← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 120

Sashe 10

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yamma ne sosai dan haka bai biya gidan mama sakina ba dan bata sabulu da omon daya siyo harda ita ba dan haka ya wuce gida saiya dubosu saika ya fito dasu yaje ya kai mata batareda ya shiga gidan ba san anjima da baba ila yai masa iyaka da shigar masa gida sedai ya tsaya daga waje gefen gidan mama sakinar ta fito ko kawai ya aika mata ummita ta shiga takai ta fito shikuma yana waje yana jiranta su koma.

Yana doso gidan tin bai karasa ba ya hango Ummita tana fitowa daga hanyar bayan gidansu tana kuka hannuwanta da kafafunta qasa da jini.

Wani irin abu ne ya daki kirjinsa da tsakiyar kansa dan haka da sauri ya qaraso ya tarbeta tareda ajiye kayan hannunsa ya jawota gaba daya jikinta yana kallan hannuwanta muryansa dayake da wahalar ji shima dan baya wani magana sosai sbd baida abokin firar yace

"Ina ummah?
Meya faru?

Kuka takeyi sosai ta juya bayanta ta nuna masa hanyar data fito tana cewa

"Umma ta tafi,
Dodo ya bita da gudu ta tafi......

Wani mummunan yawu me dacin gaske ya hadiye yana daukan ummitan ya nufi hanyar data nuna batareda ya tsaya fahimtar me take fadaba yana jin kaman kansa zai zare.

Duhun magriba yayi amma sam baya ma gani ya doshi hanya yana tafiya yana duba umman kaman zai zai haukace a take yaji yana ji dan haka ummitan dake jikinsa ya sake qamqamewa yana jefa kafarsa duk inda ya samu yana adduar Allah kada ya jarabcesa da wannan jarabawar me girman gaske akan mahaifiyarsa da ita da ummita sune rayuwarsa da hasken dayake gani a wannan rayuwar ko yaya ummansa ta koma yana tsananin buqatanta a hakan.

Tafiya yakeyi harya isa wani kauye duhu yai sosai amma kwata kwata baya hayyacinsa.

Kaf kauyen babu ummansa babu wanda ya ganda dan haka ya juyo ya dawo kauyensu lokacin tini akai ishai amma be zauna ba ya zagaye kauyen tas nanma babu umman ga ummita wahala da zazzabin raunikan jikinta sun saka tayi bacci a jikinsa jikinta zafi sosai.

Bai taba shiga mafi munin tashin hankali da firgici irin daren ba na rashin umman amma bai damu da daren ba haka ya doshi wani kauyen a cikin tsananin duhun dare nemanta idanuwansa sunyi wani irin mummunan jajir.

A cikin dare mafi tashin hankali a rayuwarsa kauyuka uku ya zagaye amma kwata kwata babu ummansa babu wanda ya ganta dan haka ya yanke jiki ya fadi qanqame da ummita zazzabi me mugun karfi ya gama gabalaitar da ita a jikinsa.

Jamaar kauyen daya somen suka yo kansa sbd lokacin har anfito sallan asuba gari ya waye sosai suka yo kansa suna son cire ummita a hannunsa amma yai mata wani irin mugun riqo da dole tana jikinsa aka zuba musu ruwa a tare.

A tare suka sauke ajiyar zuciya sedai kowannensu a galabaice musamman ummita shi kuwa ganin yayi kaman baya ganin komai sbd azaba da wahala tareda galabaita da tsananin tashin hankali.

Tashi zaune yayi yana gyarawa ummita zama a jikinsa yana sake rungumeta da kyau wasu zafafan hawayen daya manta rabonsa daya zubo suka gangaro daga fararen idanuwansa da suka koma jajir ya ambaci sunan umman ahankali yana rokon ALLAH ya kawo masa kowacce irin jarabawa indai ummansa zata dawo garesa zai jure ya runguma kaddarar.

Tausayinsa ne ya rufe jamaar gurin dan haka aka taimaka masa aka tayasa bincika neman umman tasa a kauyen amma har yamma babu labarinta kuma har dayan kauyen suka tayasa nemanta amma babuta.

Kauyensu ya nufo ummita na jikinsa a some sbd ruwan saman da akeyi sosai duk ya qare akansu.

Koda ya dawo kauyensu ana sallan ishai duhu yayi sosai,

Kofar gidan ya shiga wanda ruwan sama ya cika gidan kai tsaye dakinsu ya nufa ya bude ya shiga
Taku daya yayi zuwa biyu kafafunsa suka kasa daukansa ya zube a gurin yana fasa wani irin kuka me karfin gaske Ummita dake jikinsa azaba ta farfado ta bude idanuwanta daqyar batada karfin motsawa anan ta sake lumshe idanuwanta suka rufe jikinta ya sake sakewa alaman ta sake fita hayyacinta.

