← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 120

Sashe 71

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Are kidding me?
Meya hada aurena dana jannah da duk abinda kike magana?
To hell with his daughter,
Idanma mutuwa zatai i dont care
I don't give a damn
Ta mutu kawai shima ya mutu amma bazan taba bari wani yama sake furta maganar auren Jan dita ba batateda na dauki matakin illatasaba"

Dad Zaunawa yayi Ahankali har lokacin baice komaiba sbd harga Allah baisan tayaya zai bullowa lamarinba sbd AZIZ ya janyo musu matsalarda bata hakan yaso bullowa Ammar dinba.

Anny ce ta sake bude baki ganin koina jikin Ammar din rawa yake yana neman loosing control ya fara musu fashe fashen kaya karshe ma zai iya raunana kansa ya raunana wani tace

"Ammar pls calm down"

Batada zabin daya wuce shirya masa karyan da zata fiddasu dan haka kallan dad tayi kafin ta kalli Maheer dayake nufar Ammar din da tausarsa tayi saurin tare Maheer din kada yaje Ammar ya rasa control nasa ya illatasa dan haka tace

"Ammar abinda yake faruwa shine
Falaq Aziz nada ciwon da mutuwa zatai she only hv 3 month to live,
Tana tsananin son Jan as her mum
Kuma ka sani akwai kauna tsakaninsu sosai,
Daddynta na son bata farin ciki a kwanakin da suka rage mata so ya roka abasa auren jannah for only 3 month shikuma zai bamu dukkanin abinda ya mallaka in return......

"What¿" Ammar ya fada cikin tsananin mamaki da sabon tashin hankali sbd zancen kadai neman sake juyar masa da kai yakeyi.

Dad kuwa da sauri ya kalli Anny kansa na sarawa da tsananin ciwo shima jin abinda take fada...

Magana zaiyi Maheer ya bude baki a hankali yace

"Dad a tafi a hakan atlast idan ya aminta zamu samu ayi auren daga baya asan yanda zaayi"

Maheer dinne ya karbi zancen d cewa

"Ka sani muna cikin financial crisis hakama shine biggest catch namu da muka sani zai iya tadomu,
And atlast tinda anzama kamar family bazamu iya taimaka masaba akan yarsa?
Auren wata 3 fa?
Idan harmu dukanmu zamu iya yadda da hakan meyasa kai bazaka iyaba,
Babu wani soyayyar dayake tsakaninsu,
Kana tinanin akwai abinda zai girgiza soyayyar da jannah take maka?
Ita kanta zatai ne sbd falaq,
Gabaki daya assets dinsa zai bayar a matsayin auren kankanin lokaci,
Bazaka iya sacrificing wata uku naka ga familynka ba?
Karka manta mun taso da taru a tinani daya da tabbatarda ci gabanmu,
Meya canza Ammar?
Kana tinanin har abada zamu taba son wani ya auri jannah akanka?
Wlh muna kaunarka fiyeda yanda kake tinani ta yanda ka dauka hakan da zamuyi babu zabi ne kuka bamu yadda da hakan bane saida muka tabbatarda lokaci muka bawa auren zamu dawo da ita gareka."

Ganin zancen yafara shigar Ammar ya saka Dad dago idanuwansa da suka sauya ya kalli Ammar yace

"Ammar indai nine na haifi Jannah insha Allah nai maka alkawarin aure maka ita indai har zaka iya hakura a yanzu dan samarwa kanmu mafitar abinda mukeso,
Ban basa aurenta dan ta zauna dashi har abada ba na basa ne sbd ita kanta Jannah din ta samu abinda takeso a can amma insha Allah zata dawo a lokacin ne zan daura muku aure da hannuna,
Ka sani Ammar ina sonka sbd kai jinin Zayneb ne da har abada jinin Zeynab yafi komai dana mallaka daraja amma ayau ina rokon ka bamu lokaci kankanin a cikin soyayyar da kakewa Jannah"

Wasu irin hawayen masu tsananin radadi da baisan suna fito masa bane suka fara gangarowa Ammar din kafafunsa na wata irin rawa zuciyarsa na neman bugawa ya zube gurin jikinsa na rawa ya fara girgiza kai yana cewa

"No,no i can't"
Har abada bazan iya kallan jannah a hannun wani ba koda na minti dayane bare wata uku,
Bazan iyaba dad
Mutuwa zanyi,
Zuciyata bugawa zatai,
Dad bazan iya ba,
Mutuwa zanyi"

Kirjinsa ya dafe yana masa wani irin tsananin radadi da azaba kansa na neman juye masa yana jijjiga yafara daga murya sosai yana cewa bazai iyaba mutuwa zaiyi,
Indai aka aurawa jannah wani zai iya kashesa ya rabasa da duniya koma waye.

Anny na ganin hakan ta kalli su Dad tace

"He's looking it,inaga ai masa Allura ya samu bacci idan ya tashi kansa ya sake zaifi fahimtar abinda ake nufi amma a yanzu yana rikicewa komai zai dagule"

Kallanta dad yayi yace tai masa alluran kawai sbd yana rikicewan nan raunana kansa zaiyi wanda ya tsani ganinsa a cikin yanayin da zai raunana kansa dan harga Allah tin daga zuciyarsa kaunar Ammar take amma kuka bazai iyawa jannah auren da bataso ba wanda hakan zai iya kawo matsala a cikinsu dan daman tin farko sbd basason matsala ta shigo tsakaninsu sbd tsananin kaunar da sukewa juna basa wani son auren zumucin amma kuma sbd dagewan Mimi da ganin yanda Jannah din take tsananin son Ammar da yanda yake mutuwar sonta suka kaunace auren harya sabu da jin bazai iya kaita aure wani gurin ba bayan na nan cikin gida.

