Sashe 16
Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta bangaren business dinsu da alhaji saad kuwa komai Allah ya saka musu albarka sosai ake tafiye tafiye kudi na shigowa sosai kuma ganin ABDULAZIZ din yanada wani irin farin jinin aiki ya sakasa fara sakasa a aikin ta can bangaren lagos sai ya zama ABDULAZIZ din baya abuja baya lagos ga karatu da kuma dayan business dinsa dayake habbaka sai ya zama busy sosai bai wani cika zuwa gida ba sai akai akai sedai kullum yana cikin waya dasu dan bai taba bacci ba batareda yayi waya da Ummitah ba wadda itama duk tsananin bacci batayinsa sai lokacin kiransa yayi sunyi waya take bacci.
*****lokacin yaja karatunsa yana gap da kammaluwa hakama zuwa lokacin kudi sun fara zauna masa sbd tako ina kudi shigosa sukeyi business dinsa na tafiya hakama na gurinsu saad na tafiya.
A shekaran daya kammala degree dinsa a lokacin yafara fita qasar waje tareda saad akan harkan business dinsu dayayi wani irin habbaka hakama ga nasa na daban na harkan computers da aircraft dinsa dayake daukaka sosai kaman ma saurayin matashi ba dan kudi kam suna zaunuwa.
Italy suka fara zuwa suka share kusan watanni kafin suka dawo shi ya sauka a ghana shi kuma saad ya wuce abuja.
A ghana saida share tsawon lokaci kafin ya dawo lagos tukuna ya wuce abuja acan yayi service dinsa.
Da yana service ne yake yawan zuwa ganinsu Ummitah daya sauya rayuwarsu a garin suka koma tamkar taurarin dake haske garin.
A garin ABDULAZIZ LIMBA shine tamkar gatansu kuma sarkinsu sbd yansa yake taimakawa kowa yake musu alkhairi dan ya riga ya saba duk abinda zaiyi aike me yawa yake aikowa sbd a rabawa mutane harma da maigari ABDULAZIZ ya zamar masa tamkar wani ginshikin dayake jingina akansa.
Alkhairi yake musu sosai sbd kowa na kaunar Ummitansa duk inda ta wuce kowa sonta yake hakan yasa babu abinda bazai iyawa yan garin ba,
Ya gina musu islamiya da masallaci me kyau hakama gidansu mama ya koma wani tauraro a garin da babu abinda suka rasa a kauyen.
Yana gama service babu bata lokaci ya jona degree na biyu a italy sbd business dinsu dayake tafiya acan sosai dan haka ya tattara yabar kasar ya tafiyarsa.
Yaso dawo dasu Mama abuja sbd karatun Ummitah amma sbd baya zaune a qasar yasa yafi samun nutsuwa dasu zauna acan gida cikin family da tsaro kafin yayi settling tukuna dan ko ya dawo dasu baida nutsuwa tinda bayanan hakama suma basu saba da nan dinba zasu shiga kadaici da damuwa dan haka tinda shima baida takamaimai inda yake zaune saiya zabi su zauna acan din kafin ya zauna guri daya.
Mashin ya siya aka ajiye na kai Ummitah makaranta me kyau kawai hakama babu abin jin dadin dabai zuba musu ba.
Acan italy yana karatu ne tareda business hankali kwance cikin nutsuwa da ilimi da wayewan data shigesa sedai bai sauyaba daga mara son hulda da mutane sosai da hayaniya yana nan ABDULAZIZ AYOUB LIMBA dinsa HAMMAN UMMITAH.
Bayan halinda da dabiunsa da basu sauya ba babu abinda bai sauyaba daga garesa,
Ya koma wani irin kakkarfan namiji me ji da sabon jini da farin jini da kwarjini me karfin gaske tareda kudi dasuke zauna masa hakama matashin da kyau da nutsuwansa suke sakawa mutane kwarjinsa sosai.
A rayuwarsa bayan bautawa ubangijinsa idan gari ya waye geamin ko jogging yake fita kowace safiya
Daga can kuma yana dawowa yake wanka yayi breakfast ya fice karatu daga can yana dawowa gurin aikinsa yake wucewa,
Wani lokacin kuma aikin yake fara fita kafin ya tafi makaranta daga baya.
4 years ya share a italy ya gama karatunsa tini ya fara aiki me kyau sbd iliminsa dayake fin na abokan karatunsa ko yaushe dan haka yana gamawa ya samu aiki kusan guri hudu masu kyau da girma akaso daukansa aiki amma karshe ya fara aiki a wani babban kamfanin qera jiragen sama kuma a babban matsayin daya sakasa mallakan gidan kansa da motan hawa har biyu.
A farkon fara aikinsa kwata kwata babu wata dama ko kadan ta barin kasar yayi tafiya dan haka duk yanda yaso tafiya gida bai samu damar hakan ba seda maman da kanta ta karfafesa akan babu damuwar komai yayi zamansa tinda suma suna lafiya ba matsala ko damuwar komai.
Ummitah data zama yar budurwa itama karfafasa tayi akan ya vari saiya samu time tinda idan yazo zai daukesu ne yabar qasar dasu gabaki dayansu.
