← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 120

Sashe 30

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anny ma bata tsaya kallan nasu ba tabi bayan Ammar suka bar gurin zuwa wata kofar dake gurin.

Wata Nurse ce ta sake fitowa dauketa baby nade a cikin farin showel me tsananin taushi da tsadar dasuka taho dashi aka karba tin acan asibitin dr ken.

Tinkarosu Nurse din tayi da babyn wadda take lafe idanuwanta a rufe.

Dr Abraham da dr fin sai wani likitan daya fito baqi ne bahaushe musulmi ma yana zare hular kansa ya wuto gaba yana kallansu suma akansa suka maida kallansu suna kallansu da imaninsu sbd ganin shine nasu tinda su dr Abraham turawa ne bama gane musu zasuyiba.

Nurse ya kalla tana miqawa Sayyid din baby ya miqa hannuwansa cikin wani irin farin ciki dayake saka jikinsa rawa yana kokarin karba Muryan dr ismail wadda take tafe da bayayyanarda radadi da alhinin kai tsaye ta sauka a kunnuwansa....

"Anyi nasarar cire mata abinda yake cikinta cikin koshin lafiya sedai ALLAH YA KARBI RAN UWAR bawa baya wuce lokacinsa ayi haku........

Sakin jaririyar hannunsa Sayyid yayi cikin mummunan shock din dabai masan yayi hakanba.

Nurse dince tayi saurin zubewa qasa ta tare babyn a hannuwanta cikin ihu.

Wani mugun busashiyar yawu mama take kokarin hadiyewa amma ya kasa wucewa yankar mata maqoshi tanaji yanayi kaman da wuqa dan haka ta kyafta idanuwanta da suka qanqance tana kallansu daya dayan daya kafin ta tsayar da idanuwanta akan dr ismail din da qyar ta tina bakinta zata bude ba hannuwanta datake budewa ba muryanta na yankewa tace

"Kace an sauka lafiya ko?
Ita Ummitan fa?

Numfashi me zafin gaske ya sauke yana kallan Sayyid da yayi mutuwar tsaye yana wani vibrating amma tambayar maman ta sakasa dago jajayen idanuwansa da suke neman fashewa ya kallesa yana son jin amsar tamyar maman dan shima abinda yakeson tambaya amma ya manta yaya ake bude baki ayi magana gaba daya..

Sunkuyar da kai dr ismail din yayi yana kasa kallan idanuwansu da suka zuba masa ya bude baki yana tausasa harshensa yace

"Babu yanda zamu iya dukkaninmu akan hukuncin ubangiji,
Hakuri zamuyi dukkaninmu,
AN RIGA AN RASATA,TA RASU ABINDA TA HAIFA KAWAI AKA SAMU....."

Mama bakinsa take kalla kalaman na fitowa daga bakinsa kafin ta juya ta zubawa kofar dakin idanuwanta kafin ta sake wani yunqurin wani bugu kirjinta yayi so daya ta yanke jiki a gurin ta zube idanuwanta na juyewa gabaki daya.

Sayyid kuwa baya yayi kafafunsa na kasa daukansa ya durqushe a gurin yana fasa wani irin irin ihun daya saka gabaki daya rabin asibin daukan qarar kafin ya fasa wani irin kukan daya saka su dr Abraham yin baya cikin firgita sbd kukane daya zo masa kansa na zarewa gabaki daya yana wata irin jijjigar data saka dr Ismail kasa riqe abinda yakeji ya rungumesa yana jin idanuwansa shima cikowa da hawaye sbd radadin abinda sukai dayake ji a zuciyarsa wanda yayi a bisa rashin zabin dayake dashi.

Riqe sayyid din yayi a cikin jikinsa sbd irin jijjigar dayake zata iya sakasa samun collapse wanda zai iya qin tashi idan hakan ta samesa.

Jijjiga me karfin gaske yakeyi yana wani irin kuka me gunjin daya saka nurses dake kusa tahowa sun kallansa cikeda wani irin tausayi me cikeda tsoro sbd ganin namiji kamarsa yana irin wannan kukan me tada hankali.

Mama kuwa dr Ken ne yace nurses suyi saurin daukanta akaita emergency sbd ita kam kamar raima ya fita a jikinta.

Sayyid ma rikicewa yanayinsa yayi dole cikin tsananin gaggawa dr ismail yasa akai emergency dashi sbd wani irin kumfane ma yake fita bakinsa kaman yana kokarin samun wata matsalar ne suna buqatan gaggawar dawo dashi daidai.

Nurse Latifat aka bari da babynsu a hannunta tana yawo da ita sbd tashin hankali da firgicin ganin su dukan suna neman mutuwa a asibitin tasu.

Dr Abraham da dr finn kuwa Bayansu Dr Ammar suka bi sbd shiga tiyatar Jannah wadda Allah yayi sun samu abinda suke zo ba matsala fatarsu daya yanzu ana sakawa tayi saurin matching da vessels na jikinta batareda tasha wahalar kafin gama sabawa ko binding na komai daga zuciyar zuwa jikinta da jininta.

