Sashe 6
Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fita yayi ya sake siyo mata koko da saura Canjin daya rage ya kawo mata sedai koda ya dawo gabaki daya ta fice hayyacinta bama zata iya ko motsawa ba bare sanin meyake fada.
Ajiye robar hannunsa yayi yana kokarin dagota amma gaba daya jikinta ya sake.
Ambatar sunanta yafara yana shafa fuskanta zuwa wuyanta kuka na zuwar masa sosai.
Kuka me qarfin gaske babyn datake gefensu ta fasa wanda ya sakasa saurin juyowa yana rasa ya zaiyi.
Kuka sosai baby tafara wanda ya sakasa sakin umman ya zauna tsakiyarsu yana sunkuyar da kai shima ya fara kuka yana wani sheshekan da har jikinsa rawa yakeyi.
Ya jima a hakan batareda yasan me zaiyiba har babyn ta gaji tayi shiru ta koma bacci.
Ummansa kuwa wata firgita ta fara tana jijjiga.
Qanqameta yayi yana ambatar sunanta amma batasan ma yanayi ba.
Kusan awa daya a hakan kafin jikinta ya sake sakewa tayi baccin wahala.
Shima a gurin cikin jikinta baccin walaha da yunwa ya daukesa.
Sai azahar ya farka ya fita gidan ya nufi gurin aikin lakar dayake zuwa yana dan tayasu suna basa nera dari.
Acan yayi sallah yayita musu aiki har wanda yafi karfin shekarunsa.
Daga can wani kokon ya sake siyowa ya kawo yasha shida umman wadda sedai ya bata daga kwancen dan bata iya tashi hakama gabaki daya ta koma kamar ba umman tasa ba sbd wasu abubuwa takeyi da fizge fizge da zabura.
Yamma nayi yasan baba ila baya gida dan haka ya dauke babyn ya rufeta da zani kusan uku ya nufi gidan mama sakina da ita sbd tanada kuka.
Harya isa gidan babu wanda ya taresa ya tambayesa sbd gudunsu ma akeyi a kauyen sbd camfa ummansa da akai da baqar mace.
Mama sakin wuni tayi cikin damuwa da tinaninsu dan haka tana zaune tana hada saka da warwara tagansa ya shigo da zani
kallo daya tai masa ta gane jaririyarce ya dauko.
Cikeda mamaki da tsoro ta kallesa tana miqewa ta karbi 'yar tana cewa
"Abdul meyasa ka fito da ita??
Yaya ummanku?
Ya jikinta?
Kasancewarsa mara hayaniya da rashin sabo da magana sosai sbd baida abokan wasa ko wasu yan uwan daya taso cikin gata yasa ita kadaice ma wacce yake magana da ita sosaima
Ya dan dago kansa batareda ya kalleta ba yace
"Tanata kuka ne tin dasafe,
Umma kuma batada lafiya tanata firgita"
Kasa cewa sakina tayi ta nufi daki takai yar da sauri tana fitowa ruwan zafi tafara dorawa kafin ta dauko abincinta na rana da bata samu ci ba sbd damuwa ta miqa masa tace
"Maza zauna ka cinye yanzu"
Zaunawa yayi yaci abincin ita kuma tana sauke ruwan dauko babyn tayi tahau yi mata wanka sbd batason baba ila ya dawo ya taddasu hakama batason yayi dare a hanya da 'yar.
Wanka sosai me kyau tayi mata duk da bata taba haihuwaba batasan yaya akeyiba amma dayake anata haihuwa a gidan tana gani kuka tana dan saka hannu sai ta iya.
Tana gama mata wanka kayan data siya guda daya na jiran haihuwar matar Gali 'dan mijinta ta dauko ta sakawa yar ta dauko madarar shanun datake da ita me kyau ta bata kuma cikin ikon Allah yarinyar tasha take ta koma bacci abinta.
Sake nade masa ita tayi sosai ta basa tace maza ya koma.
Karbanta yayi ya juya ya fice daga gidan.
Koda ya isa gida ummansu ta tashi tana zaune ta zubawa kofa idanuwanta da sukai fari fes hakama bakinta ya bushe sosai.
Cikeda mamaki da dan farin cikin ganin ta tashi ya qaraso yana cewa
"Umma kin samu lafiya?
Juyo idanuwanta da suke kamar a buge tayi ta zuba masa batareda tace komaiba sbd kamar ba yayanta bane take gani.
Sake tambayarta yayi yaga ko kyaftawa idanuwanta basayi kallansu takeyi numfashinta baya fitama daidai.
Babyn ya bude daga zaninta ya dora mata a hannunta yana cewa
"Mama sakina tai mata wanka ta saka mata kaya"
Babyn ta saukar da idanuwanta ta zubawa ido tsawon mintina kafin ta dago ta zubawa Abdul din idanuwan shima
Shima ita yake kallan cikin tsoron irin kallan datake musun.
Sakin babyn tayi da sauri ya tare tareda daukanta ya ajiye gefensu yana cewa
"Umma kin gaji ne?
Har lokacin batace komaiba bata kuma dena kallansaba kaman wanda bata saniba ko bata taba ganiva.
Zamewa tayi ta koma ta kwanta tareda zubawa babyn gabanta ido.
