← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 120

Sashe 35

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin daga lokacinda ta wayi gari ta samu kanta a sabuwar rayuwa daukeda sabuwar zuciyar datake bugawa a kirjinta tasan duniyarta ta sauya ta dawo sabuwa a daidai lokacinda ta cire rai da rayuwa gabaki dayanta,

Allah ya bata damar cigaba da rayuwa a lokacinda take saka ran ta farko ta samu kanta a duniyar barzahu,

Duk wanda zuciyarsa take bugawa a kirjinta tana masa fatar samun rahamar ubangiji dashi da danginsa a duk inda suke,
Harta bar duniya bazata dena yi masa addua ba sbd sadaukarwansa gareta.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana lumshe idanuwanta tana sake jin bugun zuciyar wadda take tata ayanzu yana ratsata cikeda shauqi da samun nutsuwa da yanayin da bata saniba a baya na bugawar Lafiyayyar zuciya a kirjinta.

Ayau kusan wata hudu da kwanaki kenan da aikinta amma haryanzu ta kasa sabawa da sabuwar rayuwar data samun koyaushe jinta takeyi kamar sabuwar mutum sedai kauna da tsananin son datakewa yan uwanta familynta babu abinda ya sauya saima qaruwa da yayi sbd jajirwansu gareta.

Kaman yanda samun lafiyarta ya sauya rayuwarsu gaba daya a qanqanin lokaci sbd sabon farin ciki da jin dadine tareda sabuwar rayuwa ta dawo musu sabuwa dan haka komai nasu ya dawo tamkar baya kusan ma fiye dan farin ciki da kwanciyar hankalin dasuke dashi yanzu na tafiyar da komai yafi na bayan.

Ta jima a tsaye kafin ta juya ta fito toilet din.

Qamshin dayake tashi a bedroom din nata ne ya shiga hancinta ta dan Lumshe ido tana jinsa yana ratsata sbd komai a yanzu jinsa take kamar sabo gareta.

Gaban mirror ta nufa bayan ta zaro wani towel din tana goge jikinta a hankali kamar batason taba soft fatarta sosai.

Da kanta ayau ta shirya kanta sabanin tinda suka gama jinya a asibiti suka dawo gida Mimi ke tayata shiri sbd batason tayi aiki da jikinta ta gaji sbd sun saba a lokacin ciwonta abu daya takeyi zuwa biyu ta gaji sosai ba kuzari.

Body milk me kyau da qamshi ta shafa tareda Turare mai sanyin qamshi ta miqe ta nufi closet nata ta saka undies kafin ta saka oversize skirt and shirt na Liliana ta saka hula me laushi da rashin nauyi a kanta ta fito da slippers a kafarta sbd yunwa takeji abinci take buqata.

Anty Anny ce ta nufo palon itama sanye da shaking doguwar riga mara adon komai sai kudi tana qamshi fuskanta fresh dan itama gaba daya yinin ranar bata fito daga bedroom ma bare palonsu harta fito zuwa nan sai yanzu data fito neman abincin da zata dan duk da a familyn kowa da nasa bangaren amma a hade suke guri daya babu wani rarrabewa sosai dan kusan duka a guri daya suke kowa baifi kayi tafiyar corridor ba zuwa palo da bedrooms wani hakama duk yanda kowa yake bangarensa a tare ake cin abinci dining room dinsu daya ne hakama chiefs dinsu da masu aikin.

Rayuwar hutu kawai sukeyi mazan gidan ne suke fita aiki suma bawai sammakoba tinda sune masu companies dinsu amma matan kuwa da saleem ma sai lokacinda suka ga dama suke fitowa idanma ba abinci zasuci ba saika wuni a gidan bakaga ko dayansuba sai idan dare yayi ake taruwa babban palon ayita fira da yar hayaniya cikin walwala.

Anny na ganin Jannah ta zuba mata idanuwanta tana kallan yanda take sake warwarewa tana komawa lafiyayyar jannah dinta wadda ita bata saniba a baya,

Wani irin sirrin kyau da kwarjini ne da itama duk da bata gama zama cikakkiyar budurwar data amsa sunanta budurwanba amma haka kawai wani lokacin sai take mamakin saa irinta jannah din kowa sonta yake,
Babu abinda ta nema ta rasa,
Kowa zai iya komai dan bata abinda takeso,
A irin wannan gatan da Jannah din take ciki me zata nema a duniyar nan ta rasa?
Duk yanda familyn suke ganin babu abinda bazasu samar mata indai har tanaso akwai abinda yafi karfinsu shine ikon Allah,
Ita kanta zataso Allah ya kawo abinda Jannah zataso fiyeda komai ko buqata fiyema da zuciyar da aka dauki rayuka da dama akanta amma kaf familyn babu wanda zai bata kuma dukiyarsu bazata taba iya siya musu ba,

Zataso taga wannan ranar sedai batajin tana zuwa dan raine kadai bazasu iya siya mata amma ko rai din da zaace musu ana iya sakawa wani ran wani to tabbas zasu iya sedai Allah bai bada damar hakanba.

