← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 120

Sashe 84

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No kema kinyi girman daya kamata ki dena shiga kwata kwata idan ba shine ya kira ba,
Ba daddynki kadai ba bedroom din kowane namiji a duniya karki sake shiga saina mijinki kadai idan anmiki aure,
Baa shiga Addininmu ya hana hakan kwata kwata baayi ki kiyaye sosai karki sake saina mijinki,kinji???

Shiru falaq tai tana nazarin zancenta sbd Daddynta daman yana fada mata kowane namiji a duniya karta yadda ko hannunta ya kama koda da sunan gaisuwa,
Yasha fada mata hakan tin tana yarinya sosai haryanxu bai dena fada mata shiyasa iya shi kadaine take iya hada jikinta da nasa sbd shi mahaifinta ne batama iya zama idan baa kusa dashiba ta maqalqalesa indai yana kusa.

Kallan jannah tai cikin dan tinanin daya rikitar mata da tinani tace

"Kikace harda dakin Daddyna na dena shiga sai nayi aure?
To idan nayi aure saina ringa shiga dakin Daddyn kome??

Shafa fuskanta tayi tace

"No idan kinyi aure dakin mijinki kawai zaki ringa shiga banda na daddynki,
Kwata kwata dakin kowane namijin daga yanxu kin dena shiga saina mijinki har tsufa,
Idan kika shiga dakin wani zai iya cutatar dake kaman irin yanda kika ringa jin tsoro a school lokacin"

Kallanta falaq tai da sauri tana fahimtar abinda take nufi dan haka ta sauke ajiyan zuciya tana gane abinda yasaka kenan Daddynta yana rufe bedroom dinsa wasu lokutan da safe saitayita bugawa yazo ya bude mata.

Kallan jannah ta sakeyi tace

"To ke zaki iya shiga kenan tinda ke mijinkine nima idan nayi aure nima ni kadai zan shiga na nawa mijin ko??

Faduwa gaban Jannah yayi ta kalli falaq din da sauri tace

"Aa ni yanzu nima bazan iya shigaba sai matarsa"

"To ai kece matarsa Jan"

Mantawa jannah tai da fada hakan sbd rikicewan datai ta sake kallan falaq tace

"Yanxu bai tashiba inaga and ba buqatan tadashi mu tafi kawai idan ya tashi ya fito saimu gaidasa acan."

Sam falaq bata yadda da hakanba sbd bata taba zuwa ta fita ziqau batareda taga daddynta ba dan haka miqewa tai tana kama hannun jannah din tana ja zuwa hanyar master bedroom dinsa tana cewa

"To muje tare da matarsa da yarsa tinda ni kince na dena shiga ni daya"

Da sauri jannah take kokarin janye hannunta zata juya aka bude kofar Bedroom din wanda ya sakasu tsayawa cak dukansu itada falaq din suna kallan kofar.

Qamshinsa da koina yakeyi tin daga palon har koina ne ya bugo mata daga cikin kofar datake buden ta dago idanuwanta masu kyau ta kallesa.

Sanye yake da Ash balmains na wata crazy shirt me shegiyar tsada da straight wando sai tsadaddun shoes din dake kafarsa na ballies.

Fuskansa wani irin sabon sirrin kyau ne na safe wanda idan ka fito kafin ka fara hayaniya ko fita a cikin haske kake kasancewa fresh dinka wasu na kiran hakan da morning beauty ko morning freshness.

Fin karfinta zuciyarta tai ta kasa dauke fararen idanuwanta akansa tana masa wani irin kallan dayake bayyanarda gabaki daya sirrin dayake boye a zuciyarta,
Tsananin azabtuwan da zuciyarta take akan tsananin sonsa dayake maqale a cikinta ne idanuwanta ke loosing control gurin bayyanawa har idanuwan na cikowa da hawayen da batasan dasuba.

Falaq tsayawa tayi kallanta cikeda tausayawa sbd duk da ba komai take ganewa ba tasan Jannah na tsananin son Daddynta hakama a yanxu din kallo ne na ganin abinda zuciya take tsananin so amma ta kasa samu.

Ahankali ya qaro taku biyu ya tsaya a gabanta ya dan rankwafo kadan batareda ya kalli cikin idanuwanta ba ya kai bakinsa gefen fuskanta daga nesa kadan sbd kada falaq taji abinda zai fada da wata muryan data sakata qanqame hannuwanta a jikinta sbd kauri da tsananin nutsuwa da taushin muryan yace

"Me kikeson koyawa yarinyana?
Learn to control your feelings Ms,
Sbd kada ko koyar da ita irin hakan bata isa sanin kallan meye wannan ba"

Skipping bugawa zuciyar Jannah tai sbd tsananin kunya da baqin cikin maganarsa tareda wani irin qamshin dataji yana shiga hancinta wanda ta tabbatarda daga bakinsa yake fitowa kaman na lemon da mint sun hadu.

Dagowa yayi yai mata kallo daya yaga yanda idanuwanta ke cikowa da hawayen kunya da baqin ciki yayi gaba yana amsa maganar falaq a natse.

Rawa jannah taji kaman kafafuwanta sunayi
kasa riqe hawayenta tai saida suka sauko ta saka hannunta ta share tana juyowa da kyar ta biyu bayansu.

