← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 120

Sashe 117

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motar na ficewa daga harabar kotun idanuwanta suka rufe ahankali ta some a jikin Ummah dukkaninsu jikinta na sakewa.

Taimakawa Ummah akai aka fitar dasu kotun zuwa waje acan Ummah sbd kan ba daidaiba ta zauna tareda dora kan jannah din a kafafunta tana rarrashinta a tinaninta bacci takeyi.

Har yamma suna gurin tukuna jannah ta farfado ko gani batayi sosai ta miqe daga jikin Umman tana jin zuciyarta na qafewa.

Dafawa tai ta tashi tareda miqawa Ummah hannu ta bude baki Ahankali tace

"Ummah muje"

Kama hannunta Umman tayi da sauri ta miqe suka farawa takawa suka bar gurin.
#MAMUH
#NEW LIFE
#BESTlove
#MothersLove
#JANNAH ZAD
#FATIMA UMMA ZAD
#The ZAADENS
#The LIMBAS
#BESTSTORY
#HOTLOVE
#HOTROMANCE
#CRAZY LOVE
#BESTLOVERS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
96
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

*********
Tafiya sukai me dan tsayi kafin jannah ta tsayar musu da mota suka hau batareda ta iya cewa komaiba sbd jikinta gabaki daya dayake a mace zuciyarta na bushewa da baqin ciki da damuwa.

Ummah data ga yanayin jannah din hannunta ta saka a cikin nata ta kama tana hadewa da nata cikeda kauna me tsafta da karfi tana jin kamar ta yaye duka kuka da damuwar dake damun jannah din ta dawo dashi kanta.

A hanya aka ajiyesu suka qaraso da kafa sbd kwata kwata baa barin motocin haya na shiga anguwar,
Suna isowa gida silalewa jannah tai ta zauna tareda rufe idanuwanta tana rafka wani irin tagumi da nisa a tinani.

Ummah zama tai gefenta tareda tagumin tana zubawa jannah idanuwanta shiru.

Lokaci mai tsayi suka dauka a hakan kafin jannah ta iya sauke ajiyar zuciya tareda miqewa tsaye ta nufi toilet tayo Alwala tazo suka tada sallah.

Suna zaune a gurin akai ishai suka miqe sukai,

Kwata kwata batajin yunwa damuwa da qunci sun cike mata cikin amma tasan umman na buqatan abinci dan haka miqewa tai jiki ba karfi suka fito tareda umman hannun Ummah na cikin nata suka fara tafiya tinaninta yayi nisa jefa kafarta kawai takeyi har suka isa gurin madam dinsu jannah ta karba abincin da suke karba suka zauna anan can bayan kitchen Umman taci ta koshi ta sakata cin dole itama suna gamawa suka fito suka koma gida.

Suna dawowa gida Umma ta kwantar da jannah kan kafafunta tana mata fita tana cewa tayi bacci.

Rufe idanuwanta tayi ahankali tana jin nutsuwa da sassaucin komai na ratsata,
Kasancewan Ummah a rayuwarta ta sani rahama ce me girman gaske wadda take sake jinta har cikin ranta,

A yanxu Ummah danginta,uwa kuma ubanta hakama abokiyar rayuwa.

Cikin Amincin Allah bacci me nutsuwa ya dauke a hakan wanda bata taba tinanin samun bacci ba a yau din.

Kwana Ummah tayi har asuba tana gadi da kulawa da jannah din wadda ta tashi cikeda wani irin tawakkali da karfin zuciyar rungumar kowace irin kaddara da Allah zai jarabceta dashi,

Allah ya bawa Ahalinta damar sake wata rayuwar idan sunyi juriya da hakurin shekara guda dan haka zata jure zata karba zata jira lokacin kuma tanawa Allah godiyar wannan damar daya basu.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali a lokacinda ta kalli time a jikin wayar taga karfe goma na safe kuma lokacinda kotu ta basu ta barin gidan karfe goma sha daya ne dan haka ta kalli yan kayan datake dasu har ita har Ummah iyakacinsu jaka daya.

Juyawa tayi ahankali ta kalli jakarta dake rataye jikin bango wadda ta dauki lokaci bata ko kalla inda take ba sbd abinda yake cikinta abu ne da har abada bazata iya budewa ta kalla ba.

Hannu ta miqa ahankali ta ciro jakar tareda saka hannunta ciki ta ciro takardar da Saleem yabar mata sbd tinanin zata iya buqatan hakan.

Akan envelope din dayake ciki hannunta ya fara sauka wanda ya sakata rintse idanuwanta ahankali tana jin kamar wuta ce hannunta ya sauka akai.

Janye hannunta tayi ahankali tareda lalubo takardar Saleem wadda take dauke da Sunan garin da batama san yaya zatai pronouncing nasa ba amma kuma rayuwa ayanxu can zata kaita a cikin mutanen da batasan yaya zasu karbeta,
Bata sansuba basu santa ba rana tsaka zataje garesu tace itace jikar yar uwarsu data shafe shekaru da rasuwa kuma yayanta vasu nema danginta ba sai yanxu.

Numfashi ta sauke idanuwanta na jajir amma koma me zata tarar a kauyen ta shirya zata dauka zata daure zata zauna ta jira fitowan iyayenta su taru su koma kauyen sbd acan Allah kuma yanzu ya zabar musu rayuwa.

Tattara musu kayansu tayi a jaka ta rufe ta sake duba dukkanin tamardun ahalinta na karatu da id cards nasu da sauran duka takardunsu masu mahimmanci suna hannunta dan haka ta sake sakasu qasan jakarta kafin ta miqe tsaye tareda miqawa Ummah hannu wadda ta kama da sauri tana miqewa.

