayi masa tambayar yana furzar da iska mai zafi tare da fixge hannunsa cikin nashi "ni dai kayi hakuri naga ka ɗauki zafi "akan me zan ɗauki zafi ya sake katse shi yana haɗe hannuwansa guri daya "ni babu wani zafi dana ɗauka aiki ne babu fashi gobe ko jibi zan aiwatar dashi akan idanunku zanje na dawo ya karasa maganar yana murnushin gefen baki alamun nasara yake ji ajikinsa "ka fahimceni abokina "dan me zan fahimceka akan
mutumin da babu Allah a ranshi? kuke jin tsoron tunkarasa .....
"nasani amman ka tsaya mu shiryawa tunkararsa tukunan irin su Alhaji tanko ba'a tukaransu haka nan dole sai anyi shiri na musamman "listing anas akan wannan mutumin bazan taba fahimtarka ba, batu akan tsara tunkurarsa an wuce gurin sai dai kuma wani aikin "shikenan shikenan ni zan bi ... , kar ku bini ko kunce zaku bini ma bazan lamunta ba ,ya karasa maganar cikin fushi , Anas ya sauke ajiyar zuciya "shikenan Allah ya baka Sa'a "ameen ya fada yana mik'ewa haɗe da shiga bathorrom ....
**********