Hakan ya basa qwarin gwiwa da kwanciyan hankali ya nutsu akan aikinsa.
Baai wata shida da fara aikinsa ba sukai tafiyan karatun wani program na wani aircraft dazasu hada a kamfaninsa dayake kokarin budewa shima zuwa Sidney.
Tinda yayi tafiyar su Mama suka dena samunsa shima kwata kwata ya dena samunsu sbd wayarsu da aka sace daga zuwa bikin wata yar gidan da aka aurar aka kai binni sukaje kai amarya.
Sun siya wata wayar amma tsautsayi da kaddara suka hana Ummitah haddace numbernsa sbd kullum cikin yawon kasashe yake numbernsa ba daya bace dan haka bata haddace numbernsa ta Sidney dinba sabanin sauran numbers nasa data haddace dan haka communicating ya yanke a tsakaninsu kwata kwata.
Sun shiga damuwa da tsoro sosai wanda ya saka Ummitah komawa wata sanyi sanyi hakama maman.
Amma dayake sunsan yace yana dawowa zai taho ya tafi dasu sai suka ringa saka idon zuwansa kawai ba waya,
Duk yan gari sunsan wannan karan ABDULAZIZ LIMBA na zuwa tafiya zaiyi da mamansa da Ummitansa dan haka aketa kewansu tin basu tafi ba.
Ummitah karatunta yayi nisa hartana ss1 suna kokarin shiga ss2 amma babu labarin HAMMANTA,
Tin suna saka ran zuwansa har suka cire rai suka ringa adduar idan ba wani abin ne ya samesaba.
Ahankali rayuwa tafara sauya musu gatansu ya fara ragewa sbd duk abinda ya tanadar musu ya qare sun fara shiga damuwa da matsin rayuwa.
Halinda suke ciki ba shine damuwa da quncinsu ba rashin jinsa da ganinsa dan haka suka sake dagewa da addua ba dare ba rana harma da azumi Allah kadai suke roqon ya saka yana lafiya Allah yasa wannan shirun nasarace tafe garesu.
*******Babban tashin hankalin daya riski rayuwarsu shine bayyanar dangin mahaifinsu ABDULAZIZ din garin da babbar maganar data saka mama kusan somewa saida aka riqeta.
Ummitah suke so a basu sbd sun samu labarin ABDULAZIZ yayi kudi zuwa ma zaiyi ya tafi dasu bazaa sake jin labarinsu ba dan haka basu Aminta da hakan ba Aure zasuwa Ummitah anan ta yanda bazai taba barin nan dinba har abada.
Ba mama kadai ba ko inna tana gama jin zancen kuka ta fasa tana rokon ALLAH ya kawo musu ABDULAZIZ kafin a lalata rayuwar Ummitah da suka daukan masa alkawari da rayukansu akan bazasu taba barin rayuwarta ta lalaceba.
Su kawu kuwa acikin kankanin lokaci suka bude wuta akan hakan wanda magana har a gaban me gari dayaqi yadda da maganarsu shima.
Mama kuka ta zube a gabansu tana rokonsu akan kada suyi hakan su bari ABDULAZIZ ya dawo qasar.
Kallanta kawu shehu yayi yanajin wani baqin ciki na taso masa sbd jin wato ma ABDULAZIZ din baya qasar sbd samun daukaka gasunan yaransu sun danqare a kauye basa komai sai aure aure suna tara yara da qananun shekaru.
Tsokin baqin ciki kawu shehun ya sake yana kallan kawu isyaku da shima baqin cikin yake yace
"Wlh bazamu jirasa ba tinda ba shine ubanmu ba,aure kuma wlh babu wanda ya isa ya hanamu yimata aure tinda duka sa'anninta gasunan anmusu aure harda haihuwa wasu ma
Duk kunbi kun mayarda yarinya sakarta shiyasa zaizo ya dauketa yakai qasar turawa ta qarasa lalacewa ko?
To idan shi yafi karfinmu baimasan damu ba to ita kafin tafi karfin namu zamu nuna matsayinmu kanta"
Cikin kuka mama ta dago jajayen idanuwanta zatai magana kawu shehun ya katseta a kufule da cewa
"Ke wlh babu abinda zamuji
Ke wlh ma vazata qara sati a gida ba nan da kwana uku idan bata fidda miji ba aure zamu daura mata da 'dan uwanta 'dan wajen isyaku jibi a daura musu aure mu tafi da ita ta tare ai shikenan idan ya dawo ya ringa kai mata ziyara acan da duk ma abinda ze kai mata ya ringa kai mata acan"
Hawaye masu tsananin zafi ne suka gangarowa mama sbd a bayyane tsananin kwadayi da baqin ciki da hassada ce zata sakasu yin abinda sukeson yi.
Qara mama ta sakasu amma karshe sune aka bawa gaskia sbd sune dangin uba dan haka hankalin mama dana maigari ya tashi sbd bazasu taba bari a iya lalata rayuwar Ummitah ba sbd itace rayuwar ABDULAZIZ kuma kuzarinsa na nan duniya.
#MAMUH
#LIMBAS
#BROTHERS LOVE
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070