Numfashi me dumi jannah ta sake saukewa tana jin kirjinta na mata wani irin nauyi rauninta na neman bayyana sbd rayuwa taza mata matakin karshe na fadawa wata rayuwar wadda batasan wane qalubale kuma zata tarar ba.

Bude kofar dakin tai ahankali tareda juyowa ta kalli Ummah da idanuwanta da sukai jajir wani irin radadi mara faduwa ne yake cinta da zuciyarta ta bude baki Ahankali cikin tsananin sanyi tace

"Ummah zaki bini??

Da sauri Ummah ta gyada kai tana sake qanqame hannunta cikeda kauna datake ji har ranta tace

"Duk inda zaki tafi bazan taba barinki ba har abada,
Bazan qara rabuwa dake ba,
Muna tare ba rabuwa UMMIJAN"

Wani numfashin ta sake saukewa tareda ficewa daga dakin Ummah na sake murmushi a fuskanta na kasancewanta da Umminta.

Suna fitowa daidai gate din gidan motocin kotu da lawyers suna isowa tareda yan media anan aka karbi dukkanin takardun komai dayake rubuce aka tabbatarda duk abinda yake rubuce na kadararsu ansamu takardar mallakarsa a cikin takardun data bayar akai komai ta saka hannu da hannunta dake rawa a qasan signature dinsu Dad dayake jere a takardun wanda saida aka kai musu gidan yari suka saka hannun sun bada komai tas tukuna.

Juyawa tayi tabar gurin batareda ta iya juyowaba tanaji anata daukan hoton da yar hayaniya amma bata dakata ba bare juyowa sukai tafiyarsu itada Ummah.

Tafiya sukai kafin suka isa gurin madam wadda tasan da komai kuma ta amince ta sakasu a cikin ma'aikatanta masu kwana kafin su samu abin tafiya dashi.

Daki ne me dan girma wanda yake store ne na ajiyar abinci anan masu aikinta biyu rak data yadda dasu suke kwana sai kuma su jannah din yanxu.

Bata bari ciwon dayake ranta ya takureta ba aikinta data saba ta kama jiki a mace tana kokarin hana kanta mara godiar Allah daga sassaucin da suka samu na hakan.

Wuni tayi aiki har saida aka rufe restaurant din da dare tukuna ta samu ta watsa ruwa taxo tayi sallan ishai ta kwanta a gurin wahalallen bacci mai hade da zazzabi yana dauketa.

Ummah ce ta dawo kusa da ita ta rufe mata jikinta ahankali tana daukan abin fifita tana kore mata sauro da kuma dan zafin dake akwai cikeda kulawa tana dan danna mata kafafunta da hannuwanta data san sun gaji matiqa.

Washe gari da karfin jikinta ta tashi tana rage damuwa a ranta ta zauna tana taya Ummah gyara farcenta kafin ta gama ta kalli Umman tace

"Ummah kiyi baccinki idan zanje nayi aikina idan na gama saina hada miki ruwan wanka kada ki fito kiyi zamanki tinda kinga madam tace batason wanda ba ma'aikacinta ba na fitowa gurin ayyukan,
Kinji Ummah?

Gyada kai Umman tayi tana cewa

"Idan kin gaji ki aje ki dawo ki hutawanki kinji"

Wani murmushi da iyakacinsa bakinta ne ya kubce mata daya saka ramammiyar fuskanta kyau tace

"Ummah zan huta amma ba yanzu ba insha Allah"

Itama umman murmushi tai mata tana kallanta harta fice.

Madam din data iso tafara zuwa ta gaida cikeda girmamawa kafin ta wuce gurin aikinta wanda tafara da wani uban tarin yankan cabbages da vegetables tukuna ta koma fere Dankali wanda kusan buhu guda ne aka zazzage.

Saida tai kusan rabi tukuna aka basu abincin breakfast ta karba ta koma dakin da suke takaiwa Ummah suka zauna sukaci suna gamawa Ummah taqi xama ta biyota ta zauna gefenta tana kallan yanda take fama da aikin fere dankalin dan haka itama ta karba ta fara tayata daman ta iya tinda tayi aiki a gidajen abinci itama.

Kaman wasa sai gashi Ummah ta ringa tayata aikin da har yanzu bata wani qwareba sbd bata saba ba.

Sai yamma sosai suka samu saukin aikin suka koma aikin wanke wanke.

Ana magrib suka samu kammala komai suka tafi wanka tafara kaiwa umman ruwa toilet tayi kafin itama tayi,

Sallah sukai suna gamawa dukkaninsu a gurin bacci ya daukesu kamar matacci na wahala.

Sai dare sosai Ummah ta farka ta rufe jannah din tana mata aikin korar sauro da fita tanaji tana gyangyadi ahaka dai suka ga asuba.

Washe gari ma haka suka wuni a aikin wahalar baji ba gani ba hutu sai dare suka samu hutu,

A hankali suka fara shude kwanaki a cikin gurin wanda babu komai sai aikin bauta da wahala,
Tinda suka shiga basu taba fitowa ba sbd babu inda zasu idanma sun fito din,

Ahankali Ummah ta shiga cikin aikin sosai sbd bata iya kallan jannah cikin wahalar datai mata yawa ita kadai,

Da farko Jannah bata bari sai daga baya ganin Umman bata iya bari hakama ta fita iya komai sai ya zamana tare suke komai,

Ita kanta madam din dataga Ummah na aiki sosai saita dan qara musu kadan akan abinda take bawa jannah duk da ba yawa.
Chapter 117 · 0% Book details