Mama na ganin fitowansu taji farin ciki ya sake cikata cikin farin cikin ganinsu tace

"Falaq meyasa ke wai bazaki girma bane kinbi kin kanainayesa bazaki bari itama jannah din ta samu damartaba."

Gaida maman yayi yana hanasu cigaba da zancen ta hanyar janyowa mama wani zancen daya san zai dauke hankalinta gaba daya.

Dining suka nufa banda jannah dataji ta kasa sakewa kwata kwata hakama taqi yadda ta sake kallansa sbd kada ya kuma tozartata.

Mama ce ta jata da kanta har Dining din ta zauna a kusa da maman saiga Sayd shima yazo ya zauna yana gaida mama itama kallanta yayi da kulawa suka gaisa kafin ya maida hankalinsa kan falaq datake gaidasa tanason basa labarai amma ba dama dole sai angama.

Suna fara breakfast din babu wanda ya sake magana hakama ita dai bata dagoba ta kallesa.

A natse taci Fried potatoes da liver sauce sai ketchup da kuma tea mara zafi sbd bata wani son zafi sosai a abinci.

Shi kansa abinda yaci kenan sai falaq da sayd da sukaci Da kwai da plantain mama kuwa kunin gyada ta hada dashi wanda yaji madara sosai yayi kauri da haske sosai.

Jannah dince ta fara gamawa amma bata bar table din ba sbd girmama su maman.

Shine ya fara miqewa yabar dining din sayd yabi bayansa sai a lokacin falaq ta dawo gurinta.

Saida mama ta gama tabar dining din itama ta miqe tareda falaq suna kokarin barin dining din Fiddausi tazo tafara tattara gurin.

Bedroom dinta ta koma ta zauna tana janyo wayarta ta sake saka kiran Dad dinta wanda basuyi magana ba da safen.

Waya ta fara yi da familynta da suka boye mata halinda Ammar yake ciki ta debewa kanta kewa sosai da wayan.

Lokacin sallah nayi tayi sallah ta sauya kayanta zuwa marasa nauyi sosau sbd ta saba bata iya wuni da kaya masu nauyi a jikinta.

Fitowa tai ta nufi kitchen dan taya Fiddausi aiki sbd zaman shirun ya isheta.

Falaq ma binsu tai kitchen din duka masu aiki suka fice daga kitchen din aka barsu sbd girmamawa.

Abincin rana din suka kammala a tare Fiddausi ta jera a dining ita kuma ta nufi dakinta ta sake wanka tanajin yar gajiya ta kwanta dan ta dan huta.

Sai yamma sosai ta fito lokacin su mama already sunci abincinsu dan haka ita kadai ta nufi dining din ta zauna falaq na islamiyya.

Gidan tsit ba hayaniya sbd Fiddausi na kitchen mama kuma tana can palonta.

Abincin ta zuba brown spaghetti ce dataji kidney da liver dasu vegetables sai kazan da aka gasa da vegetables.

Daidai cikinta ta zuba abincin ta zuba orange juice a cup tana fara ci kenan Fiddausi tazo dining din ta saks jera wasu abincin tana barin gurin qamshinsa ya doso gurin ta dago ahankali ta kalli hanyar shigowa dining room din daidai yana sako kai sanye da kayan shan iska alaman ya dade da dawowa daga aiki haryayi wanka.

Fararen qafafunsa da gashi me kyau ya kwantawa taiwa kallo daya ta juyo da kanta sbd three quarter Fendis ne a jikinsa farare da suka maidasa wani lafiyayyan Kyakkyawan matashi me ji da hutu da aji.

Shi kansa baiyi tinanin ganinta a dining dinba a daidai wannan lokacin dan haka ko kallanta bai sake yiba saida ya zauna ya kalleta itama shi ta dan dago zata kalla ta gaida zancensa ya katsata da cewa

"Akwai dabiun na rashin tarbiya da kikaxo dasu da kike buqatan sauyawa sbd tarbiyan tawa yar,
Na koyawa yata girmamawa da gaida na gabanta gashi ke da alama baki samu hakan ba"

Qarasawa yayi yana bayyanarda takaicinsa da mamakin rashin hankali da tinani irin na zaadens da babu abinda suka iya sai son zuciya da haryanzu suke a cikinsa.

Dagowa tayi idanuwanta na sauyawa sosai da tsananin ciwon zancensa ta bude baki jiki a mace zata gaidasa din ya daga mata hannu yana nuna mata abincin dayake kan table din da hannu fiskansa a daure sosai baya ko kaunar kallanta a gabansa.

Dan sunkuyar da kanta tayi ta hadiye hawayen da suka ciko idanuwanta ta miqe ta zagaya gefensa tafara serving dinsa hannuwanta na dan rawa zuciyarta cikeda damuwan datakejin kuka da kewan gidansu na zuwar mata.

Dauke kallansa yayi daga hannuwanta dake rawa yana cewa abincin ya ishesa.

Ruwa da juice din da Fiddausi ta shigo dashine taga yanda jannah din hannuwanta ke rawa ta qaraso ta ajiye ta juya.

Ajiye masa komai gabansa jannah din tai ta koma ta zauna sedai ta kasa cigaba da cin abincinta daci zuciyarta ke mata dan haka miqewa tayi ahankali tabar gurin jikinta a mace.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
69
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Chapter 84 · 0% Book details