Kuka yakeyi sosai yana wani irin jijjiga zuciyarsa kaman zata fashe akan abinda yake ji,
Shima zazzabine sosai me karfin gaske a jikinsa amma ya kasa sakin Ummita barema yasan shika halinda yake ciki.

Kuka me yawa sa karfi sosai da idan da ba ruwa akeyib kusan duka makotan dake kusa sai sun jiyosa amma karfin ruwa bai bari anjisu ba.

Ummansa yasan a duk inda take tana cikin wannan ruwan da duhun dare wanda zai firgitata ta qarasa haukacewa mutane su kyareta su qyamacet su hantareta shikenan ta shiga gagarin da babu wani gata ko rufin asiri gareta........

Wannan ke saka zuciyarsa daukan wani irin nauyi kaman zai haukace shima yakeji ya fasa kukan da babu me jinsa bayan Allah dayake fatan ya kawo masa dauki da sassauci a wannan rayuwar.

Tsakar dare sosai ya dago jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumbura ya kalli ummita datake a sake jikinsa ya miqe ya koma gefen da babu sanyi a adakin ya gyara gurin kwanciyarsu ya kakkabe duk da baya ganin komai ya sauya mata kaya sbd na jikinta akwai sanyi ya kwamtar da ita.
#MAMUH
#BESTSTORY
#BESTLOVE
#BROTHERS LOVE
#LIMBAS
#ZADEENS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
8
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

*************
Koda cikin Fatima ya isa haihuwa karfin da zatai naqudar arziki batada shi sbd yunwa da ciwo tareda cikin da duk ya janyeta ta koma kana ganin qashin bayanta ya fito dosai da duk qashin kirjinta kana ganinsu idanuwanta sunyi ciki sosai tayani muni dik ya gama sauya kamanninta sbd ciwon da yunwar da bayan Allah da yayita babu abincin da zai dawo da ita yanda take kila.

Abdul yana kokarin daya fi na shekarunsa sbd har local government yake zuwa nema da aiki harma da tallan rage wadda bayayi da yawa sbd baya iya dadewa waje yake komawa gida gurin ummansa dan komai shine yake mata sbd baba ila ya rabasu da Mama sakina wadda take cikin tsananin daci da ciwon rai na hakan amma Abdul dinne ya roketa akan kada ta rabu da baba ila sbd su shiyasa kawai take zaune a gidan amma aurensa gabaki daya ya fita daga zuciyarta ba sauran sonsa ko qwaya daya a ranta gashi daman Allah bai bata haihuwaba tayi neman haihuwar harta gaji ta barwa Allah.

A cikin wannan halin da suke ciki ne Allah ya kawowa Umman naquda cikin ciwo da ukubar rayuwa tareda yunwar data gama kame duk wani kayan cikinta da gangar jikinta ta haihu,
Haihuwar data taho musu da sabuwar kaddarar da babu yanda zasuyi bayan rungumar rayuwa a yanda taxo musu batareda taimkon kowa ko kulawan kowaba bayan ta mama sakina da suke samu jefi jefi Abdul ya reni kanwarsa da mahifiyarsa wadda ta koma masa tamkar UMMITA wadda take yar shekara biyu zuwa uku dan kuwa duk inda zashi dasu yake zuwa sbd fita sukeyi su tafi yawo dan haka duk inda zashi yanzu suna tare dan haka da yawa ake musu kallan almjirai ko yan yawon neman sadaka duk da yana iya kokarinsa akansu gurin ganin ya tsaftace su.

Yanzu sun dena zuwa irin guraren dake kaman kasuwa ko tasha gurin aikin nema ko sanaa sbd bayason ana kallan ummansa da ummitan dan haka Local government yake zuwa dasu har makarantarsa wadda yake gaf da kammalawa yanzu.

Har ciki a ke barinsa shiga dasu saiya kaisu bayan ajinsu yace su zauna karsu tashi saiya gama ya fito.

Haka zasu sauna suyita wasa a gurin harya gama batareda da damuwa da abinda dalibai ke fada akan mahaifiyarsa da rabin ransa dayake jinta kaman shine babanta sbd BAABAH take kiransa dan bata san kowa ba bayanshi da ummanta hakama shi take kallo ubanta tinda umman ta koma kaman ita tare suke wasa duk da umman ta dena magana.
Chapter 10 · 0% Book details