← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 120

Sashe 90

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

**************
Maheer ne da kansa ya nutsu a cikin daren ya kira Abraham ya sanar dashi abinda yake faruwa sbd suna buqatansa duk da Ammar yana nan amma sunsan damuwa da tashin hankali zai iya hanasa nutsuwar dubata yanda yakamata.

Basu sanar da Mimi ba a cikin daren Motar Dad tareda Saleem daya jasa tabar Zaadens zuwa limbas,

Motarsa na ficewa ta Maheer tabi bayansa tareda Daddy mahmoud
Sai ta Ammar a bayan tasu suka nufi Zaadens din gabaki dayansu damuwa a cikeda kirjinsu da fargaban idan ba ciwon dasuke fatan sun rabu dashi bane kwata kwata yake kokarin dawowa ace itama wannan zuciyar datake kirjinta tanada matsala ko me??

Koda suka iso limbas Securities sun san da zuwansu wanda Sayd ya sanar masu tareda umarnin daya san ko LIMBA bai fadaba shine abinda yake daidai a mansion din nasu.,

Dan haka motar Dzad na isowa da sauri Securities suka bude masa gate ya saleem ya sako kan motar ciki,

Motar Maheer ma sako kai tayi a ciki shima da gudu yana parking gefen motarsu Dzad.

Motar Ammar na sako kai chief Security na Securities din gidan ya taso yana bada umarnin a rufe gate din yana kallan Motar ya qaraso fuskansa ba rahama ko kadan Kaman zai dauki rai a gurin yake jinsa da hannu yayiwa Ammar din alaman ya sauke glass.

Wani kallan qyama da Mamaki Ammar din ke masa tareda tsanar duk wani abin dayake cikin limbas din da dukma wanda yake gidan tin daga kan Securities har asalin masu gidan tsana me girma yake jin yana musu sbd shi kadai yasan yanda yake jin zuciyarsa daya taho sbd Jannah amma badan hakan ba zai iya zabar zuwa ga azaba akan zuwa limbas dayake jin tsananin tsanarsa da zafinsa.

Aron da bai damu da komaiba sai umarnin da aka basa dan kuwa sedai ayi ruwan albarushi a guri idan har umarni suka sauko daga LIMBA to haka zaayi kuwa koda ana mutuwa a shirye suke da mutuwa da kashewa akansa dan haka ganin Ammar din yaqi sauke glass yana jiran su bude masa gate ya saka Aron din komawa gurin zamansa yana cewa Securities din

"Mamas boy da alama bai san yana bakin limbas bane,
Idan bai sauke glass nasa ba daga nan har saiya gaji ya koma inda ya fito kada matansa ta qara ko inci daya zuwa gaba,
Idan ya qaro gaba zuwa ciki just Shoot"

Ammar dayaji abinda daya fada Dago idanuwansa da sukai jajir yayi yana kallan gate din Limbas din zuciyarsa na tafasa da narkewa ahankali sbd tinda aka haifesa ya taso cikin gata da buga lokaci tareda juya abinda yakeson ya juya yanda ransa yakeso batareda shakka ko umarnin kowaba sbd suna juya duniyarsu ne da hannunsu yanda suke sonta sbd sune ZAADENS,
ZAADENS da kowa yake shakka da tsoro,

Ayau shine a gaban gidan wani ana rufe masa gate tareda bada umarnin a harbesa idan ya qara gaba,

Duk gwagwarmayar da yayi akan jannah da ciwonta yana tashi a banza ne ko me?
Ya sadaukar da lokacinsa da kuruciyansa gurin komawa baya a karatu,
Ya sadaukar da imaninsa ya koma makashin gaske,
Ya sadaukar da rayuwarsa ya ture lokacin komai na rayuwarsa ya bayar duka akan macen da zai iya bata rayuwarsa amma a lokaci daya wani yana tsayar masa da dukkanin iyakansa akanta ta hanya mafi ciwo.

Jajir idanuwansa sukai wani irin radadi me sanyi da ciwo na cike kirjinsa ya rintse idanuwansa hannuwansa dake riqe da steering suna dan rawa cikeda radadin dayake gauraye koina a jikinsa.

Securities kuwa gabaki dayansu tsaye suke da bindigoginsu sunfi su goma babu wanda baa shirye yake da harbi ba sbd yana motsawa ruwan bullet zasuyi masa su kuma ce Shine yayi intruding dan haka sun harbesa a matsayin suspect dayayo cikinsu da mota da niyar barazana ga rayuwarsu so a taiqace sun harbesa as self defence.

Su Dad kuwa Sayd ne dayake harabar gidan ya tarbesu a natse suka isa ciki.

Dayake dare ya danyi su mama gaba daya sun shige dan haka kai tsaye dakin Jannah din suka nufa tana sanye da kayan sanyin da AZIZ din ya dora mata akan kayan dayake jikinta tana kwance babu abinda yake motsawa ajikinta hatta bugu da fitar numfashinta kaman babu ko daya.

Dukkaninsu kallo daya sukai mata suka dago cikeda matsanancin tashin hankali da mummunan yanayi suka kalli AZIZ daya kallesu hankalinsa ba alaman ya damu da yanayinsu.

Dad ne ya tsaya akanta yana kallan yanda idanuwanta sukai zurfi hancinta ya qara tsayi dosai sbd muguwat ramar datai tayi pale sosai gabaki daya kammanninta sun sauya sbd ya dade bai gantaba....

