← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 120

Sashe 103

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

***********
Maheer ma matsanancin shock dayafi na Dad ya shiga bakinsa na bushewa,

Shi kansa Ammar dayake tinanin hakanne yasan waye AZIZ LIMBA din jin maganar daga bakin AZIZ din sai daya mugun girgizasa ya kallesa da sauri idanuwansa na yin jajir harda cikowa da wasu hawaye masu tsananin karfi.

Dad kirjinsa tsananta ciwo yayi idanuwansa sukai jajir ya rintsesu ahankali zafafan hawaye masu tsananin zafi na gangaro masa,

Kallansu AZIZ din yayi da jajayen idanuwansa daya bayan daya tsananin ciwon dayake shimfide a zuciyarsa yana tasowa,

Akan Dad da idanuwansa ke tsiyayo hawaye masu tsananin ciwo yayi kafin ya saka hannuwansa biyu ya kamo wuyan rigarsa ya dagosa da karfi ya jijjigasa yace

"Kana hawayene sbd yarka datake hannun wanda bazai taba yafe abinda kukaiwa tasa 'yar ba?

Wannan radadin dakake ji a zuciyarka ko kadan baiyi zafi da ciwon wanda kuka sakamin ba"

Wurgi dashi a gadon AZIZ yayi yana dawo da kallansa kan Maheer daya isa da sauri ya tare Dad daya fado gadonsa numfashinsa na neman yankewa sbd zuciyarsa dake neman bugawa da tashin hankali yace

"Jinin Limbas a tsarkake yake baya da tsatsa ko daya,
Bana bata hannuwana da imanina da jinin kowa amma lalata rayuwarku da tabbatarda kun nema kisan kanku da kanku shine abinda bazan taba barin qasar ba saiya tabbata,
Ban taba so ko kaunar sadakar da kuka ban ba,
Amma bazan taba dawo muku da itaba saina mayarda ita masu aikin gidana ma sun fita daraja da kyan gani"

Ammar ne yayo kan AZIZ din cikin tsananin bacin ran da ko gani bayayi zai miqa hannunsa ya kama wuyansa Wani lafiyayyan marin daya sakasa juyawa gefen Maheer baya gani sosai ya sauka fuskansa daga Sayd wanda yasha gabansa a hankali yana masa kallan tsana me tsananin gaske,

Sake juyowa Ammar din yayi yana fita hayyacinsa zai sake nufar AZIZ Sayd ya sakar masa wani mahaukacin marin tareda kama hannunsa ya sake sakar masa wani marin idanuwansa ba rufewa shima zuciyarsa na tafasa tako ina jin yake ayau da suka fuskanci juna a matsayin su din babu boyo kaman zai iya kashe Ammar yakeji sbd radadi da tsana me karfi ce yake dannewa da boyewa tsawon lokaci amma banda yau.

Kasa dena tasowa Ammar yai sbd gabaki daya ya fita hayyacinsa AZIZ yakeson shaqewa ya rabasa da duniya ko zasu samu salamar rayuwarsu daya riga ya lalata masu su duka kaf zaadens.

Sayd da shima nasa idanuwan suke a rufe da zuciyarsa duk motsi daya idan Ammar yayi na yunqurin matsowa mugun naushin dayake fasa hancinsa yake sakar masa yana jin zuciyarsa na kasa samun sassaucin abinda yake ji ko kafan.

Maheer dayake riqe da Dad dake neman rasa ransa hawaye ne masu tsananin radadi da ciwo shima suka gangaro masa ganin yanda hancin Ammar ke fidda jini.

Juyawa AZIZ ya fice sbd shima zuciyarsa gap da sakasa hawayen tsananin ciwon dayake ransa....

Sayd kuwa saida ya tabbatarda Ammar ya zube qasa yana neman taimako kafin ya juya ya fice daga dakin hawayen d suka cika idanuwansa suna zubowa kan fuskansa ahankali.