Har dare yai suka kwanta batareda sun samu abinda zasu ci ba umman batai magana ba har lokacin hakama bata dena kallansu ba.
Cikin tsakar dare cikin bacci yaji motsin umman ya bude idanuwansa sai yaga ta tashi zata fita ko dan kwali babu a kanta hakama bata ko iya tsayuwa da kyau.
Kasa daukanta kafafunta sukai ta zube qasa kanta na buguwa da bangon kofar fita dakin take goshinta ya fashe da jini.
Tashi yayi da sauri yana riqota cikin tsoro da tashin hankali yana cewa
"Umma ina zaki?
Zaki bandaki ne?
Kallansa ta juyo tanayi kafin ta dago hannunta dayake wani irin rawa ta nuna masa kofa batareda tace komaiba.
Kofar ya kalla kafin ya kalleta sai ya rasa me zai fada ya kamo hannunta kawai ya dawo da ita kuma ta biyosa kamar yarinya qarama.
Kwantawa suka koma sukai take kuma saita koma baccinta.
Gari na wayewa yaje yayo aikinsa ya dawo mata da koko ya sake dafa mata ruwa ya sake ficewa.
Sai yamma ya dawo musu da tuwon dawa da miyar kuka dan kadan wanda aikin wahala yayi ya samosa.
Kasa cin abincin umman tayi duk yanda yayi sa ita dan haka kaman yanda yake bata koko haka ya zauna ya bata abincin a baki da kansa.
Babyn kuwa sake kaita yayi gurin mama sakina ta bata irin madaran jiya tasha ya dawo da ita gida.
Yana dawowa a hanya ya hadu da ummansa tana tafiya tana jiri ba dankwali akanta,
Da sauri ya kama hannunta suka juya gida yana mamakin abinda ya samu umman ga jikinta duk jini.
Suna komawa gida ya zaunar sa ita yana mata magana amma kwata kwata batacewa komai kallansa kawai takeyi.
Hawaye ya fara batareda yasan me zaiyiba.
Da daddaren ranar ma so biyu tana kokarin fita yana dawowa da ita tim anan ya fahimci ummansa ta kamu da wani sabon rashin lafiyar.
Kuka ya ringa yi har safe kuma da safen ma daqyar ya iya fita yabarta.
Koda ya dawo bata fita ba amma tana zaune babyn nata kuka sosai kamar bataji sai kallanta takeyi idanuwanta sunyi jajir kamar zasu fashe.
Daukan babyn yayi ya zauna gaban umman ya fada jikinta yana fasa kuka shima yana ambatar sunanta.
Kukansa ne ya saka wani irin hawaye masu tsananin zafi da ciwon da bata saniba tsinke mata tana qanqamesa tana jin tsananin sonsa shi kadai dan shi kadai take jin sonsa amma babyn kwata kwata kamar bata santaba dan kanta dake kokarin juyewa koma ya juyen.
Sun jima a hakan suna kuka duka su ukun harda babyn da suka matse a tsakiyarsu.
Sun jima a hakan kafin umman tayi bacci da babyn shi kuma ya fita sallan magrib yana dawowa a gida yayi ishai sukai baccinsu.
***kwanaki suka fara tafiyar musu ahankali ahankali ya fahimta da kyau kamar ummansa ta haukace sedai hauka bame tashin hankali ba wanda asalin yunwa da infection ne daya mummunan shigarta a gurin haihuwar me mugun karfi daya juyar mata da kai kwata kwata ta manta wai haihuwa tayi.
Mama sakina na cikin tsananin damuwa da tashin hankalin da suke ciki sbd yunwa da ciwo me karfin gaske na kokarin shigar babyn wadda tafara qanqamcewa ga Abdul din da shima wahala take neman kashesa da qananun shekaru.
Abdul kuwa da ummansa sun koma masu baran karfi da yaji sbd duk zai tafi gurin aikin wahalar dayake yi binsa takeyi bata zama fitowa takeyi dan haka tare suke zuwa ya zaunar da ita guri daya wasu su bata sadaka sbd tinanin almajirace wasu kuma gudunta ma sukeyi.
A cikin wannan halin sukai sati kusan uku sedai zuwa lokacin duk jamaar kauyen sun fahimci fatiman ta samu tabin kwakwalwa dan haka sadakar ma aka dena bata.
****FATIMA UMMITA shine sunan da Abdul ya sakawa qanwarsa dayake jinta kamar ransa dan kuwa shine me goyata da kansa duk yawon da zaiyi da ummansu yarinyar tana bayansa harya saba yanzu kauyukan gabansu suke zuwa tallan yalo dayake sara yana siyarwa.
UMMITA daga baya umman na bata nono dan haka tafara lafiya ta koma cikakkiyar lafiyayyar baby sedai har lokacin sitirar sakawanta daya ce tak wadda mama sakina ta saka mata,
Wanka kuwa sai suyi sati baayi mata ba sai daga baya yake kaita mama sakinata tayi mata harda hudan kunne tai mata ta saka ma yan kunne harda wasu kayan ta sake siya mata guda daya dan itama batada wani karfi.
##MAMUH
#LIMBAS
#ZAADENS
#BESTSTORY
#UMMITA LIMBA
#JANNAH ZADEEN
#DONOR
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070