← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 160

Sashe 45

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaro Ido tayi waje cike da mamaki  tana maimaita  abinda yace a zuciyarta " ki maida wadan nan  idanun naki  kiyi abinda nace  yana gama fad'ar haka ya juya zai fita ya jiyo sautin muryarta tana cewa  "akan wani dalili zan had'a da wankan  tsarki ni ba janaba  ba ?"ya juyo a natse  yana kallonta tai saurin kare  qirjinta da hannuwanta , ya kwa'be baki yana kashe idonsa d'aya  a ransa yace" abinda na kwashe rabin dare Ina sarrafasu  shine dan  manufarci  kike wani  boyewa  ,numfashi ya furzar ya sake juyawa yana cewa"kiyi k'okari  kiyi wankan dana tsarki idan Kuma kin Isa karki yi zan gane "baza'a yi  ba , babu  janaba  ajikina  dan hk babu wani wankan tsarkin  da  zan yi  daf da zai bar d'akin yaji ta fad'i haka "kwa'be fuska yayi " yarinyar nan da alamun sai na baki tarbiya kafin na maidake  gidan ubanki  dan kanki na  mugun rawa."

d'akinsa ya koma ya shiga wanka sai daya d'auki minti ashirin yana bayi  sannan ya fito yana  goge jikinsa da karamin towel fari tasss yana tunanin  tanweer,  hakan nan  yake qara Jin qaunar yarinyar na mamaye  ilahirin jikinsa sai dai yayi ta k'okarin yakice hakan yana karyatawa , ya shirya kanshi cikin wasu  Kanana kaya wando da riga  farare  sol  ya feshe ilahirin jikinsa da turare , ya  zauna a bakin gadansa  ya d'auki d'aya  daga cikin wayoyinsa   ya kira number aliyu number  bai shiga  ba da alamun akwai matsalar  network ya mike tsaye ya fito yana neman layin eku kira d'aya ya d'auka tare da cewa "boss Ina yini  ?"Lafiya ya fad'a atakaice , yana tafiya yana  bashi umarnin  ya d'auki  kudi yaje adidas ya siyo  masa  abinci  ya k'arasa maganar yana  tura  kofar d'akin da tanweer take ,Koda ya shiga d'akin  tana kwance ta lullu'be jikinta da blanket  kanta ne kawai a waje tana rawa sanyi .
gashin kanta yabi da Kallo bai ga alamun ruwa ba  ya had'e fuska sosai ya k'arasa ya Kai hannunsa  cikin sumar kanta ya cusa har yana ta'ba fatan kanta  bai ji alamun ruwa  ba ya cire hannunsa  yana cewa  "ke........" !
ta d'ago kod'ad'un idanunta ta zuba masa batare data amsa ba " wasa nake dake Koni sa'anki ne ?to ni me nayi Kuma nifa wallahi bana son takura tunda Kai ba sa'ana  bane  ka mayar dani Inda ka d'aukoni mana "tayi maganar jikinta na karkarwa ta janyo blanket ta sake rufe jikinta har kanta a zuciye ya fixge bargon yayi filinging dashi yana jan tsaki  "ki tashi kije kiyi wankan  tsarkin da nace  ko na 'bata miki rai yanzu  "kamkame jikinta tayi guri d'aya  ta lafe akan katifa  bata da alamun tashi ."

wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda yasa tayi  zumbur  ta mike tsaye har hantar cikinta na  kad'awa  ta kwa'be masa  fuska tana kallonsa, da yatsansa ya nuna mata hanyar bayi simi simi ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar dan kwata kwata bata ga al'amun wasa atattare dashi ba a yadda take kallonsa zai iya marinta har ma ya had'a da duka  yabi  tafiyarta  da kallo gbdy yanayin tafiyarta ta canza kallo d'aya me hankali zai mata ya fahimci halin da take ciki ,bai  d'auke  idanunshi ba har  sai daya shiga bayi ta bugo  kofar  da karfi .
numfashi ya sauke ya koma bakin   gado ya zauna yana neman layin amminsa suna waya ta fito d'aure da towel tana rawar sanyi   ya tashi ya rungumota  jikinsa ya zaunar  daita a gefensa  ta rakube  ajikinsa tana karkarwa  ya janyo blanket ya lullu'beta tare da yi mata alamar ta kama kanta waya yake  sun dade suna waya da amminsa tana sauransu  Kuma duk akan maganar  abinda za'a yiwa baqinsu masu zuwa neman auren shafiqa ne  acikin satin  ...
Lokacin da suka gama wayar tuni bacci ya  d'auke tan  ya kwantar daita  ya tashi ya d'auko mata wata rigar ya dawo har zai Saka mata ya tuna da magani dan haka ya  fita ko second biyu bai yi ba ya dawo rike da roba da gayen magariya yayi adduoi aciki  ya shafa mata sannan ya  Saka mata  kaya ya lullu'beta ya kashe  ac d'akin gbdy ya fita daga d'akin zuwa nashi  ya kwanta a falonsa akan  doguwar kujera."

