← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 120

Sashe 11

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga makaranta shagon dayake aiki yake wucewa dasu ya siya musu abinci suci ya ajesu guri daya suyita walwalansu harya gama se yamma su nufo gida sbd baya kaiwa dare sbd su duk da megidansa yana son ya ringa kwana shagon sbd yadda dashi da yayi da kuma kokarinsa tareda amanarsa amma sam baya iya hakan sbd kare mutuncin ummansa da Ummitansa dan haka duk abinda yake samu a aiki ko sanaa yamma nayi yake wutowa gida dasu su wanka suci dan abinda ya samu ya ringa koyawa ummita dan karatun yara har suyi bacci itada umman ya gyara musu gurin kwanciya ya kaisu su kwanta shima ya zauna gadinsu dan baccinsa rabi da rabi ne akansu sam bayada wata irin yadda da kowa gashi basada koda rabin gidan a zube dan haka baya wani bacci akansu.

Ranar wata alhamis ya samu wani aiki a wani sabon kamfani da zaa gina a local government na gyaran shinkafa me kudin dayafi tsaron shagon dan haka ya karba ya hada biyu yana yi sedai aikin gurin akwai hadari dan haka dole yake barin su ummita a gida amma saiya fada musu yafi so ashirin kada su fita koina.

Sunji maganarsa basa fita dik ya tafi harya dawo baya cikin nutsuwa amma yana tarar dasu a gida basa fita koina sedai gidan zai tarar anyi masa kaca kaca hakama sunyi wata irin dauda hakanan zai tsaftacesu ya gyara gidan ya basu abinci suci su koshi suyi sallah wadda tasa ce kawai ta arziki su kam ture ture sukeyi a gurin sallan tsakanin umman da ummita yana jinsu zai kyalesu a gama a hakan.

Akwai wata irin kauna da so me tsananin gaske tareda shaquwar datake basa tsoron da baisan na mene ba a tsakaninsa da Ummansa da Ummitansa haka suke sakasa wasa dasu dole wanda su kadai ne suke ganin dariyarsa da walwalwansa dan Allah ya sako masa wani irin kame kai tin yana yaronsa shiyasa ya taso hakan.

Tin yana fargaban barinsu a gida yaje ya dawo harya dan rage fargaban yana aikinsa cikin dan nutsuwa amma bawai hankalinsa baya gidan bane dan baya kara ko minti daya yana tashi aiki yake komawa gidan dan ya dena zuwa makaranta exam kawai yake jiran ranar yinta yazo ta gamawa tinda suka shiga ss3 ya dena zuwan waec kawai yake jiran yi.

A yau tinda ya kamo hanyar zuwa gida yakejin baida nutsuwa dan haka ya qara sauri yana jin kirjinsa na nauyi ya kuma saba da hakan a duk lokacinda bay taredasu jin yake zuciyarsa ta ringa shiga damuwa da nauyi kenan.

Yamma ne sosai dan haka bai biya gidan mama sakina ba dan bata sabulu da omon daya siyo harda ita ba dan haka ya wuce gida saiya dubosu saika ya fito dasu yaje ya kai mata batareda ya shiga gidan ba san anjima da baba ila yai masa iyaka da shigar masa gida sedai ya tsaya daga waje gefen gidan mama sakinar ta fito ko kawai ya aika mata ummita ta shiga takai ta fito shikuma yana waje yana jiranta su koma.

Yana doso gidan tin bai karasa ba ya hango Ummita tana fitowa daga hanyar bayan gidansu tana kuka hannuwanta da kafafunta qasa da jini.

Wani irin abu ne ya daki kirjinsa da tsakiyar kansa dan haka da sauri ya qaraso ya tarbeta tareda ajiye kayan hannunsa ya jawota gaba daya jikinta yana kallan hannuwanta muryansa dayake da wahalar ji shima dan baya wani magana sosai sbd baida abokin firar yace

"Ina ummah?
Meya faru?

Kuka takeyi sosai ta juya bayanta ta nuna masa hanyar data fito tana cewa

"Umma ta tafi,
Dodo ya bita da gudu ta tafi......

Wani mummunan yawu me dacin gaske ya hadiye yana daukan ummitan ya nufi hanyar data nuna batareda ya tsaya fahimtar me take fadaba yana jin kaman kansa zai zare.

Duhun magriba yayi amma sam baya ma gani ya doshi hanya yana tafiya yana duba umman kaman zai zai haukace a take yaji yana ji dan haka ummitan dake jikinsa ya sake qamqamewa yana jefa kafarsa duk inda ya samu yana adduar Allah kada ya jarabcesa da wannan jarabawar me girman gaske akan mahaifiyarsa da ita da ummita sune rayuwarsa da hasken dayake gani a wannan rayuwar ko yaya ummansa ta koma yana tsananin buqatanta a hakan.

