← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 120

Sashe 104

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mimi,Saleem da maheer da tsananin tashin hankalin dayafi wanda suke ciki sukai kansa suna kokarin kwace Falaq wadda bakinta ke jini sosai tana kokarin riqe numfashinta dake kokarin saka zuciyarta dena bugawa sbd bugun zuciyar ya sauya sosai zuwa yanda baa so gashi sosai aka tabbatarwa limbas takai matikin da baaso ta sake samun matsala.

Jannah zubewa qasa tai tana fasa wani irin kuka me tsananin ciwo da qunci kamar zuciyarta zata fashe.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
85
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

***************
Ahankali Dad idanuwansa suka bude sika sauka akan ahalinsa da suke cikin mummunan yanayi anata kokarin cire falaq a hannun Ammar wanda ya qarasa haukacewa gabaki daya ya koma asalin cikakken mahaukaci,

Kuka sosai Mimi takeyi tana jansa a jikinta amma sam yaqi banbaruwa,

Jannah datake kuka mai tsananin gaske jin take inama ta bude ido taga duka wannan rayuwar da sukai tin farkon dawowansu Nigeria mafarki ce,

Inama ta koma lokacinda take cikin ciwonta tayi jinyarta cikin Aminci ta tafi ta huta,

Maheer cikin tsananin zafi da tashin hankali ya sakarwa Ammar din wani mummunan marin daya sakasa faduwa shi da Mimi datake rugume dashi ta baya.

Saleem ne cikin tsananin sauri ya tare falaq ta zata zube qasa babu numfashi a jikinta ko kadan.

Da sauri jikinsa na tsananin rawa ya fito da ita zai nufi emergency da ita latif dayake mota idanuwansa suka sauka akansu da tsananin firgici ya futo ya nufosu yana cewa

"Meya sameta????

Akan jinin dayake fuskanta da kayan jikinta idanuwansa suka sauka wata mugun firgici ya shigesa baisan lokacinda ya kwatota daga hannun saleem dinba yana nufar mota da ita cikin tashin hankali da tsoro me tsananin gaske.

A rikice ya figi motar ya nufi gida kaman zai tashi sama sbd yasan ganganci ne zaiwa AZIZ LIMBA barin a duba falaq din asibitin zaadens.

Koda ya iso gidan cikin matsanancin tashin hankali yayi ciki ya kira mama da Fiddausi cikin tashin hankali suka fito..

Fiddausi kallo daya taiwa Falaq take jikinta ya dauki rawa tayi kanta tana tallafo ta,

Mama kuwa a rikice ta kallesa tace

"Accident kukai?
Meya sameta?
Innalillahi wainna ilayhi rajiun,
Ku kuramun AZIZ da sauri a waya kar naga baqar rana yau"

Kokarin fiddo da falaq din mota ake aka wangale gate
Dukkaninsu mayar da kallansu kan gate din sukai ganin motar AZIZ ce gaban Latif yayi mummunan faduwa.

Sayd parking yayi yana kallan su maman.

Shi kansa AZIZ ganinsu harabar gidan duka ya sakasa fitowa yana kallansu kafin kowa ya motsawa idaniwansa suka sauka akan Falaq da Fiddausi da fadilah suka fitar kamar wadda tai hadarin mota.

Miqawa Sayd wayoyin hannunsa yayi yana isa gurin kai tsaye ya karbeta gabaki dayanta yana cewa

"Meya sameta???? Cikin wani irin mummunan yanayin daya sake saka jikin kowa sanyi.

Mama a rude tabi bayansa tana cewa

"Accident sukai"

Sayd kuwa wayarsa y fidda cikin tsananin sauri ya kira likitoci yanace maza maza ana buqatansu.

Dukkaninsu ciki suka dungumo hankali tashe.

Babu bata lokaci su dr Ashir suka iso tareda nurses da komai na buqatan taimakon gaggawa..

A wannan lokacin ne Latif ya tako ahankali cikin damuwa me tsanani ya sanar dashi ba ba Accident bane daga dakin zaadens kome ya faru.

Rintse idanuwansa da sukai jajir yayi Ahankali wani irin abu na gangarawa kirjinsa ya danne masa.

Abu dayane yazo kansa Ammar ne ya taba masa 'ya....

Sabuwar tsanar zadeens din yaji tana gaurayesa wadda take kewaya dukkanin jinin dayake yawo jikinsa,

Duk taimakon dasu dr Ashir zasu bata sun bata sedai bugun zuciyarta be dawo yanda akesoba da alama ta riga ta shiga stage din da baa so,

A yanzu akwai hope qalilan idan har bazata sake bugawan zuciya ba sbd tana sake samun attack shikenan komai ya lalace kodai a mata dashen zuciya kokuma ayi hakuri a jira lokacinta kawai.

Wannan zancen da dr Ashir ya koro masa bayan sun mata wasu irin gwaje gwaje har kusan asuba shine ya tarwatsa dukkanin kuzari da zuciyar wanda yake limbas sbd maganace da akai gaban kowa.

AZIZ din kasa riqe kansa yayi ya zube qasa a gaban likitan yana cusa kansa cikin qafafunsa idaniwansa n wani irin radadin daya saka mama fasa kuka mai tsima zuciya sbd bata taba tinanin zasu iya rasa jinin da Ummitah tabar musu a duniya ba,

Rasa falaq shine rasa jinin Fatimanta a duniya kwata kwata sbd AZIZ bazai taba rayuwa ba idan ya rasa Falaq wadda itace abinda ta rikesa da yanzu ya dade da mutuwa a nakasashe mara hankali.

