Sashe 85
Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
***********
Shima ruwa ya dauka yasha a natse ya miqe yabar gurin batareda ya qarasa cin abincin ba.
Fiddausi dataga yanayin da jannah ta wuce a cikinsa dakinta ta bita ta zauna tana tayata fira tana sake gyara mata dakin tin tana kasa cewa komai har ta biyewa Fiddausi din suna fira tana bata labarin kuruciyan falaq da yanda suke fama da ita a lokacin idan daddynta yayi tafiya ta gane bayanan.
Dadin firar jannah takeji sosai zuciyarta na sanyi da jin yanda falaq ta taso wanda a cikin firar ta fahimci kila a gurin haihuwan falaq mamanta ta rasa ranta sbd a kaf labarin babu inda aka fadi asalin mamanta,Fiddausin ce kenan ta reneta tin tana jaririyarta itada mama dan haka kauna da jin falaq din a zuciyarta ya qaru taji zata iya daure komai sbd bawa falaq din kauna irin ta uwa data rasa duk da tariga tasan har abada babu me iya hawa matsayin da mahaifinta ya riga ya cike na uba dana uwa dan kuwa koda uwartata zata dawo duniya to bazata iya cike gurbin daya riga yacikeba sedai kwatantawa sbd ita kanta falaq din babu wani dan adam dayake duniya da zata iya bawa matsayin data bawa mahaifinta ba sbd ba qaramin tsananin kauna take masa ba dan duk da tana yarinya babu abinda takejin bazata iyaba sbd daddynta shiyasa taiwa Ammar tsanar gaske duk da bata gama sanin tsanar me take masa dinba.
Har magrib Fiddausi na dakinta tana tayata fira da kalle kallen da suke a ipad ga kuma qatuwar flat screen tv datake dakin nata dayakeda girma sosai.
Falaq na dawowa kai tsaye dakin ta nufa tana ganinsu ko uniform na islamiyya din bata cireba ta xauna cikinsu jannah na tayata cire hijab din jikinta dayake qamshi me dadi duk da anyo yawon makaranta amma sbd tsadan turarenta da ake siya mata yasaka komai na jikinta qamshin yakeyi me sanyi.
Hularta ta jannah ta zame mata sbd tasha iska tana cewa
"Falaq kodai zaki cire uniform din kiji dadi?"
Girgiza kai tayi tana shan ruwan da Fiddausi ta miqa mata cikeda kulawa.
Mama data jisu shiru ta dauka basa nan sai bayan magrib suka fito dukansu kowannensu da walwala akan fuskansa.
Kallan falaq tai da uniform a jikinta tace
"Me kikeyi da uniform a jikinki har yanzu falaq?
Oh ni Sakina wannan yarinya anyi shiryayya"
Murmushi jannah tai tana cewa
"Ko data dawo mama ta gaji ne shine ta huta sai yanzu zata sauya"
Kallan jannah mama tai tana cewa
"Allah na gode maka,kema yanzu jannah sahun AZIZ zaki bi kuna biye mata komai tayi bata laifi daidai ne ko??
Murmushi jannah din ta sake yi tana kallan falaq tace
"Je ki kicire uniform din kilama sunata damunki"
Dariya mama tayi tana kallan Fiddausi kaunar jannah na sake cikata tace
"To ai shikenan saiku bada himmar qarasa lalatata kunyiwa mijinta bayani daga baya"
Falaq na jin hakan ta dawo da sauri tana cewa
"Mama Jan tace na dena shiga dakin Daddy tinda safe ba kyau sai nayi aure dakin mijina kawai zan ringa shiga karna sake shiga na kowane namiji sai nasa"
Mama cikeda mamakin falaq din tace
"To wannan nasihar datai miki wayace miki ana fada?baa fadawa kowa gaskia ta fada miki"
Basusan da isowansa ba sai zancensa sukaji wanda ya sakasu yin tsit Fiddausi na hadiye hadiyarta da sauri tana kama kanta.
"Wane mara hankalin ne ya sakata fadawa yarinya hakan?
Fuskansa a daure take sosai bacin ransa na bayyana a cikin sautinsa dayake fita a natse ya kalli jannah din wadda ta kasa dagowa
Yace
"Wane kalan tarbiya ne kikazo dashi?
So nawa zan fada miki tarbiyanku dana mutane ba daya bane,
Kinsan inda maganganunki zasu kai tinaninta?
Meya hadata da maganar zuwa dakin miji a wannan shekarun?
Ke tin kina yarinya qarama aka nuna miki xuwa dakin mijin ne or wat??
Like seriously??
Mama ce ta katsesa da cewa
"AZIZ me kake fada haka?
Tana bata tinani me kyau ne ai sbd tintini ya kamata ta dena shiga dakinka anyhow,
Ta girma ya kamata tafara sanin ta girma hakama tin a yanzu ne ya kamata tasan baa shiga dakin kowane namiji saina mijinta idan akai mata aure shima"
Hawayen da jannah ta kasa barin su saukone ta hadiye su ta maqoshinta suka wuce mata da wani irin daci ta kasa dagowa.
Shi kuwa maman ya kalla yace
"Mama duka wannan zancen ba yanxu ne lokacin yinsu ba,
Tana buqatan kiyaye kalan namu tarbiyan da dabiun dasu basuda shi banason zance kowane iri yana shiga kunnen Falaq din"
Falaq jannah din ta zubawa ido itama nata idanuwan na cikowa da hawaye ta miqe ta koma gurinta tana rungumeta ta dago ta kalli daddyn nata tana bata fuska.
