← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 120

Sashe 73

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba, gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.

Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.

Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan 90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.

*********
Janyota kusa dashi sosai Maheer yayi yana kama hannunta daya ya riqe cikin kulawa da tsananin kaunarsa datake bayyane suka shiga palon..

Kanta a qasa yake amma a hankali ta dan rife idanuwanta sbd qamshinsa daya gauraya palon duk da akwai nasu Maheer da dad harma dana su Alh saad dika masu tsadar ne amma qamshin nasa ya fita daban tana jinsa a cikin numfashin datake shaqa yana isa zuciyarta yana karya dukkanin kuzarinta.

Kasa dagowa tayi sbd sanin tabbacin yana palon dan haka Mimi kawai taji tana buqata a wannan lokacin sbd ta rungumeta ta samu nutsuwa daga uwa da karfin gwiwa.

Bata qarasa isowa tsakiyar palonba Ammar daya farka cikin wani irin tsananin nauyi da ciwon kai yana saukowa daga gadonsa daqyar ya iya duba time baisan lokacinda jiri na dibansaba ya fito zuciyarsa na neman faso kirjinsa ta fito sbd tsananin harbawan datake ba daidaiba yana jin kaman zai rasa numfashinsa.

Dakin Mimi yai niyar nufa ya fasa ganin akwai baki a gidan dan haka kai tsaye ya nufi palon Dad yana isa Jannah da maheer na shigewa da sauri ya qaraso idanuwansa akan Jannah baya ganin komai da kowa sai ita.

Maheer ganin yanda Dad ke kallan bayansu ya sakasa juyawa a hankali cikin basarwa ya kalli bayan idanuwansa suka sauka akan Ammar dayake sako kai palon a mummunan yanayi.

Sayd dayake kusa da kofar shigowan Kallo daya yayiwa Ammar ya juya ahankali ya kalli uban gidansa wanda yake zaune a kujera hankalinsa kwance yana fidda wani irin kwarji kamewa daga jannah din data shigo har Ammar din dake shigowa ko inda suke bai kallaba duk da babu wanda baisan da zuwansa a gurinba cikinsu sbd ita yasan ta shigowanta a gurin,Ammar dinma kallo daya yayiwa Dzad da Maheer ya faminci Ammar suke kalla a kofa sbd yanda yanayinsu ya nuna.

Sayd akwai abinda ko AZIZ bai kallaba bare magana yana gane umarninsa ko abinda yake nufi kokuma abinda ya kamata yayi dan haka miqewa yayi.

Gadan gadan Ammar ya nufo Jannah wadda batasan dashiba tana kokarin bude baki ta gaidasu Baba Alhassan..

Kafafunsa da hannuwansa har wani rawa sukeyi ganin manyan rigunan shaddodi masu shegiyar tsada da huluna masu tsadar suma suna daukan ido a jikin kowa
Jin yayi ma suna kashe masa ido sbd masifar dayakeji tana kunnuwa a kirjinsa da cikin kansa
Jannah din yake kokarin kamowa jikinsa tukuna yayi magana sbd yafisan duk abinda zai fada ko tambaya ya zama tana hannunsa already sbd kada a a rabasa da ita dan ayau yakeson a daura musu auren kaman yanda aka tsara ba dagawa,
Ayau yakeson mallakarta,.ayau yakeson maidata cikakkiyar macensa ta yanda babu iya rasashi da ita ko a magana bare a wani aikin.

Yanda ya tinkarota kai tsayen zai kamota Sayd yasha gabansa ahankali cikin nutsuwa tareda kallansa da idanuwansa da suke nuna zai iya rabasa da hannuwansa har lahira idan suka sauka akan jannah din.

Su baba Alhassan kallan kofar da Ammar din ya shigo sukai cikin mamaki

Dad Maheer ya kalla cikin mamaki da tashin hankali alamar yayi handling din Ammar din yayi masa batareda baqin sun gane ba.

Ammar cikin tsananin zafin gaske da yawon dayaji kaman tsintsaye nai masa cikin kai ya kalli Sayd zai ciresa daga gabansa ya wuce yace

"Kasan me kakeyi?

A lokacin Jannah ta juyo da sauri jin Ammar tana ganinsa cikeda mamaki take kallan yanayinsa ta daga kafa zata nufess Sayd ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa da bata girmamawa da hannu ya nuna mata hanya yana matsawa gefe da nutsatsiyar sauti yace

"Pls Mrs LIMBA"

Hanya da inda yake nunawan cikeda girmamawa ta kalla da sauri hannuwanta na dan rawa cikeda mamaki da tsoro sai alokacin ta iya daga ido ta kallesa yana zaune dukansu basu ishesa kallo ba wayarsa ya dauka wadda Falaq ta kirasa cikeda kwanciyar hankali da nutsuwa ya dauka ya dora a kunnesa yana bude bakinsa yace

"Yes Falaq Aziz"

Abinda Falaq din ta fada kai tsaye a cikin wayar da wani irin farin ciki ya saka sai alokacin ya saukar da fararen idanuwansa akanta itama shi din take kalla tana neman zarewa ga Sayd bakin rai ya hanata wucewa zuwa ga Ammar wanda ya fara wani vibration yana.

