← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 160

Sashe 22

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi mata  yaki cewa komai ya cigaba da abinda yake ta sauko daga kan gadon ta tsaya a bayansa har lokacin babu komai sanye  ajikinta tana kokarin haɗe jikinta da nashi
  ta kai hannunta jikinsa tana kokarin kifesu a qirjinshi dan murza kan nipple's dinsa yayi saurin juyowa tare da tsareta da kyawawan idanunshi yana mata gargadin abinda take son aikatawa bata damu da irin kallon da yake mata ba ta kai yatsanta kan nipple's dinsa zata soma zagayewa taji  ya  ɗauketa da wasu maruka guda biyu ajere tasa tasa  ..
Saurin dafe kuncinta tayi  tana  fidda numfashi da kyar gabad'aya marin ya dimautata ya  gigiceta da kyar ta samu ta sauke numfashi da karfin gaske idanunta na kanshi  "minti biyu kawai na baki ki tattara abinda kika san naki ne a dakin nan  ki bar min gida kar na sake ganin kafafunki  ya  karasa  maganar a fusace sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa ya isa gaban wordrobe dinsa ya bude  ciro wasu kananan  kaya bakake wando masu taushi da kyau    ya soma shirya kanshi.

jikinta a sanyaye ta dauki rigarta ta saka tana kallonsa har ya gama shirinsa tsaf   bandir din yan dubu dubu guda biyar taga  ya dauko ya watsa mata "kije dan Allah ki bar rayuwata bana son damuwa idan ina bukatarki zan nemeki da kaina "naji zan tafi amman dan Allah ka dinga  ɗaukar   kirana .."
  "Bazan miki alkawari ba saboda ina da abubuwan yi idan bukatar ɗauka yayi zanyi  "bata ce masa uffan ba ta dauki jakarta batare da ta dauki kudin ba  a dan zafafe yace "kudin fa"?
Ta juyo kamar zatayi kuka  "bana bukatar su dan nafi bukatarka dasu ..."tana gama fadar haka ta sake juyowa idanunta cike da ruwan hawaye, ta bude kofar d'akin zata fita  hannunsa ya kai ya shako wuyanta ya dawo daita cikin  bala'in da tashin hankali ya amshi jakar hannunta ya kwashe dukan kudin ya zuba mata  cikin jakarta , tayi shiru kawai tana kallonsa kamar ta daura hannunta bisa kanta ta fashe da kuka , yanayinta ya bashi tausayi  sosai kamar ya lalla'bata su rabu lafiya  sai kuma yaga hakan bai dace ba kamar wata dama zai sake bata.."

Muryarta a raunane tace  "meye laifina adnan da kake wulakantani  ? "shin laifi ne dan zuciyata ta soka ?  ta k'arasa maganar wasu zafafan hawaye na zubowa a saman face d'inta, girgiza  mata kai yayi yana furzar da iska sannan ya motsa lip's d'insa a hankali  "laifinki daya  zahra da kike takurawa rayuwata alhalin kinsan ni din mutun ne da bana son damuwa "  sannan baki da wani sauran mutunci da darajan da zan soki zahra ,gaskiya ɗaya ce wallahi zahra bana sonki koda kuwa  akwai budget din soyayya arayuwata bare babu  mafi mahimmanci abu arayuwata shine  ahlina  "
ba iya soyayya kawai zata iya da zuciyar jaguwa ba Bare lalacewata bata kai na amincewa auren mace irinki ba ,"zahra da ƙaruwar gida da karuwar waje akwai bambamci idan aure kike bukata me zai hana ki koma gaban iyayenki ki tuba Allah zai duba lamarinki ya baki wanda yafini wanda zai soki da d'aukacin rayuwarsa  amman batu na soyayya ko aure tsakanin zahra da adnan babu....."
"To mu'amular fa ?"idan bazaka aureni ba ka barni na rayuwa da kai shi kadai zai sanyaya zuciyata sannan zai sa na  dangwama cikin farinciki "shima bazan yi alkawari ba dan ita kanta zinar ina son na daina shiyasa kika ga ina gujewa haduwata dake ,ta durkushe a gabansa "karka min haka adnan karka juya min baya ka  taimakeni ka taimaki rayuwata wallahi bazan iya rayuwa babu kake "enough Zahra ya fada a tsawace "Haba me kike son nace miki kinga tashi tashi dan Allah yadda taga ya soma birkicewa yasa ta tashi da sauri tana fuskantar shi ido cikin ido yake kallonta"Ni ne na samo having sex dake ? "Ko ni ne na baki ticket din fitowa yawon duniya ?"ko ni nace dole sai kin soni ? yayi mata duka a lokaci tayi shiru hawaye na gangaro mata "kin yi shiru ki bude baki ki bani amsa yayi maganar yana zaro mata ido tayi saurin girgiza masa kai"okay tunda kinsan  bani bane me yasa zaki ce kar na miki haka kar na juya miki baya ?"daga yau Karki sake tunkarata da batun soyayya bare wani aure okay ?"oya out idan kika sake tunkarata sai ballaki idiot Kawai ..

