← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 160

Sashe 96

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

a tsatsaye ya samu su jubi saite da bindiga ak47 sun zagaye sorrounder gurin suna ganinsa suka fara harma wucewa ,eku yayi saurin bud’ewa jaguwa gaban mota sai dai bai shiga ba ya janyo kwalar rigar ajirebi a fusace ya ‘barka rigarsa ya daure hannunsa me tsiyayar da jini dan kar ya ‘bata musu aiki sannan ya karasa ya bude boot din mota yace “shiga!”
babu mutsu jikinsa na kyarma ya shiga ya maida murfin boot ya rufe ya shiga gaban mota alokacin da kowa ya gama shiga shi kadai ya rage da mugun gudu suka fita daga hotel din suna fita sai ga motocin police da jiniya sun karaso bakin get .
kai tsaye shigowa sukayi kasancewar get din a bude yake,
suna kokarin fitowa daga mota securities suka fito daga maboyarsu alokacin shima manager ya fito da sauri tare da yi musu gutun bayani abinda ya faru jikinsa na kyarma ,daya daga cikin securities yace “kuyi sauri ku bisu abaya dan sun saka wani acikin boot din motarsu sun wuce dashi jeep ce motarsu land cruise .
cikin sauri suka koma cikin mota ,
sauran da basu gama fitowa ba suka juya motarsu securities na nuna musu motarsu jaguwa datayi nisa ta kusan kure titin ai kuwa suka bi motar da mugun gudu.”
Yadda motarsu jaguwa ke gudu akan titi haka motocin yansanda guda uku ke falfala gudu kamar zasu tashi sama tare da jiniya mai tsanani ,nan take tsirarrun motoci dake gudu akan titi suka shiga basu hanya dan da ganin irin gudun da suke bana lafiya bane sannan zai iya daga hankali duk wani mutun mai tsoro ,gudu eku yake sosai amman gani yake kamar ba gudu yake ba dan gani yake kamar za’a cimmasu ne.”
A dan rikice yace “boss jamian tsaron nan fa na daf da cimmana “
“wani dogon tsaki jaguwa yaja tare da cewa “ka cigaba da tafiya kawai karka tsaya ai kuwa ya qarawa motar gudu har suka karaso pape jucton wanda dole tasa eku ya tsaya sakamakon masu bada hannu, hakan ya bawa ‘yansanda dake biyedasu damar cimmasu .
jamian tsaro suka fito suka zagaye motar tare da saita bakin bindiga suna basu umarnin su miko kansu kafin su bude musu wuta.
gbdy duk wani wanda ke cikin motar babu wanda zuciyarsa bata tsinke ba ,hankalinsu ya bar gangar jikinsu suka lula tunanin abinda zai faru yayinda wasu daga cikin mutane da basu da tsoro suka yi cirko cirko a bakin titin suna son sanin abinda ke faruwa sai dai babu me basu amsa sai jami’an tsaron dake gurin su kuma bata su suke ba burinsu kawai
yan fashi su shiga hanunsu.”

Tashin hankali wanda ba’a saka mashi rana ,Jin ana taba murfin motar da bindiga yasa anas dake kusa da jaguwa ya rike masa hannu gam jikinsa na wani irin rawa , shi din ba matsoraci bane amman yana jin tsoro ,yana jin tsoro da kunyar shiga hannu hukuma “babu abinda ke fita daga bakinsa sai “ya Allah ka taimakemu karka sa mu shiga hannun hukuma ,allah kasan zuciyarmu allah ka rufa mana asiri anan duniya da lahira sosai hankalinsa ya tashi wanda yayi silar daga hankalin jaguwa dan idan akwai abinda ya tsani gani shine tashin hankalin anas nan take gabansa ya shiga faduwa da sauri da sauri ya waigo ya kalli anas hawayen nadama ya gani kwance acikin kwayar idanunshi nadama yake ji wacce bai taba jin irinta ba daya byn daya ya kallesu gbdy a firgice suke sai dai alamunsu ya nuna ba mutuwar suke jin tsoro ba domin mutuwa ta lokaci daya ce musibar da zasu shiga suka fi ji !
“Me zasu cewa hukuma?”
“Me zasu cewa iyaye da yanuwa da abokan arziki “?lallai rana dubu ta barawo ce rana daya ta maishi yau dai gasu suna daf da shiga hannu basu an kara ba suka jiyo sautin muryar jaguwa cikin tsinkewa zuciya da faduwar gaba yace“Ku kwantar da hankalinku babu wanda ya isa ya cutar damu inshaallahu akwai mafuta ,Ku dafani gbdyanku,cikin sauri kowannensu ya kai hannunsa kan kafadarsa suka dafashi kamar yadda yace,tamkar walkiya motarsu ta bace akan titin .”
jamian tsaro da mutanen da hankalinsu ya karka ta zuwa garesu sun sha mamaki ganin wannan abun almaran “wannna wani sabon abu ne suka gani da basu taba cin karo dashi ba ,sun sha haduwa da barayi suna bacewa amman na wannan ya fita dabam dana sauran tunda har motarsu basu bari ba bare ta zamo musu sheida wajen da motar take tsaye suka cigaba da bi da kallo kamar ance musu idan sun cigaba da kallo gurin motar da mutanen ciki zasu bayyana.”
“ikon allah lallai wadan nan barayin sun sha bam bam da sauran barayi da suka saba batakashi dasu“.
wani daga cikin jamian tsaron ya fada yana sake shiga rudani da shiga tashin hankali mara misaltuwa jiki a sanyaye suka juya suka fara tafiya kamar wadan da aka zarewa lakkan jiki suka koma cikin motacinsu’ har suka bar gurin mamaki abinda ya faru suke .”
Chapter 96 · 0% Book details