Maheer ne yayi saurin isa ga Ammar din ya jasa da karfi cikin kyaftawar ido suka fice Ammar din na kwacewa yana son magana Ammar harshensa jin yake kaman ya karye sbd Bugawan da zuciyarsa ke kokarin yi.

Sayd cikin fuskewa ya rufe kofan palon yaja ya tsaya koda Ammar din zai dawo dan da alama yana kokarin zarewa ne dan haka yana taba abinda ba nasa ba zarar dashi zaiyi a cikin gidansu ya tafi yabar musu sabon nakasashen Ammar.

Tsit palon yayi kowa ya kasa cewa komai sbd yanayin da aka samu din saida Daddy Mahmoud ya fuske ya kalli jannah cikeda kulawa yace

"Jannah ki gaida iyayen LIMBA gasunan"

Bakinta rawa yakeyi sosai ta budesa batareda ta iya kallansu ta gaidasu tinaninta duk a rikice ta dena gane komai so kawai take ta fita taje gurin Ammar.

Amsawa su Baba Alhassan sukai cikeda kulawa suna mata Addua da saka albarka.

AZIZ takeson gaidawa shima amma ta kasa sake kallansa dan haka jiki a sanyaye ta juya tabar palon Dad dinta yabita da kallo cikeda tsananin kauna da kulawa.

Maheer kuwa koda ya fita da Ammar din daman Anny taga wucewansa da sauri tayo palon saiga Maheer ya taho dashi dan haka batai wata wata ba ta sake sakasa baccin da zai iya masa illa amma bata damuba.

Kallanta Maheer yayi zaiyi magana sbd bayason wani abin ya samu Ammar ta dakatar dashi da cewa

"Babu abinda zai samesa for his own good nake masa komai sbd kansa bazai iya daukan wannan tashin hankalin dayake saka kansa a ciki ba so yana buqatan hakan dan ya karba lamarin a hankali"

Ajiyan zuciya ya sake yana mata kallan kin tabbata
Gyada kai tayi tana kama hannunsa suka fice bayan ya gyarawa Ammar din kwanciya da rufa.

Suna fitowa dakin Jannah na isowa da sauri tana cewa

"Ina Ammar din,
Meya samesa?
Yaya na gansa haka?
Meyake faruwa ne??

Kokarin fadawa dakin take Anny ta riqota tana cewa

"Auren AZIZ LIMBA dayake kanki ne yake faruwa,
Ki kula sbd yanzu ke din matan wani ce wanin ma AZIZ LIMBA ake magana"

Dakatawa jannah tayi tareda juyowa gaba daya tana kallan bakin Anny kafin ta dawo da kallanta kan Maheer tace

"Meyake faruwa?
Ance an daura auren to waye aka daura dashi ni banganeba,
My Ammar kokuwa wani daban??

Riqota Maheer yayi tareda kokarin kwantar mata hankalin dayaga yana neman tashi sbd tsoro da firgici yace

"Kwantar da hankalinki my love kinji,
Da AZIZ LIMBA aka daura miki aure sbd samarwa da zuciyanki abinda takeso,
Bazamu taba iya hanaki abinda zuciyarki takeso ba koma meye"

Rawa hannuwanta suka fara a rikice tace

"No,no no
Ammar nakeson aura,
Ammar nakeson aura basai abinda zuciyana ke so ba,
LIMBA bai taba sona ba Ammar ne yake sona,
Meyasa zaku rabani da Ammar?
Ammar can't take ita zai zare,zai haukace zai iya zama komai akan hakan zai iya komai akan hakan..........

Anny ce ta katseta cikesa takaicin zantukan tace

"Kinsan shi LIMBAn waye akan haukar da zarewan?
Idan hauka Ammar zaiyi to ni banga alamar akwai rashin haukan a tattare da LIMBA dinnanba ki dena ganinsa kaman baya ji ko gani,
Kima aje LIMBAn kinga Sayd?
Kinsan komai zai iya akan LIMBA?
Kina ga bazai iya daukan ran Ammar dinba akan LIMBA"

Wani kallo Maheer yayiwa Anny din yana cewa

"Ke me kike fada?
Stop scaring her,
Kina daga mata hankali cant you see tana cikin damuwa da firgici"

Janyo jannah din yake kokarin yi tan kwacewa tana son shiga dakin Ammar wanda a daidai lokacin Mimi data taso ta iso gurin jikinta va wani karfi.

Da gudu Jannah tayi gurin Mimin ta rungumeta tana fasa wani kuka me sanyi tana cewa

"Mimi Ammar bazai iya daukan wannan hukuncin ba,
Inason a warware auren dan Allah a dauramun da Ammar"

Mimi wasu hawaye ne masu radadi suka gangaro mata dan daman koda ta fito ta fahimci tabbas andaura auren yau Amma bata dauka zasu iya daurawa wani auren jannah ba Ammar ba.

Rungume jannah din tayi batareda ta iya cewa komaiba sbd ciwon datake ji yana cike zuciyarta da bacin rai me tsananin gaske.

Dakin Ammar Mimin ta ja jannah zuka shige batareda tacewa Anny da maheer komaiba suka rufo kofa.

Kallo daya Mimi taiwa Ammar zuciyarta ta karye ta share hawayenta tana zaunawa gefensa.

Jannah ma gefensa ta zauna tana ambatar sunansa Mimi ta hanata tabasa da hannuwanta.
Chapter 73 · 0% Book details