Barin asibitin sukai,
Suna ficewa Maheer ya buqaci likitoci suyi gaggawan zuwa ga dad,

Ammar ma gaggawar ficewa akai dashi daga dakin ana wucewa dashi inda zaa dubasa,

Mimi kallo daya taiwa Ammar ta kusa yanke jiki ta fadi Saleem yayi saurin riqeta yana shiga tsananin mamaki da tsoron meya faru shima,

Jamian tsaro likitocin zasu kira Maheer ya hanasu yana cewa su barshi issue din cikin gida ne.

Hankalinsu dawowa yayi kan Dad da aketa kokarinsa ceto rayuwarsa datake nisa,

Ammar ma aka gyarawa fuska duk bandage dawowa yayi dakin suka zauna zaman jimami da qunci sbd babu me iya magana idan ba ganin sukai Dad ya farfado ba,

Maheer wasu hawaye ne masu zafi ne suka ganganro masa ahankali yana jin zuciyarsa na neman mutuwa,
Idan dad bai tashi ba baisan ta ina zai fara rayuwarnan ba da sauran familyn da nauyinsu zai rataya akansa baida mai jagoransa,

Ta ina zai fara fuskantar babbar matsalar da suka aikata su da yawa a wayi gari ace shi kadai ne zai fuskanceta sbd Ammar dai ya riga ya samu tabin kan da ba lallai ya karba hukuncin komaiba,

Tayaya zai iya kubutar da jannah daga AZIZ shi kadai?

Innalillahi wainna ilayhi rajiun"""' shine abinda zuciyarsa ke maimaitawa yanajin kaman zuciyarsa zata fashe.

Mimi bata iya magana a yanzu karfinta ya qare tas tayi weak sosai batajin dadin zuciyarta ko kadan,
Saleem ma kusan baida abin cewa ko tambaya sbd komaima a yanzu kamar baida amfani,
Dukkaninsu qasar suke son bari su koma inda suka fito rayuwar zatafi musu dadi acan,
Zasu bude sabuwar rayuwa su sake gina sunansu cikin kwanciyar hankali da Aminci.

Ganin jikin Dad din yana sake nisa sai kawai Maheer ya kira jannah daya san dad din zaiso ace ya bude ido yayi mata ganin karshe.

Koda Maheer ya sanar da ita ana sallar ishai lokacin dan haka sallar ta samu kawai tayi jikinta na dan rawa zuciyarta na wani irin rawar tsananin tsoro da tashin hankali.

Ko mama bata tsaya fadawa ba ta fita hannuwanta na wata irin rawa.

Ganin yanayinta ya saka falaq hanata driving tace suje da driver su kaita tinda dad din baya nan.

Bata musa ba sbd bata cikin cikakkiyar nutsuwarta matsanancin tsoro ne ya rufeta sbd batasan tina mutuwa akan mahaifinta da shine rayuwarta.

Tausayinta sosai falaq takeji sbd tasan irin tsananin so da kaunar datakewa Daddynta shi Jannah kewa Dad dinta dan haka kwatanta rayuwa babushi abune da shi kadai zai iya zarar da kai.

Koda suka isa asibitin falaq bata fita motar ba ta bari jan din ta tafi ita kadai sbd ta fara ganinsa ta samu nutsuwa tukuna.

Jannah na isa dakin a sanyaye ta bude ta shigo dukkaninsu suka dago jajayen idanuwansu da duk suka jeme suka zuba mata.

Sanyi qafafunta sukai ta tako ahankali hawayen cikin idanuwanta na saukowa ta nufi gadon Dad din wanda yake kwance kamar ba rai a jikinsa yayi mummunan jemewan data sakata rintse idanuwanta tana zaunawa bakin gadon ta dora hannunta akan nasa tana fashewa da kuka mara sauti.

Tsit dakin yayi kowa ciwon ransa na qaruwa kukanta na ratsa kunnuwansu.