Tafiya yakeyi harya isa wani kauye duhu yai sosai amma kwata kwata baya hayyacinsa.

Kaf kauyen babu ummansa babu wanda ya ganda dan haka ya juyo ya dawo kauyensu lokacin tini akai ishai amma be zauna ba ya zagaye kauyen tas nanma babu umman ga ummita wahala da zazzabin raunikan jikinta sun saka tayi bacci a jikinsa jikinta zafi sosai.

Bai taba shiga mafi munin tashin hankali da firgici irin daren ba na rashin umman amma bai damu da daren ba haka ya doshi wani kauyen a cikin tsananin duhun dare nemanta idanuwansa sunyi wani irin mummunan jajir.

A cikin dare mafi tashin hankali a rayuwarsa kauyuka uku ya zagaye amma kwata kwata babu ummansa babu wanda ya ganta dan haka ya yanke jiki ya fadi qanqame da ummita zazzabi me mugun karfi ya gama gabalaitar da ita a jikinsa.

Jamaar kauyen daya somen suka yo kansa sbd lokacin har anfito sallan asuba gari ya waye sosai suka yo kansa suna son cire ummita a hannunsa amma yai mata wani irin mugun riqo da dole tana jikinsa aka zuba musu ruwa a tare.

A tare suka sauke ajiyar zuciya sedai kowannensu a galabaice musamman ummita shi kuwa ganin yayi kaman baya ganin komai sbd azaba da wahala tareda galabaita da tsananin tashin hankali.

Tashi zaune yayi yana gyarawa ummita zama a jikinsa yana sake rungumeta da kyau wasu zafafan hawayen daya manta rabonsa daya zubo suka gangaro daga fararen idanuwansa da suka koma jajir ya ambaci sunan umman ahankali yana rokon ALLAH ya kawo masa kowacce irin jarabawa indai ummansa zata dawo garesa zai jure ya runguma kaddarar.

Tausayinsa ne ya rufe jamaar gurin dan haka aka taimaka masa aka tayasa bincika neman umman tasa a kauyen amma har yamma babu labarinta kuma har dayan kauyen suka tayasa nemanta amma babuta.

Kauyensu ya nufo ummita na jikinsa a some sbd ruwan saman da akeyi sosai duk ya qare akansu.

Koda ya dawo kauyensu ana sallan ishai duhu yayi sosai,

Kofar gidan ya shiga wanda ruwan sama ya cika gidan kai tsaye dakinsu ya nufa ya bude ya shiga
Taku daya yayi zuwa biyu kafafunsa suka kasa daukansa ya zube a gurin yana fasa wani irin kuka me karfin gaske Ummita dake jikinsa azaba ta farfado ta bude idanuwanta daqyar batada karfin motsawa anan ta sake lumshe idanuwanta suka rufe jikinta ya sake sakewa alaman ta sake fita hayyacinta.

Kuka yakeyi sosai yana wani irin jijjiga zuciyarsa kaman zata fashe akan abinda yake ji,
Shima zazzabine sosai me karfin gaske a jikinsa amma ya kasa sakin Ummita barema yasan shika halinda yake ciki.

Kuka me yawa sa karfi sosai da idan da ba ruwa akeyib kusan duka makotan dake kusa sai sun jiyosa amma karfin ruwa bai bari anjisu ba.

Ummansa yasan a duk inda take tana cikin wannan ruwan da duhun dare wanda zai firgitata ta qarasa haukacewa mutane su kyareta su qyamacet su hantareta shikenan ta shiga gagarin da babu wani gata ko rufin asiri gareta........

Wannan ke saka zuciyarsa daukan wani irin nauyi kaman zai haukace shima yakeji ya fasa kukan da babu me jinsa bayan Allah dayake fatan ya kawo masa dauki da sassauci a wannan rayuwar.

Tsakar dare sosai ya dago jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumbura ya kalli ummita datake a sake jikinsa ya miqe ya koma gefen da babu sanyi a adakin ya gyara gurin kwanciyarsu ya kakkabe duk da baya ganin komai ya sauya mata kaya sbd na jikinta akwai sanyi ya kwamtar da ita.
#MAMUH
#BESTSTORY
#BESTLOVE
#BROTHERS LOVE
#LIMBAS
#ZADEENS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
9
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

********
Tashi yayi ya fito cikin duhun ya sauya kayansa yaje toilet ya fito yayi alwala ya dawo dakin
A gefen ummita yayi sallah yafara sabon kuka yana fadawa Allah ummansa kadai yake fatan Allah yabata kyakkyan kariya tareda fatan dawowa garesa.
Chapter 11 · 0% Book details