← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 120

Sashe 41

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa palonsa take kokarin nufa Kofar palon Mama ta bude maman na fitowa tana kokarin saka kiran numbern data kasa nemowa da kanta tana kiran Fiddausi tazo ta nemo mata.

Cikin ihun daya saka maman firgita tana saurin ja da baya wayar hannunta na faduwa falaq ta saki tana rufe idanuwanta da sauri tana cewa

"No no no,bazan fara saka Mama a idonaba,
Ina fara ganinta shikenan idona zai zama wani iri ayau,
Idona babu wanda zai fara gani se the No 1 handsome and the most beautiful and amazing BestDaddy in Falaqs Universe..So i can't let my beautiful eyes su fara da ganin oldLady.

Fiddausi datake bayanta maman ta kalla tana danne dariyarta

Mama kuwa data saba da wannan iya shegen na Falaq din hade fuska tayi sosai tana gyara tsayuwarta daga firgitan datai tana cewa

"Fiddausi dakyau,
Kina kallan yarinyar nan ta zuba wannan ihun tana kusa dake baza kiwa bakinta mugun dukan da saiya fashe ba kika tsaya a bayanta kina dariya tana cewa Uwar ubanta mayya ko??

Falaq na jin hakan ta saka hannuwanta tana rufe kunnuwanta tana bin bango idonta a rufe tana cewa

"Har muryan kowa bazanji ba Muryan datafi na kowa dadi and Nutsuwa"

Nufota mama ke kokarin yi tana cewa

"Kamo mun ita Fiddausi ki ban nan...

Tana jin hakan da gudu ta qarasa hanyar palonsa tana Kiran sunansa da karfi sbd tasan Fiddausi na kaita Dukanta Maman zatai sbd a duniya ita kadaice take dukanta ko zaneta Daddynta baya ko dago kai bare iya cewa komai amma ko school baa dukar masa 'ya sam bai nuna zai yadda ba dan haka kaf rayuwanta maman kadai take tsoro duk da hakan baya hanata fadan magana sedai maman ta bige bakin amma bayan mama sbd Daddynta daya tsaya mata bata tsoron kowa duk da tana qarama amma sam batajin tsoron kowa a ranta sbd ubanta ya tsaya mata.

Ihun kiran Daddynta datake ya isa har makeken dakin Sayd dayake bacci cikin lafiyayyan gadonsa sanye da kayan baccin Logous Ash cikin duvet dinsa me laushi dayake tashin qamshin jikinsa da gama kama turarensa..

Sama sama yake jiyo ihun nata yana shiga kunnensa dan haka motsawa yayi Ahankali tareda miqa hannunsa daya batareda ya bude idanuwansa ba ya janyo wani pillow dayake gefensa ya rufe kunnuwansa yana komawa baccinsa.

Mama cewa tai "Fiddausi idan baki kamo mun ita kika kawo mun ba zaki fuskanci bacin raina kuwa ayau"

Falaq na jin hakan ta qarawa kafafunta gudu tana isa kofar palon ta miqa hannu zata bude aka bude kofar palon..

Wani irin nutsatsiyar qamshi mai sanyin dadi dayake tabbatarda tsadarsa a shaqa daya sanyin ac ya kado waje daga cikin palon wanda har inda mama take tsaye yakai yana sauya numfashin main babban palon gaba daya..

Bude kyawawan idanuwanta da suke sak nasa falaq tai tana kallo tin daga fararen yatsun kafarsa dasuke wani irin fes kaman baya fita dasu sanye cikin versace slippers,

Sanye yake da black pyjamas Basu tsantsi sai jacket me girma daya sako dazai fito daga bedroom dinsa sbd tashinsa kenan daga bacci muryanta ta fiddosa.

Fuskansa datake wani irin fresh ta kalla ko morning face dinsa ganin takeyi tafi duka daddies din duniya kyau dan har fada takeyi a school da fahari Daddynta is the most handsome mutum dayafi kowa kyau.

Hannuwansa dake cikin aljihun jacket din jikinsa ya zare yana bude hannuwansa kafin ma ya karasa kai hannuwan nasa akan fuskanta ta fada jikinsa tana cewa

"Yesss BestDaddy idanuwan Falaq Aziz suka fara gani ba Oldy ba"

Da farin ciki sosai a muryanta da yanayinta ta qarasa zancen tana qanqamesa cikeda tsananin son mahaifin nata.

Wani Kyakkyawan murmushin daya saka Fiddausi saurin sauke kanta sbd yanda ta kusan dauke wuta agurin ya sake mai sauti yana durqusawa ya ajiye gwiwowinsa qasa sbd ta rungumesa da kyau ya rungumeta shima yana gyara mata veilhijab dinta ya bude baki da muryansa dake cike da wani irin nutsuwa da steez daya gama kamasa yace

"Bazaki dena tsokanar Mama ba ko?
Kinason ta dokamun bakin my one and only Falaq Aziz"

Sakinsa tayi tana juyawa ta kalli Hanyar da maman take tana riqe hannunsa cikin nata tace

"To ni kasan ai bazan yadda na fara ganinta ba banfara ganin My Besty ba"

Hancinta ya shafa yana kallan Fuskan Ummitansa akan tata ya sake sakin murmushin daya fito daga asalin zuciyarsa yanajin kaunarta data uwarta da bata duniya suna yiwa zuciyarsa yawan da yakejin ko tinanin komai bazaiyiba akan basu ransa,

Idan yana kallan fuskan falaq duniyarsa nutsuwa take tana samun sanyi da nitsatsen farin ciki me yawan gaske duk da rayuwarsa na cikin wani irin bushewan da har abada bazata sake jiquwa ba sbd rashin Ummitah wadda rashinta shine asalin ciwonsa da ba warkewa bawai na rashin iyayensu ba.