Mimi ce ta bude baki Ahankali batada ko wani karfi sosai ciwon dayake cin zuciyarta na bayyanuwa cikin mutuwar jiki tace

"Mahaifinki bai hada soyayyarki data komai da kowa ba amma ayau mijin da kika zaba kikace shi kikeso wanda a hakan mahaifin naki ya zabi farin cikinki akan familynsa shine yake neman neman ganin bayan mahaifinki da ahalinki,
Me ahalinmu sukai masa dayake neman ganin bayanmu?
Wane irin miji ne zai cakumi mahaifin matar dayake aure bayan yasan baida lafiya sosai???
Jannah me kikeyi da wannan mijin?
Me zakiyi da miijin dayake neman rayuwar ahalinki?

Kalli fuskan Ammar kiga abinda yayi masa,
Wannan shine mijin da zuciyarki ta zabar miki akan ahalinki da suka zabeki fiyeda rayukansu?

Wannan shine sakamakon soyayyar da mukai miki tin kina yarinya?

Dago jajayen idanuwanta tai cikeda mamaki da tsoro harma da fargaba me tsanani tana kallan Mimi kafin ta maida kallanta kan fuskan Ammar da sai a lokacin ta lura nade take da bandage mummunan duka ne a fuskan ba kyan gani.

Waya Ammar ya fidda ya nuna mata hotinan da yayiwa AZIZ a lokacin daya shaqo Dad ya zubar.

Mummunan faduwa gabanta yayi ta dago cikin slow ta kalli Maheer wanda idanuwansa suke jajir ya kasa kallanta.

Kan Saleem ta maida kallanta wanda ya saukar da idanuwansa da sukai jajir shima a hankali yana jin ciwo da radadin abun har qasan zuciyarsa.

Wani irin nauyi me girman gaske taji yana danne kirjinta ta juya ta kalli mahaifinta hawayen baqin ciki na gangaro mata tareda da jin soyayyar AZIZ LIMBA na sauka daga zuciyarta ahankali tana zubewa.

Ammar kuwa bude bakinsa dayake rawa sosai kamar me koyan magana sbd kansa dayake a juye tin dazu da azabar duka ta tayar da ciwonsa yana bubbuga kansa da hannunsa idanuwansa na sake rinewa da ja yace

"AZIZ LIMBA makashi ne,
Shine ya kashe Daddy mahmoud,
Shine yake kashe kowa,
Shine ya kama su Abraham,
Shine yakeson kashe dad,
Idan ya kashe dad zai kashe kowa,
Kema jannah yace saiya kashe ki,
Zai kashe kowa,
Bazai dena ba saiya kashe kowa dayake zaadens sbd Qanwarsa,
Qanwarsa ce a kirjin jannah,
Qanwarsa ta mutu,
Yace saiya kashe kowa,
Ya fada da bakinsa.......

Shiru sukai dakin ya sake daukan shiru maganganun Ammar na futa hayyaci ne kawai suke tashi ahankali kuka na zuwar masa.

Maheer zuciyarsa ta gama saddakar da komai vazan iya hana ammar maganar data saka su mimi shiga tinani ba sbd komai dai yazo karshe da alama.

Mimi gabaki daya hawaye take tsiyayarwa na baqin cikin jin Ammar na magana a zare basuda abinda zasu iya yi,

Saleem ma baqin ciki da ciwon zarewan Ammar din ne ya hanasa fahimtar abinda Ammar din yake fada.

Falaq dake tsaye kofa isowanta kenan taji dukkanin maganar da Ammar yake fada akan Daddynta wata irin mummunan bugawa kirjinta yayi kafafunta suka dauki rawa zuciyarta na kasa dauka ta shigo idanuwanta na cikowa da hawaye masu zafi tace

"Daddyna ba makashi bane bazai kuma taba zama makashinb insh......."

Ammar da dukkanin jikinsa ke rawa kanta yayi idanuwansa na rufewa ya shaqota yana bugata da bango da karfi bakinta ya fashe da jini ya saka hannuwansa biyu ya shaqeta yana cewa

"Saina kashe AZIZ LIMBA,
Saina kashesa saina kashesa kaman Ummitah,
Saina kasheki,
Ai kene AZIZ LIMBA......
Chapter 103 · 0% Book details