Kafin suyi wani yunkuri Ammar din ya fara haukace musu da sauri Maheer ya rungumesa yana kokarin calming dinsa amma ina dan haka dole Anny tai masa allurar da baisan da itaba kuma batareda sanin kowa ba high dose ta basa dan haka bedroom dinsa Maheer yakaisa y kwantR tareda rufesa ya daidaita masa ac bayan ya sauya masa kayansa zuwa na bacci marasa nauyi dan haka baccin kwanciyar hankali suka sakasa.

Anny jin tai hankalinta ya kwanta dan daga Mimi har Ammar din insha Allah sai gama daurin aure zasu tashi dan haka itace ta karbi ragamar hidiman bikin cikeda farin ciki.

Dad da wuri ya shige zuciyarsa na shiga wani irin rashin nutsuwa haka kawai ga jininsa daya dan hau dan haka yasha magani ya shige.

Kiran Alh saad ne ya shigo wayarsa suka gaisa ya bayyanar masa da matsayinsa na wakilin AZIZ suka dan tattauna akan goben kafin sukai sallama.

Maheer ma damuwar yakejin ya shiga haka kawai sbd jin kaman abind yake faruwa bai kamata ba amma Anny ta dage ta sakasa dawowa da mood dinsa daidai.

********Washe gari tinda safe Su Baba alhassan da Alh Ahmed da Alh saad suka taho gidan suka sake gabatar da kansu sukai neman aure yanda ya kamata tareda kudin neman Aure ten mil suka baro sai kuma sun hade gurin daurin auren karfe goma sha biyu na ranar.

Saleem daya kasa yadda da cewan Jannah AZIZ takeso saida yayi magana da ita ya tabbatarda da hakan dan haka shima bai wani daga hankalinsa ba duk da su dad basu bude masa zancen sosaiba dan haka koda akace damuwa ta saka su Mimi fitowa sai bai takura Mimin ba tinda ya shiga ya sameta tana bacci hankali kwance hakama Ammar din dan haka kai tsaye cikin farin ciki yahau shirin daurin auren mutane biyu dayake tsananin kauna.

Jannah kasa Fitowa tayi duk da gidan akwai mutane rufe kanta tayi a daki tana kasa fitowa duk da batasan meyake faruwaba dan taqi barin kowa ya shigo mata hakama ta kashe wayarta hakama jamaar bikin basusan shaanin da ake cikinsaba hidima kawai Ake Anny kaman zata tashi sama sbd farin ciki.

Yau ranar aurenta da Ammar amma ayau din zata rasa farin cikin zuciyarta har abada dan haka zuciyarta take cikin wani irin yanayi na sanyi da rashin kuzari ko kadan dan hakanne ta kasa barin kowa ya ganta har lokacin daurin auren yayi.

Cikin shegun motocin dake Zaaden masu tsadar gaske da tarin securities su Dad suka fito zuwa daurin auren harda Daddy Mahmoud wanda yake cikin wasu shegun kaya masu tsadar gaske da sandarsa dayake takawa ahankali dan ya fara takawa.

Kowannensu asalin dukiyace a jikinsu tin daga manyan kayan dake jikinsu zuwa agogayensu da shoes
Luxuries tako ina kawai.

Koda suka isa masallacin da zaa dauka gabaki daya anguwar koina securities da jamian tsaro an cika.

Su Alh saad already sun iso suma dan haka AZIZ din ake jira wanda very late ya iso.

A cikin wata black RR ya iso gurin wadda ta saka aka san da shine din ya iso.

Sayd ne ya fara fitowa da fahad wanda ya baifi mintina arbain da sauka Nigeria dinba.
#MAMUH
#TWO PSYCHOS
#CRAZY Lovers
#limbas
#zaadens

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
58
Dad da Maheer dake jin matsuwar a daura auren suna jin sanarwan isowansa ajiyar zuciya suka sauke a tare cikin sirri sunajin nauyin kirjinsu na raguwa sbd maganace kadai basuyi da junansu ba amma babu wanda babu shakkar Zuwan AZIZ LIMBA a zuciyarsa sbd a yanda yake baa gane alkiblansa zai iya qin zuwa ko cewa bai karba aurenba wanda a daidai wannan lokacin idan yayi hakan ayau sun gama saukowa daga zaadens a idon mutane sun koma dezaans kila dan haka duk murmushi da farin cikin dayake bayyane a fuskokinsu fargaba da rashin nutsuwa ne a fuskokinsu saida sukaji isowansa suka saukin abinda ya toshe kirjinsu.

Fitowa yayi mota sanye da wani black tsadaddiyar luxury cashmere datai masa wani irin kyau da hula a kansa qamshinsa kadai me kirari ya shaqa take ya sauya kirarinsa yana qarawa da me qamshin alkhairi da babu irinsa.

Securities ne suke sake bawa gurin tsaro yana wucewa kai tsaye ciki Sayd na gefensa da Securities a bayansu sai fahad dayake gabansu ya basa kariya ta gaban.

Suna shiga masallacin take aka fara kokarim daura auren sbd ana kokarin gota lokacin da akace.

Dakatar daurin auren AZIZ din yayi lokacin da yake kokarin qarasowa har gurinsu Baba alhassan dake kokarin gabatar da komai.

Wani irin kallo Maheer ya dago da sauri yanawa AZIZ din zuciyarsa na bugawa da karfi da kuma mamakin menene.

Dad kuwa numfashi ya sauke ahankali yana dan lumshe idanuwansa yana jiran jin abinda AZIZ zai fada wanda zai iya sakasa samun Mummunan shock a gurin komaima zai iya faruwa dan haka kasa dagowa tayi yana jiran jin wani abin.
Chapter 71 · 0% Book details