Tana gama jin abinda ya faɗa  ta juya da sauri ta fito daga d'akin tana goge hawayen idanunta a bakin kofar suka kusan ci karo da Anas ,da sauri ta wuce shi ya biyo bayanta yana  kiranta "zahra! zahra !! amman ina  taki tsayawa ta wuce  tana kuka  yayi saurin biyota ya sha  gabanta "plz Ki tsaya ki saurareni menene? " me yayi miki kike kuka plz tell me ko akwai abinda zan iya yi " muryata cike da kuka tace  "tabbas nayi kuskuren  afkawa cikin soyayyar adnan "
"Wani irin mutun ne shi    nayi iyakar kokarina akan soyayyarsa amman sam yaki fahimtata na rasa yadda zanyi adnan ya fahimci irin matsanancin soyayyar da nake masa gabad'aya zuciyata ta kasa hakura dashi ka faɗa min me ya kamata nayi  ya aure ni ? duk Sanda zamu kasance tare  sai ɓacin rai ya biyo baya" why !why!! ? Ka faɗa min abinda ya kamata nayi ?"Ni kaina   babu wannan tsarin arayuwata ban shiryawa aure a yanzu ba amma  na rasa dalilin da yasa  na nacewa mutumin da bai ɗauki kowa da mahimmci ba ? gabadaya ta fita haiyacinta sai maganganu take faɗa masu taba zuciya "kiyi hakuri muje muyi magana aciki "babu inda zani dan nasan kona koma wani sabon bakinciki zai kunsa min , kawai ka barni na tafi abuna  ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa gefe ya bata hanya dan ta wuce kamar yadda ta bukata dan shima yasan ko ya maidaita sabon bala'i za'a yi a hankali ya juyo ya nufa cikin gidan
Yana ƙoƙarin tura kofar dakin jaguwa ya  fito yana ciccin magani tamkar wani jinin saurata.

"me ka yiwa yarinyar mutane jaguwa  ?',me tace nayi mata yayi masa tambayar atakaice , cikin natsuwa ya raba ta grfenshi yayi gaba "ko bata faɗa min  ba nasan kayi mata wani abu shiyasa ta fita cikin fushi da ɓacin rai  dan Allah ka dinga sausauta   yarinyar nan tana bala'in qaunarka "kace mata daga yau  ta daina son adnan  dan babu   wani amfani da zai mata ya karasa maganar yana ci-gaba  tafiya " Anas ya biyosa  da sauri  "na rasa dalilinka nakin yarinyar  nan bayan irinsu ne kawai zasu iya rayuwar aure  da irinmu, ko kana tunanin akwai wata mace mai mutunci da daraja da zata iya da irin rayuwar da muke ?

Jaguwa ya tsaya cak tare da juyowa ya fuskanci Anas sannan ya  zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya zubawa Anas idanunshi yana kare masa kallo tsaf  "kai kake ganin haka amman lalacewata bata kai na auri mace kamar zahra ba, karka manta inda muka tsinto   zahra da irin rayuwar da take   duk gidan rawan fela   kowa yasan wacece Zahra,  nasan nima  mai tarin zunubi ne agurin Allah  amman ta nemi mijinta a gaba  adnan baya sonta kuma bazai taba sonta a rayuwarsa ba kai gabad'aya ma babu wata soyayya a tsarin rayuwata  "

"Wannan kuma karya ne dan da alamun ma a yanzu zuciyarka  ta kamu da soyayyar diyar Minister of health dake cikin gidan nan  "dariya jaguwa  yayi wanda ya bayyana tsantsar kyawunsa sannan   a hankali ya sake gyara tsayuwarsa ,fuskarsa cike da mamakin jin furucin Anas  ",this is rubbish anas what are you try to say ? wannan maganar  naka ba gaskiya bane abinda nake son ka sani zuciyar Adnan amad tayi nisa a kiyyaya  babu wani mutun mai darajan da zan so kamar ahlina idan ma soyayya ce wannan yarinyar tayi min  karama Anas , kuma idan duk duniya zasu taru akan na sota itama  bazan sota ba "ya wuce ta gefensa ya soma tafiya da baya baya  kamshin turarensa na tashi ya nufi dakin da tanweer take ya daura hannunsa akan handle din kofar ya murd'a ya shiga dakin Anas bai daina kallonsa ba har ya karasa shigewa dakin ya maida kofar ya rufe .."

Cikin natsuwa yake  kallon inda  zaune  take akan kujera ,juyar da kanta gefe tayi kamar bata ganshi ba , ya jingina jikinsa da bango dakin  yana Kallonta ,sosai yaga ta rame akan ranar daya d'aukota sai dai fuskarta tana nan da kyawunta ..."
ganin taki kallon inda yake yasa shi takowa  a hankali ya tsaya a gabanta shiru taki dagowa ta kalleshi ya cire hannunsa daya  acikin aljihun wandonsa tare da d'ago ha'barta ya tsura ma kwayar idanunta nashi idon yana Kallonta , da ido yayi mata alamar taci abinci ? bata fuska tayi cikin son nuna masa  abinda yake son sani bai shafesa ba, furzar da iska yayi yana tabe bakinsa sannan ya cire hannunsa ya buɗe kwanon tangaran din  dake ajiye akan table ,abincin na nan kamar yadda akawo shi   ya waigo ya kalli inda take a hankali ya maida murfin ya rufe "you don't eat ?why don't you eat?" I don't want to eat food in this situation "why ? ya tambayeta idanunshi na kanta kamar zai had'iyeta  "I'm not hungry"bakya jin yunwa ? ya sake tambaya  ta yatsina fuska cike da shagwa'ba.

"yarinya  idan kika sake ɗaukar lokaci baki ci abinci ba zaki mutu just for nothing yayi maganar tare da zama a bakin gado ya fuskanceta "tun safe  rabon da ki sanyawa cikinki wani abu hakan fa babu kyau "it's not good for your health okay ? Ya kamata kici wani abu saboda taimakawa rayuwarki a matsayinki na likita kinsan yunwa na daya daga cikin abinda ke saurin kashe dan adam ko ba haka ba "?
Chapter 22 · 0% Book details