Isowan Jannah gabanta ya sakata sake murmushi tana sake kallan Jannah da yanayi na tinani kala kala akan fatan zuwan ranar da jannah zata dandana rashin ba komai ake nema a samu ba.

Da murmushi a fuskanta da kulawa tace

"Hey Jan sai yanzu kike fitowa?
Yaya jikinki?
Ya kikeji yanzu?
Karki manta duk abinda kikaji ba daidaiba ki sanar"

Fararen idanuwanta ta kalli Anny din dasu kafin ta saukar da murmushin kwanciyar hankali a fuskanta tana cewa

"Anty Anny karki damu i dont feel any uncomfortable yanayi,
Am all good"

Gaba tayi anty anny din na bin bayanta tana cewa

"Masha Allah"

Mimi ce itama ta fito a lokacin tana waya cikin walwala da annushuwa tabi bayansu dukansu dining room din suka nufa suka zauna daman dining din baa dauki mintina da yawa da gama shiryasa ba sbd ansan lokacin cin abincinsu na rana yayi kowane time zasu iya fitowa.

Suna zama qamshin Ammar ya doso dakin me sanyi da tsadar gaske tareda rashin hawa kai ko kadan.

Jannah ce taji wani sanyi yana ratsa xuciyarta tareda qamshin nasa ta dago idanuwanta tana kallan kofar daidai da shigowansa sanye cikin black thick riga da wando masu laushi fuskansa fresh da alama bai fita koina ba yau din shima yana gida hutu yake sosai haryanxu.

Kyakkyawan fuskansa jannah take kalla tana jin bazaa samu namijin da zai kai Ammar Zad kyau da kwarjini tareda haiba ba a idanuwanta har abada ba,

Ammar Zad shine mafi kyawun namiji data sani wanda shi kadai take zubawa ido bata gajiya da kalla.

Kallan datake masa ya saka Anny sakin murmushi tana kallansa shima kallan Jannah din yayi yana sake murmushi yana kujera ya zauna yana cewa

"Me Jan Zad take kalla??

Mimi ta kalla kafin ta kalli Anty Anny ta rage muryanta tace

"The one and only Ya Ammar Zad"

Mimi na jinsu farin ciki ya sake cikata tai sallama da wayarta ta kashe ta ajiye tana kallan Ammar din daya zauna kusa da ita yana daukan cup din fresh juice da akai na gida ya kai bakinsa yana cewa

"Mimi barka da rana"

Kafin ta amsa Jannah ma tace

"Sannu da fitowa Mimi"

Anny ma gaidata tai ta hada duka gaisuwar tasu tai musu amsawa daya tana cewa aci abincin tukuna wani zancen.
##MAMUH
#JANNAH ZAD
#AZIZ AY LIMBA
#AMMAR ZAD
#BESTLOVE STORY
#CRAZYLOVE
#BILLIONAIRES WAR

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
[27/12/2024, 3:20 pm] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
28
*_LADIES COLLECTION AND MORE_*
08169307477
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S COLLECTION AND MORE

ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻

Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko

08169307477

Address bayan gidan drugs katsina State

Kayan mu masu inganci ne sosae

Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯

***********
Da asuba jirginsu ya sauka Sayyid yana a sanyaye baida wani kuzari ko yin abinda ya wuce bin bayan Alh saad sawu kan sawu sbd kansa dayaji yana juyawa samun kansa a baqon guri inda bai taba tinanin zuwaba ko samun kansa ga jajayen fata tako ina suna wuce suna sake saka kansa juyawa amma ya daure babu abinda yake buqata irin ganin ABDULAZIZ LIMBA.

Mota suka hau wadda kai tsaye takaisu train station suka siya ticket din zuwa Milan wanda acan ABDULAZIZ din yake.

A train ma wata sabuwar duniyar Sayyid yake kalla wadda tale sake juyar da kansa sedai ko dagowa bayayi kansa na qasa Allah yasa kayan sanyi ne masu kyau da kauri a jikinsu dagashi har Alh saad dan haka rashin wayewansa da gurin ya boyu shi kuwa Alh Saad dayake gogagge ne a yawon qasashe sam babu abinda ya damesa sajewa ma yayi dasu banda banbancin fatar amma turancinsa dayakeyi hankali kwance cikin qwarewa yana waya da wanda zai kaisa har gidan ABDULAZIZ

Tafiya sukai me dan tsayin data saka Alh saad jin daya sani flight suka sake bi zuwa milan din..

Suna sauka daga train Station daga nan kai tsaye motace ta daukesu zuwa Address din Fash wanda yake abokin karatun ABDULAZIZ tin abaya amma yanzu basa tare amma yasan sabon gurin dayake zama yanzu sbd dukkaninsu sun zama busy kowa ya samu success din dayake nema.

Koda suka isa gidansa cikin sakewa ya tarbesu tareda riqesu sukai sallolin dasuke kansu sukai breakfast wanda daqyar Sayyid ya tura abincin a cikinsa sbd ba cimarsa bace hakama zuciyarsa kwata kwata a sanyaye take ba dadi ko kadan nauyi yakeji a kirjinsa.
Chapter 35 · 0% Book details