Nauyi me tsanani ne ya danne zuciyarsa ya rintse idanuwansa yana sake budesu akanta cikin tsananin sanyi ya ce

"Meya sameta ta koma haka?
Ta dade ne batada lafiya?
Jannah ce ta koma hakan?
Meyake faruwa?

Maheer dauke idanuwansa daga kanta yana jin zuciyarsa na karyewa da tsananin tausayinta da jin ciwonta a cikin ransa..

Daddy mahmoud kuwa wayarsa ya fidda yana saka kiran Ammar daya kasa isowa haryanzu yazo ya duba musu ita kokuma su tafi da ita gida ayi mata komai acan sbd normally irin haka idan tai collapsing takan dauki kwanaki kafin ta farfado.

Ringing wayar Ammar keyi a gefensa yana kallo da jajayen idanuwansa dake cikeda radadi ya kasa dauka sbd zuciyarsa fashewa zatai idan ya bude baki yayi magana,
Barin gurin yakeson yi amma ya kasa koda motsa hannuwansa ne baya gani sosai sbd baqin ciki da ciwon daya danne masa kirji da zuciya.

Cigaba da sake kiransa Daddy mahmoud keyi amma wayar baa dagawa dan haka Maheer ya fidda tasa wayar shima yana saka kiransa amma abu daya ne baa daga wayar.

Saleem ne ya kalli Daddy mahmoud yace

"Daddy bara naje na dubosa tinda dai duka tare muka fito"

Juyawa yayi ya fice dakin yayi tsit babe me iya cewa komai Ammar suke jira kaman zuciyoyinsu zasu fada sbd qaguwan yaxo ya dubata dan ganin suke kaman bata numfashi kwata kwata gashi basada yadda ko imanin bawa wasu likitocin daman su dubata da asibiti kawai zasu wuce da ita batareda jiran komaiba.

Shi kansa AZIZ din ya kira nasa likitocin suna hanyar isowa shiru yayi yana jiran xuwan nasu yana kallan time akai akai cikin basarwa.

Sayd ne dayake bayansa ya dan dago kai ya kalla batareda yace komaiba.

Sayd din ficewa yayi yana fidda wayarsa ya sake saka kiran su dr Ashir a karo na ba adadin lattinsu.

Saleem a gate ya hangi motar Ammar dan haka ya qarasa da sauri yana kallan Motar da mamaki.

Bude masa kofa akai a mutunce da girmamawa ya fito yana kallan yanda securities din duka suke a shirye a position.

Motar ya nufa da sauri yana budewa yaga yanda jikin Ammar din ke rawa sosai idanuwansa sunyi jajir.

Saurin shiga motar yayi yana ambatar sunansa cikeda tashin hankali da fargaba.

Qara jijjiga jikin Ammar din yakeyi kirjinsa na kasa daukan ciwo da radadin da zuciyarsa ke masa take yanayinsa ya rikice a gurin kansa yafara juyawa yana wani irin rawa.

Saleem fitowa yayi da sauri ya zagayo ya tura Ammar din seat din gefe ya hau na driver bai tsaya komaiba yayi baya da motar yabar gurin dashi zuwa gida cikin tsananin damuwa da sabon tashin hankalin waye zai duba jannah datake tsananin buqatan taimako a yanzu.

Zaadens ya isa dashi wanda sai alokacin Mimi tasan abinda yake faruwa itada Anny dan haka dole Anny tafara basa taimakon gaggawa saleem na taimaka mata Mimi kuwa tashi hankalinta sosai sbd gabaki daya a yanzu cikakkiyar lafiya neman gagarar Ammar din takeyi wanda kuma hakan a cikin kwakwalwansa yakeyi dr ta fada a dena bari yana yawan shiga wannan halin akai akai sbd akwai matsala sosai da hakan.

Saleem ne ya buga waya ya sanar dasu Dad abinda ake take hankalinsu ya sake tashi da tsananin tinanin ina mafitar take sbd Ammar dinne kadai likitan da zai duba jannah gashi shikuma ciwonsa ya rasa lokacin tashi sai yanzu wanda suke mamakin menene ya samesa daya haddasa hakan.

A daidai wannan lokacin Su dr Ashir suka iso aka bude musu gate suka shigo tareda qarasowa ciki babu bata lokaci suka fara bata taimakon datake buqata shi da dr Sameera da nurse da suka taho da ita bayan kowa ya fice daga dakin.

Dayake wannan karan shine zuwansu na farko limbas dan haka palonsa na baqi aka isa dasu suka zauna Maheer na rasa zabin daya wuce yayi contacting Su Abraham sbd akwai yiyuwar dole sai sun taho din tinda Ammar da aka saka ran zaiyi handling situation din basai sun dawoba ya rikice shima dan haka bazai iyaba dole su qaraso su karba idan ba hakan ba babu bata lokaci wasu doctors din zasu san anmata dashen zuciya wanda zaa iya buqatan history na ciwonta abinda bazasu taba bari ko a tsautsayiba wani ya taba gani ba kenan.

Sai dare sosai aka samu bugun zuciyarta ya dawo daidai tareda numfashinta amma bata farfadoba har lokacin.

Nurse aka bar mata su dr Ashir din suka wuce suma su Dad sai alokacin suka tafi bayan Daddy mahmoud ya nuna sunason tafiya da jannah din acan Zaadens kafin ta warware sai a dawo da ita.
Chapter 90 · 0% Book details