Sashe 84
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
commissioner ya dafa ta ya fara tmbyrta jaguwa alokacin daya Kuma sauran police suna dudduba d'akin ,sai dai babu shi ba alamunsa ita kuwa kuka take sosai da iyakacin karfinta, tayi biyu babu ta fada masa komai sbd tunaninta zai saduda ya sota amman duk da haka bai saduda ba bare hakan yasa ta zama wani bangare na rayuwarsa duk tmbyr da suke mata bata bud'e baki ta basu amsa ba."
A hankali police suka cigaba da duba lungu da sako kafin suga fitowar commissioner, jaguwa yana ganinsu yay sauri ya boye yana tunanin ko ya haura sai kuma ya fasa ba mamaki wasu police na dakon baya tunawa da yayi ba da fuskar da suke nemansa yake ba Kawai ya fito daga maboyarsa ya soma tafiya a natse Suna bincikensu yazo ya wucesu , sai dai bai tsaya shigar motarsa ba ya bar hotel din .
tare da commissioner zahra ta fito "kin kuwa d'aukar mana hotonsa na ainihi ?".
"Yallabai nayi k'okarin yin haka sai dai yaki yarda kasan mugun wayo garesa "kiyi k'okarin ki samo mana hotonsa domin da shi kad'ai zamu hanashi yawo acikin garin nan dan zamu baza hotunansa kinga duk inda ya shiga zamu Samu information har bakin motarsa suka k'arasa suna cigaba da tautaunawa ita gsky tana ganin zata hakura da kudin da zasu bata dan bazata Iya kasadar mikashi ga hukuma ba bama zai kamu ba gashi daga haduwarsu duk ta daburce ta fad'a masa komai kuma yaki yarda daita tasan ita dashi har abada ."
Tun akan hanya jaguwa ya Kira baba ya labar masa jikinsa yaki amsa bango "okay to shikenan baba zanzo ."
da misalin karfe tara na safe dady ya zaunar da tanwer yayi mata nasihohi sosai tare da jan hankalinta akan kuskuren da take neman aikatawa, har yayi ya gama bata ce uhm ba bare uhmm, abinda ma bai sani ba babu kalma daya data shiga brain dinta domin kuwa tana kan bakanta na son jaguwa da Kuma son aurensa muddin ya canza sana'a , duk ta inda zasu bullo mata ita dai babu sauyi jaguwa take so ."
Tunda jaguwa ya isa gida ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake yana zukar tabar wiwi yana cewa "ni zahra zatawa haka ?taso yaudarata fa dan dai ni din ba mayen mata bane ?anas ya matso ya dafa shi "wai meye zaka d'aga hankalinka akan zahra din banza babu abinda ta Isa tayi maka baga shi ka ganota ba " gani tayi zata bukunci lahira shine ta dinga fada min kalaman yaudara wai tana sona bata son na cutu ,kasan wani abu tun sanda ka kirani na ganota kawai na batsar dan naga gudun ruwanta ,Kai lallai ne na kama zahra na rabata da rayuwar waje idan ba haka ba daita za'a had'u a cutar dani, ina bukatar adanata zahra ....." ya fad'a da karfi yana dukan bango nan take hannunsa ya tsage sai jini ya fara zuba gbdy ya fita haiyacinsa anas ya amsa sauran wiwin hannunsa ya kamosa ya zaunar dashi "karka qara shan komai Ina zuwa ya fita da sauri ya bar jaguwa, bai dade ba ya dawo yayi masa dressing din hannunsa jaguwa ya kishingida yana tunanin yadda zai kamo zahra anas ya sake fita ya barshi .
Tunda anas ya fita bacci ya d'aukesa bai tashi ba sai gurin karfe hud'u Kuma har lokacin anas bai dawo gidan ba ,ya tashi ya shiga bayin dake manne da falo ya dauro alwala ya fito ya gabatar da azahar da la'asar shiru anas har bakwai bai dawo ba ,nan hankalinsa ya fara tashi ya shiga neman layinsa kira d'aya ya dauka yana cewa" gani nan shigowa " .
ko cikakken minti shabiyar basu da gama waya basu yi da gama waya ba ya shigo jaguwa na ganinsa ya mike ya k'arasa ya rike masa hannu" ina kaje kasan banason kanayi nisa dani ko".
"ba gani a gabanka ba muje kaga wani abu ya jashi zuwa wani daki dake kusa da wanda suka saka alqali, suna shiga jaguwa yaga zahra d'aure har bakinta sai faman zare Ido take .
Jaguwa ya kallesa ya juyo ya Kalli zahra sannan ya kwashe da wata hadaddiyar dariya ya rungume anas ajikinsa "gsky ka burgeni yau kayi abinda ni kad'ai zanyi ,yanzu zuciyata zata samu salama .
ya zare hannunwasa ajikin anas ya dawo Inda take zaune ya dan durkusa a gabanta ya cire pilastar da'a ka rufe mata baki.
"Sannu tantiriya ni zaki yaudara ko? idanunta suka kawo ruwan hawaye ta girgiza masa Kai alamun "a'a !