"Amma falaq Aziz tasan cewa Maman itace maman Bestyn nata fa,kuma shi Bestyn Ai yana son mamansa sosai...

Bata fuska tayi tana cewa

"Ai sbd itace ta maman Bestyna ya saka nake tsoronta,kuma idan baka nan ai ina jin duk abinda ta fada,
Nidai Daddy karka bari ta dukarmun baki,
Duk ta qara masa tsowo sbd duka gashi yanadon ya dena kama da naka"

Mama data nufosu taji abinda take fada cikin quluwa tace

"AZIZ kana jin abinda take fada sai murmushi kake mata ko?

Dagowa yayi yana kallan Maman da sauran murmushin akan fuskansa dake cikeda da kwarjini ya kalli maman yana cewa

"Mama barka da safiya"

Amsawa tayi tana kallan Falaq din data boye bayansa tana cewa

"Arzikinki daya yau tafiya zakiyi da sai kin kwana biyu bakinki baiyi magana ba a gidan nan"

Turo baki tai tana qin cewa komai sbd maman na cewa Daddynta ya matsa gefe matsawar zaiyi dan haka tai shiru tana turo baki.

Shi kuwa murmushi kawai yayi sbd mamance kadai take discipline na Falaq din sai Sayyid da shima yake dan bude mata ido amma idan baa gaban Babanta bane.

Maman magana zatai dashi dan haka Falaq din ta shige palonsa shi kuma suka koma palo da maman sukai maganar rashin lafiyar Baba alhassan tukuna ya koma dan shiryawa sbd lokacin fitowansa ma baiyiba rigimar falaq dince ta fiddosa.

Yana shiga palon tana zaune tana duba abu a ipad dinta tana dariya sosai,

Kai tsaye Bedroom dinsa ya nufa ya rufo

Kayan jikinsa ya zare lafiyayyar fatarsa ta bayyana tana daukan ido sbd samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau.

Toilet dinsa dayake da girka sosai ya shiga tareda nufar shower ya sakarwa kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa ruwan na sauka akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna dumama jikinsa.

Bai wani jima sosai ba yana wanka dasu gyaran fuska da sauransu kafin ya fito daure da babban towel me kauri brown jikinsa na fidda qamshin shower Soap dinsa na Ocean seaweed.

Goge jikinsa yayi a natse sa wani clean towel din kafin ya fara shafe jikinsa da bodymilk da mix na oils na Ngenas da suke saka jikinsa glowing da kyan gani da wani irin soft ya shafa perfs dasu bodyMist da sauransu kafin ya gyara fuskansa yai brushing gashin kansa dayake a kwance da santsi irin na asalin filani.

Bai dauki mintina sosaiba bayan gamawa ya shiya cikin Navyblue jeans da White long-sleeved shirt data nutsu a jikinsa sbd tasan kudin daya siyeta.

A cikin tarin tsadaddun designer agogayensa dake jere a doguwar glass drawer daya ya bude ya dauko black cartier ya saka sai navy blue Lv fcap daya sako ya fito yana daukan wayarsa ipad dinsa datake iri daya sak da 'yarsa.

Yana fitowa koina a palon an sake gyarasa kamshi da sanyin ac komai neat dukda bawai datti ko wani hayaniya a palon komai unique,simple and luxuries ne kawai.

Fiddausi ce take gyara komai na bangarensa dana Falaq saina Sayd da mama amma sauran gidan masu aiki ne ke aikin.

Tana ganin fitowan Daddyn nata ta ajiye abinda yake hannunta ta miqe tayo gurinsa tana cewa

"You're morethan handsome MyBesty"

Juyowa yayi kalleta tana hada hannunta da nasa ta riqe yace

"And you??

Dariya tayi tana dawowa gabansa tana tafiya da baya suna tafiyar a haka tace

"I'm my father's daughter,so I'm the beauty itself"

Murmushi me nutsuwa kawai ya sake mata suna fitowa palon inda suka tarar da Mama na zaune tana magana da Fiddausi dake fada mata yanda sukai da Falaq da safen tana dariya.

Sayd kuwa a tsaye yake shigowansa kenan palon yana waya ganinsa ya sakasa qarawa ya karbi ipad din datake hannunsa yana masa barka da fitowa ya koma gefe yana cigaba da waya akan baqin da zasu tattauna dasu gashi AZIZ din yau ranar 'yarsa ce sbd da kansa zai rakata sbd kowa iyayensa zasu tafi dan haka shima yace a dakatar da duka schedules nasa na kwana biyu sai Falaq Aziz ta sun gama camping dinsu.

Hakan yasak yaketa kokarin ji da ayyukan da baqinsu tareda clearing schedules din yaji da komai.

Dining suka nufa dukkaninsu Falaq na sake boyewa gefensa tana leqa mama da ko kallanta bataiba tace masa

"Daddy zan bata da Anty Fiddausi tana fadawa mama sirrina"

Kallanta yayi yana cewa

"Oh no indai hakan ne taci Amanar Falaq Aziz"

"Yes Daddy,Kuma tace tana bayana amma tana maganar sirrina da mama i heard them not once"

Mama data juyo tana harararta ta kalla tana qara shige masa tace

"Did you just see that Daddy?
Jira take kayi tafiya zata dakeni for sure akan na fada gaskia"

"No Falaq bakinki ne is to talkative shiyas Mama ke dukansa so ki dena kiga bazata dakeki ba"
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070
Chapter 41 · 0% Book details