Duk yanda Su dr ismail da wasu likitocin suka shawo kan Sayyid kasawa sukai gashi sai muni jikinsa yakeyi dole sikai rendering nasa unconscious.

Mama kuwa kaman qaramar coma ta shiga sbd komai nata dena aiki yayi.

Tsit bangaren yayi babu mafitar komai har rana tai daga mama har sayyid babu wanda aka samu kansa bare asan yanda zaayi dasu ga baby ma tafara kuka sosai ga gawar Ummitah a ciki an rasa ya zaayi dasu.

A wannan halin ne Baba alhassan ya iso abuja sbd tin a jiyan Sayyid ya sanar dashi jikin Ummitan aiki zaa mata dan haka jinsu shiru ya iso.

Asibitin dr ken ya isa kai tsaye sbd acan ya taba zuwa dubo Ummitah wani zuwan da yayi kwanaki.

Acan ana kiran dr ken da kansa yaje ya dauko Baban ya kawo Asibitin nan sbd daman neman yan uwansu suke kai tsaye.

Ana kawo baba alhassan kallo daya yayiwa Sayyid yaji tasa zuciyar na neman bugawa sedai ya dauka zai iya riqewa da jarumta seda aka miqa masa baby aka sanar dashi Ummitah ta zama babu ya zube a gurin shima yana qanqame yar a jikinsa yana hada zufa me tsananin yawa da tashin hankalin dabai taba tsammanin samun kansa a ciki ba.

Dr ken da dr ismail ne sukaita kokarin basa hakuri da hanasa shiga wani mummunan halin kamansu Sayyid sbd kada arasa wanda zai karbesu.

Addua yayita yi yana hada zufa harya dawo hayyacinsa yana jan numfashi daqyar sbd take ciwon zuciya me qarfi ya kamasa amma ahakan ya daure yana danne azabar dayake ji a kirjinsa.

Mama da sayyid din kusan a lokaci daya suka farka,

Babu me karfin iya magana ko wani abu,

Idanuwa kadai suke bin baba alhassan dashi wanda yake kokarin hanasu ganin halinda yake ciki ya bude baki daqyar cikin karfin hali ya ringa musu nasiha da adduar data saka Sayyid zuba masa idanuwansa suna rinewa.

Mama kuwa haka suka lallaba bata iya tsayuwa da kanta baba alhassan ya saka hannu suka karbi gawarda basu saka a ido ba saida aka fito da ita a rufe aka saka musu a ambulance din asibitin dr ken wadda zata kaisu har garinsu a kyauta sbd tausayi da kuma yanda dr ken din ya nuna damuwarsa sosai akansu.

Sayyid na ido biyu da gawar Ummitah rasa kansa yayi ya dafe kirjinsa dake tsananin nauyi da azababben ciwo yana kasa tafiya da kansa saida aka taimaka masa ya shiga ambulance din tareda gawar Mama da baba alhassan da baby wadda Sayyid da mama basusan yama kamanninta yake ba suka shiga motar ABDULAZIZ da drivern daya bar musu.

Duk wasu takardu na tafiya da gawa an basu daga asibitin kai tsaye garin abuja suka bari ko gida basu biya ba zuwa garinsu da gawar dan acan zasuyi janazah.

Mummunan tafiya ce ta qunci da dacin zuciya me tsananin gaske na mummunan rashin da sukai wanda ABDULAZIZ ma kadai da mama ke tinawa takejin kirjinta na tsananta ciwon dayake tsananta mata radadin rashin.

Tinda suka hau hanya babu wanda ya bude bakinsa bare ya iya magana a cikin motarsu.

Acan motar gawar kuwa Sayyid qamewa idanuwansa sukai ya zubawa gawar ido kunnuwansa na daukewa daga jin komai hakama zuciyarsa gaba daya mutuwa yakejin kaman tanayi.

Gefen fuskanta dayake dan fitowa sbd iskan dayake kadawa kadan yana saka abinda aka rufeta ruf har fuska ya zubawa ido tayi wani irin haske fayau fatarta ta dan bushe kaman zata tashi tai masa magana kota ambaci sunan Hammanta.

Baisan lokacinda wani irin kuka mai tsananin gaske da radadin dayakejin bazai iya riqewa ba na tasowa daga kirjinsa ya dafe kirjinsa yana durqushewa gaban gawar yanayi hannuwansa dake dafe kirjinsa suna rawa yana dukan kijrinsa sbd azabar radadin dayakeji.
#MAMUH
#AZIZ AY LIMBA
#UMMITAH LIMBA
#FALAQ LIMBA

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
24
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

*************
Tafiya ce me dan tsayi wadda ta sakasu isowar yamma sosai da mummunan ganin daya daga hankalin dukkanin jamaar garin sbd farin jinin Ummitah da kaunar da kowa ke mata sbd yayanta wanda duk wanda rasuwarta ta shiga kunnuwansa ABDULAZIZ ake fara tambaya sbd firgici.
Chapter 30 · 0% Book details