Bai jima da kwanciya ba aka  soma  knocking kofar  falonsa , yana  daga kwance ya bawa mai yin knocking ɗin izinin shigowa eku  ne ya shigo cikin falon hanunsa  riƙe da farar leda, cike da girmamawa ya rusunawa  ogan nasa a natse Jaguwa ya mike zaune ya zura silifas ya amsa  ledar    yana masa  godiya  eku  ya juya ya  fice daga  falon.mikewa tsaye  yayi ya  fito ya shiga   ɗakin  tan batare da yayi knocking ba  kamar yadda  ya saba  koda yaushe zai shiga Kai tsaye ne , sai kawai ya tura  ƙofar  ya shiga ciki, tun sanda ya kawota  gidan yake jin   haushi Kansa da bautan da yake mata  amman a yau din jin zuciyarsa yake fessss  akanta zai iya mata komai ciki kuwa har da zama bawanta .
Tana kwance akan gado ta  kwanta  ruf da ciki, bacci ta keyi har lokacin  hankalinta a kwance,  murmushin gefen baki yayi   kamar tana ganinsa  haɗe da aje ledar  hannunsa" sarkin rigima da rashin kunya  ya fad'a a ransa , har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya yana  kallonta   tun daga yatsun kafaunta har zuwa  kanta komai nata abun burgewa ne ,   ahankali ya taka zuwa inda take kwance,  tafin kafansa d'aya  yasa ya ɗan  shafa  tsakiyar kafarta .
azabure ta farka ta zauna tana murza   idanunta dan  har lokacin Jan da sukayi  bai baje  ba , sake kallonta  yayi, "Ki tashi kije kiyi wanka kiyi alwala kiyi  sallah , ke fa na lura sallah bata dameki ba  dan  zaki iya  wuni  bakiyi sallah ba  ki kuma kwana bakya damuwa"  yayi mgnr yana mai  tsareta da sexy eye's dinsa."

Tsura masa idanunta tayi tana kallonsa  tana Jin haushin abinda yake mata sai ya fad'awa  mutun mgn yayi kmr bashi  yayi maganar ba, saboda yanda yake fizgo mgnr da kyar Kallon agogon d'akin tayi yanzu ne ma hud'u   ta wuce muryarta a raunane tace "gara ni ko banyi sallahr akan lokaci ba zan rama Kai fa ?meye amfanin sallahrka akan lokacin tunda kana aikata aikin  haram, wad'amuhu haramun ,washarabahu haramun wa guziya bil haramun wa'anna ....."ki min shiru anan  stupid  " ya fad'a a tsawace , ana tausayinki bakya tausayawa kanki "nace ka tausaya min ne? ko nace ka cigaba da rikeni dole ? Ko  nace dole sai ka zau....."Idan kin   sake furta wata kalma  anan sai na tattakaki idan km  kin mutsa bismillah  kiyi  "  yana gama faɗan haka ya fice daga cikin ɗakin ransa a bace, gsky yayi mugun  sakewa yarinyar dayawa shiyasa ta rainashi .

Saukowa tayi ta shiga bayi tai alwala ta fito tayi sallah  tana idarwa ta mike ta Isa gaban mirrow  ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, robobin take away ne acikin  har guda  uku,  ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, kad'an taci dan zazzzabi take ji sosai bata jin dadin  bakinta   ta sha ruwa kad'an  .
 kamar ta koma ta kwanta   ta tsinci kanta da fitowa, kanta babu dankwali  ta fito zuwa falo da kyar take taka ka'fafunta , yana tsaye agaban tv  ya bawa cikin falon baya yana ƙoƙarin danna code din bude wayarsa ,  jin motsin mutun  a falon yasa  batare da ya juyoba yace.   "waye ? "Waye byn wacce ka sato ka ajiye a gidanka  ita ce ta fito  ta sha iska tayi mgnr da kyar tana kokarin zama akan kujera "shekaru sun ja wallahi ya kamata ka tuba ka daina harkar fashi ,nasan da mahaifiyarka tasan wannan aikin kake yi da bata yi alfahari da Kai ba a karshe  kashe kanta zatayi dan bakinciki  ."

A matukar fusace ya nufo Inda take  tamkar wani mayunwanci zaki ya damki wuyanta yana Shirin danne makoshinta ya fasa saboda zafin daya ratsa tafin hannunsa ya tsura mata Ido kawai yana kallonta  "ka shaki ne mana ai ni yanzu a shirye nake da mutuwa gara min mutuwa akan cigaba da zama da Kai ,a farkon had'uwa ta da Kai naji duk duniya Kai  mutumin kirki ne  ,Kai ne  mutumin da zuciya da gangar jikina suka mace akansa saboda a  tunanin zuciyarka me kyau ce a she ba haka bane mugun  ciwo ne daskare  a zuciyarka wannan mummunar sana'artaka yafi min komai zafi acikin zuciyata wanda adalilin haka  yanzu  babu kyakkyawan zaton da soyayyarka   acikin zuciyata  sai zallar tsana  ,na tsaneka tsanar da zan iya ganin bayanka ka rubuta ka ajiye muddin na bar gidan  nan sai nasa  ka shiga ha......."

"karya ne " ya fad'a  a tsawace yana  nuna ta da yatsansa  "karya ne baki Isa ba , baki Isa kisa akamani ba how could you tell someone  tanweer ?"  you can't  do that , bazaki iya ba  sannan  jaguwa ba zai kamu ba cikin sauki ba  sai dai wani mutun dabam,  da zan kamu da ban Kai iyanzu ba" yayi mgnr yana furza mata iska a fuskarta  tayi saurin runtse idanunta gabanta na faduwa , ya juya mata baya tare da rike kugunsa da hannu d'aya ya fara zagaye falon zuciyarsa na tafarfasa can ya juyo a matukar fusace  "and     kikace me  byn zaki sa na shiga hannu ?" Kin tsaneni  tsanar da zaki iya ganin bayana Shima karya ne   zuciyarki  bazata  iya rabuwa da soyayyata ba  yadda  kika furta cewar kina sona haka zaki tabbata da sona  a karshe ciwon sona ne zai kasheki  saboda Ina ranki ,na  shigeki shigar  da bazaki iya cireni a ranki  ba ,zaki je gidan wani da tarin soyayyata gangar jikinki za'a Kai gidan wani zuciyarki kuwa tana nan  ....."ya nuna qirjinta daidai saitin zuciyarta .
Chapter 45 · 0% Book details