Sayd kuwa gurin mahaifinsa ya tafi ahankali ya silale gabansa ya zauna ahankali baisan lokacinda wani irin kuka me sanyi yazo masa ba,

Kaunar yarsa a jininsa yake wadda rasata rasa AZIZ ne wanda yakewa kallan jininsa da shima zai iya shiga mummunan hali idan ya rasa.

Fiddausi ma kuka takeyi sosai sbd tamkar yar data haifa takejin Falaq kaunace a tsakaninsu me girma da tsafta,

Dik karfin halin fadilah ma sanyi jikinta yayi cikeda tausayin ahalin gidan da falaq din kanta data koma abin tausayi lokaci daya tayi fayau da haske sosai sbd matsalar zuciyar a take take janye albarka jikinta..

Tsit gidan yayi kaman gidan mutuwa sbd kowa na cikin tsananin dacin zuciya da qunci,

Ko securities da masu aiki gabaki daya kowa jikinsa a sanyaye yake.

Daman kwana zaune akai gidan likitoci na kan Falaq din.

***acan asibiti suma kwanan zaune sukai sbd Ammar daya rikice hakama Dad ba sauki ko kadan ga Mimi zuciyarta ta fara kasa dauka,

Maheer na ya zaunar da ita ya sanar da ita qasar zasu bari gabaki dayansu.

Shiru tayi zuciyarta na wani irin sanyi da ciwo duk a lokaci daya wanda a wannan karan batajin soyayya zata hanata bude idaniwanta ta tsaya tareda familynta da sukai sacrificing komai akanta,

Numfashi me zafi ta sauke ahankali tana hadiye wani irin daci da ciwo ta kalli Maheer tace

"Na Amince zan biku mu tafi bazan sake waiwayan baya ba"

Dad ne ya sauke numfashi ahankali cikin ciwo na jin dadin abinda ta fada,

Maheer ma numfashin ya sauke yana jin samun sanyi da saukin nauyin kirjinsa.

Hudu na yamma likitoci da nurses din mahaukatan daya gayyato daga lagos jirginsu ya sauka daga airport kai tsaye motocin asibitin Mahaukatan nan abuja ce tazo ta daukesu tareda motar jamian Drugs da babu me alamar yasan imani a acikinsu suka isa asibitin Zaadens.

Suna isa dakin da Ammar yake kwance an dauresa a gado abi na farko wani mahaukacin mari Wani Dan drug ya fara kashesa dashi wanda ya saka haukarsa daukewa ta wucen gadi.

Motocin police ne kusan guda biyar suka iso asibitin take guri ya cika aka hargitse.

Wani mummunan daurin azaba akaiwa Ammar kamar goro yana ihun tsananin azabar da bai taba ji ba aka fito dashi tareda takardar asibitin mahaukata zaa kaisa ta lagos.

Duk tsananin ciwon dad saida ya tashi daqyar suka fito dukkanin familyn suna roko da neman taimako cikin mummunan tashin hankali da fita hayyaci.

Maheer ayau kuka yakeyi kaman mace a gaban tarin mutane amma wani ball da akai dashi saida ya fasa goshi.

Dad ma kuka yakeyi sosai kirjinsa na tsananta ciwo.

Mimi kuwa yanke jiki tai ta fadi saleem yayi kanta.

Jannah kan maheer tayi tana goge masa goshinsa daya fashe da hannun rigarta idanuwanta jajir.

A dakin da dad yake aka kwantar Mimi dan haka dukkaninsu sunyi shiri zuciyoyinsa na ciwo da tarin baqin cikin daya rufesu,

A rayuwarta soyayyar AZIZ LIMBA itace mummunan kaddarar data afkowa rayuwarta harta tarwatsa mata family ayau sike cikin mummunan halin dasuke buqatan dauki.

Tayi danasani da baqin Kamuwa da soyayyar wanda bai taba sonta ba qarshen iyayenta kawai yakeso batareda laifin komaiba,

A yau tayiwa kanta alkawarin ta hakura da rabuwa da aurensa,
Idan ita yar halak ce zata cire soyayyarsa har abada bata buqatansa...

Miqewa tayi ahankali ta fice daga dakin taba jan kafafunta daqyar.

Gate ta nufa idanuwanta jajir ko gani sosai batayi ta tari mota ta shiga ahankali tana rufe idanuwanta bayan ta sanar dashi idan zai kaita.

Ahankali ta miqa hannunta ta dora akan zuciyarta dake bugawa da tsananin ciwo da quncin datake jin yana sake ciketa tako ina.

ko data iso gidan security da sauri suka bude mata gate ta shigo tana tafiya cikin quncin daya rufe idanuwanta.

Ciki ta shigo babu kowa a main palo sai Fiddausi data ganta ta qaraso cikin tsananin sanyi tana mata sannu da zuwa amma sam Jannah batajinta sbd nisan datai a cikik matsanancin qunci da tinani me ciwo.

Kai tsaye dakin Falaq ta isa ta taddata kwance kamar wadda tai shekaru a kwance.
Chapter 104 · 0% Book details