Mama ma tausayin Jannah din taji duk ya rufeta amma bata ji zafin AZIZ din sosaiba sbd ganin take bai saba da kowa na saka masa hannu ko baki bane a tarbiyan yarsa bayan ita da sayd dasu kadai ne suke masa discipline nata.
Fiddausi silalewa tai tabar palon jiki a mace Sayd ma dayake tare dashi shiru yayi sbd ba hurumin shigar kowa bane bayan maman sai kuma falaq da itama take iya sakasa da hanasa.
Cikin karfin hali jannah ta dago tana hadiye damuwa da radadin zuciyanta tana nunawa mama ba komai bayan barinsa gurin.
Falaq zuwa tai ta cire uniform dinta taqi sake fitowa dakinta har lokacin cin abinci yayi taqi fitowa karshema rufe dakinta tayi.
Tin Fiddausi na daukan abin wasa har taga dai da gaske take take hadda su kuka sosai dan haka ta fito ta sanarwa su jannah da mama.
Jannah ce ta nufi dakin ta ringa Knocking tana kiran sunanta cikin kulawa da rarrashi.
Qin budewa tai wanda hankalinsu ya fara tashi sbd kuka takeyi sosai taqi magana.
Jannah hankalinta mugun tashi yayi sbd tana gudun AZIZ din yaji ta sake wani laifin dan haka ta ringa rokon falaq din akan ta bude amma sam taqi.
Mama tasan zaayi hakan daman Falaq din na wannan sakarcin har sai Daddyn yamata abinda takeso idan ba hakan ba haka zata qi fitowa ta dagawa kowa hankali.
Basu san abinda yake faruwa ba sai da ya dawo kusan 10 na dare ya tararda Fiddausi da jannah din tsuru cikin damuwa.
Ko kallan inda suke baiyiba ya wuce hanyarsa yana duba time.
Sayd ne ya kalli Fiddausi yace
"Lafiya dai?akwai abinda yake faruwa ne?
Hanyar da AY yabi Fiddausi ta saci kalla tace
"Falaq ce tin bayan magrib tana daki ta rufe tanata kuka sosai kuma tin dazu ma munji shir..........
Cak din da AZIZ din ya tsaya cak sbd maganarta tsaf a kunnensa ta saka ya saka Fiddausi kasa qarasawa tana sauke kanta qasa.
Shi kansa Sayd din da sauri ya juya ya kalla ko AZIZ din ya shige ya gansa yana sauya hanya zuwa bedroom din Falaq wanda jannah ke can tsaye tin dazu idanuwanta duk sunyi ciki ita kanta tana cikin tsananin buqatan me kulawan da ita tai kalan tausayi jikin yayi tsananin sanyi sbd tasan itace zata hadiyi baqin cikin akan wannan lamarin.
Jin qamshinsa da taku a bayanta ya sakata janyewa gefe tana juyowa taga shi dinne kuwa fuskansa babu sauki ko kadan.
Tsayuwa yayi a bakin kofar ya ambaci sunan falaq da muryansa kai tsaye.
Kafin ya sake kiran falaq din juyowa yayi cikin zafi ya kalli jannah din ransa na quna yace
"Babu abinda kika daidai ne a rayuwanki ke??
Idan ta rufe kanta kusan awa biyar me amfaninki da bazaku nema mutane ku fada musuba?
Cikin tsananin sanyi da mutuwan jikinta datake jin zazzabi sbd wahalar tsayuwa da buga kofa ta bude baki a sanyaye tace
"I'm sorry"
Kaman tafasashen ruwa haka yaji muryanta datake bayyanarda itama ciwone a jikinta na sauka a zuciyarsa,
Da karfin gaske ya buga kofan yai wa falaq din kira daya daya saka falaq din mugun firgita sbd bata taba jinsa hakan ba.
Ita kanta Jannah sarawa kanta yayi sbd faduwan gaba ta dafa bango.
Acan ciki kuwa falaq ciwonta ne ma ya tashi jin tai kaman numfashi na gagara shiga cikinta,
Bugun zuciyarta tsananta yayi sosai har tana jin azabarsa ta dafe kirjinta tana jin abinda bata taba jiba.
Saukowa tai daga gadonta bata gani sosai jiri na dibanta tana son isa kofar sedai ko taku uku bataiba ta zube a tsakiyar dakin.
Jin faduwanta a qasa ya sakasa juyawa da sauri yace Sayd ya kawo keys.
Da gaggawa aka kawo keys ya bude dakin
Ganinta zube qasa ya sakasa jin kansa gabaki daya ya dauki zafi da saurin gaske ya isa gareta ya dauketa cak yana sayd yayi sauri ya kira likita.
Jannah ma tashi hankalinta yayi taji gaba daya ta rasa kuzarin jikinta ta rabe gefe tana kallan yanda falaq komai nata baya motsi.
Sayd da sauri ya fidda wayarsa yana ficewa daga dakin ya saka kiran sabuwan dr din da suka samu anan din mace da namiji ta bangaren ciwon falaq kawai.
Ganin ya rasa taimakon da zai bawa falaq din ya saka jannah zuwa bakin gadon tafara taimaka mata ganin numfashinta bai tsaya gaba dayaba sbd tayi karatun bada taimakon gaggawa a Greece sbd yanayin ciwonta hakama Ammar ya koyar da ita abubuwa da dama sbd koda wani abin zai sameta ba kowa dan basa wasa da lafiyanta sam.
Yanda takeyiwa falaq dinne cikin taka tsantsan da kulawa ya sakasa kallanta yana jiran jin wani abu daga gareta sbd ganin falaq din tana dan kokarin daidaituwa a yanda kirjinta ke wani irin ja.
Baa dauki lokaci irin sosai dinnanba dr Sameera ta iso tareda wata nurce.