"har kamar ni zaki yaudara ?"dan Allah kayi hakuri ba yaudararka nayi ba" shiiii......" "rayuwarki tazo karshe zahra kinga kin huta da yawon d'aukarwa kanki zunubi domin kuwa anan zaki cigaba da rayuwarki yana gama fad'ar haka ya mike ya dafa kafad'an anas "muje abokina karka sa a kwanceta sai tayi sati a d'aure ,
"angama mutumina, nan suka sa kai suka fita daga d'akin suka barta tare da kullewa .
****
Tsawon sati biyu Kenan tanwer tana neman layin jaguwa Kiran na shiga bai d'auka saboda yayi busy sosai domin kuwa ya bazama gari neman yarinyar da baba yace, sai dai gbdy ya nemi yarinyar ya rasa ya sake dawowa baba ,ya tabbatar masa lallai sai ya nemota ta kowani hali, ko ya auri tanwer Ko kuma ya kwana daita hakan zai Karawa aikin jikinsa karfi na tsawon wata uku zuwa biyar hatta police hankalinsu zai dauke akansa ya cigaba da alqallarka hankali kwance sai dai byn wata ukun nan ya zama dole ya sake bukatar mai taurarin idan ba haka ba komai zai iya faruwa yanzu jikinka yaki amsar bango nan gaba bindiga zata fara shigarka .."
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke byn ya gama tunanin magangun baba sannan ya tashi jiki a sanyaye gabansa na wani irin faduwa yana jin Kamar ya hakura ya auri tanwer ya koma kan kujera "to ai tanweer ta fad'awa iyayenta waye ni , dama ace bata fad'a musu cewar tana sona bane , kai iyayenta ma bazasu bani ba, gara na sake nemeta na sadu daita so that daga nan Kawai na rabu daita na cigaba da neman mai irin taurarinta da wannan shawarar ya mike ya shiga bathroom ."
Tanweer a d'aki tana shawarar rabuwa da jaguwa tunda bai sonta haka zalika iyayenta ma basa sonta dashi ,sosai tayi zurfi cikin tunani , ringing din wayarta ne ya dawo daita haiyacinta ta duba wayar sunan doctor muyis ta gani yana yawo akan screen din wayar da Kamar bazata d'auka ba ,sai Kuma ta d'auka qirjinta na bugawa fat fat "hello !"
"Kina ne tanwer ?".
"Ina gida " ta bashi amsa tana yatsina fuskar "to sai ki shirya ki fito yanzu an Kawo wata mara lafiya imagency kuma Lallai sai kece zaki dubata.
"yanzu babu wanda zai dubata Sai ni ?"Gsky sai ke saboda aikinki ne iyayen yarinyar sunce kece kikayi mata aiki sakamakon rashin shan magani da allurai da yarinyar batayi ba ya jawo ciwon ya dawo sabo " shiru tayi tana tunani kafin daga baya tace "okay ka bani minti goma zaka ganni ta fito ta nufi d'akin dady
Tun da ta shigo d'akin gabanta Ke faduwa dan batasani ba ko zai amince mata ta fita , ita dai ko ya yarda Ko bai yarda ba sai ta fita tunda taimako zatai ."
ta karaso gaban mahaifinta ta durkusa a gabansa ya ganta amman yayi Kamar bai ganta ba ya kawar da fuskarsa gefe dan kunya take bashi da iliminta da komai Amman tana biyewa son zuciyarta Kamar mara ilimi . "dady! ta kirasa tana riko tafin hannunsa cikin nata , bai amsa mata ba ,sannan bai juyo ya kalleta ba "dan Allah dady kayi hakuri inshaallahu na canza bazan sake fita koina batare da izininku ba maganar Adnan kuwa ya zama tarihi a zuciyata har abada na hakura dashi ,
numfasawa yayi ya juyo ya tsura mata Ido yana son karantar gskyrta,
"ka yarda dani dady "bazan sake ba tunda bakwa so na hakura . "Kinyi alkwarin tanweer"?
",Wallahi dady nayi maka alkwari bazan sake ba .
"shikenan mamana Allah yasa , Allah Kuma ya yaye miki kiji gbdy , tace " ameen idan ba alkhairi bane arayuwata ," "yauwa dady daman ina son na fita ne zuwa hospital an Kawo wata mara lafiya da nayiwa aiki yanzu a halin daake ciki an dawo daita hospital ana bukatar taimakona dole kuma sai nice zan dubata"
" okay to shikenan Allah ya taimaka Allah ya bada sa'a ya d'auki mukulin motarsa range rover ya mika mata ki tafi daita "yauwa dady na gode ta amsa ta fita da sauri ta Shiga mota kai tsaye hospital ta nufa ta Isa office din doctor suka gaisa atare suka fito yana mata bayanin halin daake ciki har suka k'arasa dakin da matashiyar yarinyar take tana ganin fuskar yarinyar ta ganeta lallai itace tayi mata aiki a makoshinta daya samu matsala kwanaki baya tun kafin jaguwa ya dauketa .
ta k'arasa gadon da take kwance ta bud'e ciwon "subhallah ciwon yayi wost "garin yaya kuka barta agida har haka ta faru shin baku tsiyi maganin dana rubuta muku bane "?
"wallahi babu hali ne mu din bamasu karfi bane dan abinda muke dashi muka tattaro muka kawota akayi mata Aki inji cewar mahaifiyar yarinya.
umarni tanwer ta bayar a wuce daita d'akin tiyata dan ciwo ya dawo sabo dan wani tsoka ya fito mata a wuya yana zubar da ruwa da jini.