← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 120

Sashe 26

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*************
A cikin qananin lokaci suka ji suna samun nutsuwa da iyalan Alh saad wanda shima ya shigo sun gaisa har so biyu ya kuma cewa anty maryam da kanta takai Ummitah asibitin taga doctor kafin dawowan ABDULAZIZ.

Da safe suke shirin Anty maryam din tazo suje asibiti dan haka a ranar a dakin mijinta ta kwana sbd Shine zai tasheta tinda asuba sufara shiri bare kuma daman Ummitan da kanta ta tafiyarta gurinsa itama mama bata hanaba tinda kila idan ABDULAZIZ din ya dawo bazai barsu guri daya ba sai Ummitah ta haihu ta koma masa yanda yake ganin ya kamata ta koman.

Irin tsananin Asalin son da Sayyid kewa Ummitah kusan a duniyarta ABDULAZIZ ne kadai nasa ya fi nasa sbd So me tsaftar dayake mata daga Allah ne shi ya halitta masa shi a zuciyarsa,

Kwana yayi a zaune yana kulawa da ita tareda tarairayanta yana jin kaman ya rabata da cikin jikinta taji sauki hakama shi kansa ya shirya bazata sake haihuwa yanzu ba tinda ciwo da wahala cikin yake sata hakama yana tsoron wani abin ya sameta koda agurin haihuwa ne bare ya sani ko Hammanta ABDULAZIZ bazai bari ta sake haihuwa anan kusa ba idanma bai rabasu ba akan sai sun gama karatun dayace zasuyi.

Karfe tara suka fito a shirye tsaf suka nufi dakin mama wadda tinda tai asuba bata koma ba tana zaune tana jiran lokacin zuwan nasu asibitin yayi.

Dining suka nufa wanda suka ga ancika sa sosai ayau din fiyeda kullum hakama abincin dayake kai a yau an samu sauyinsa.

Mama ce ta zauna Sayyid kuwa Ummitah yake kokarin taimakawa ta zauna
Ahankali wani irin qamshi me sanyi ya fara shiga hancinsu mai nutsuwa,

Ahankali Ummitah ta dakata daga zaunawan da zatai tana dago fararen idanuwanta dasuke sak da nasa ta waiwayo cikin sanyi hancinta da gurin suna sake gauraya da qamshinsa.

Sayyid ma qamshin ya sanyasa sakin hannun Ummitan Ahankali yana juyowa sbd Tin ranar farkon haduwarsa da Hamman ya riqe qamshinsa sbd Kaunarsa da Allah ya dasa masa arai shima sbd Ummitah.

Inda suke kalla Mama ta juya ta kalla taga mene sbd ita hankalinta da hancinta basu wani bata tinanin qamshinba.

Daidai lokacin ya sako kai a natse cikin wani irin kwarjinin daya saka Sayyid sauke kansa cikeda girmamawa yana kasa qure kallansa akansa sbd ba kwarjininsa kadaiba hatta hasken fatarsa datake wani irin shining na hutu da kwanciyar hankali tareda daula datake samu ya saka kyansa yin yawa.

Ummitah ce ta qure kallanta akansa tana jin dukkanin jikinta na mutuwa wani sanyi yana sauka zuciyarta yana mamayewa,

Batada abinda yafi mata dadin kallo a rayuwarta sama da kallansa a gabanta,

Kyansa da asalin kammminsu dasuke iri daya amma shi ya sauya gaba daya komai nasa daban yake da nata sbd rayuwar da inda suke rayuwar ba dayaba,
Hasken idanuwansa zuwa dogon hancinsa ta kalla tana rokon Allah ya basa tsari da kariya daga dukkan sharrin kowace mace a duniya.

Shima ita yake kallan cikeda wata irin kewanta dake cinsa kaman cikin kansa zai kunce dan haka yana isowa hannunsa duka biyu ya bude ya rungumeta yana karanta mata adduoin tsari da kariya itada abinda yake cikinta kafin ya saketa ya saki wani Kyakkyawan murmushin daya saka sayyid kasa dena kallansa da tattausan sauti yace

"Sorry Ummitah ABDULAZIZ,
Yaya,ya jikinki?

Kafin ta amsa gurin mama ya juyo cikin kulawa da sakewa da girmamawa yace

"Barka da safiya Mama,
Yaya fama da sauyin guri?
Na sameku lfy??

Murmushin farin cikin ganinsa tayi tana cewa

"Duk lafiya kalau
Sauyin guri kuma ai munata kokarin sabawa,
Tafiyar dare kayi kenan?

Zaunawa yayi Ahankali yana cewa

"A cikin dare na iso sai ban tasheku ba tinda kun riga kuna hutawa"

Sayyid ma zaunawa yayi yana cewa

"Barka da dawowa"

Kallansa yayi cikin kulawa da sakar masa fuska sbd ya sake yace

"Thank you,yaya kaima kanata fama da kadaici right?

Gyada kai Sayyid yayi yana kokarin sakewa da hamman.

Ummitah na gefensa fuskanta cikeda da murmushi me kyau da nutsuwar data kwana biyu bata iyawa sbd yanayinta.

Breakfast suka fara cikin kokarin sakewa dasu dukkaninsu sbd sayyid ya sake dashi tinda tsakaninsa da mama da Ummitah babu wani kamewa ko rashin sakewa.

Bazai taba tina yaushe Zuciyarsa ta samu asalin farin ciki irin wanda yake cikinsa a yanzuba sbd kasancewarsa dawowa rayuwa a guri daya da Ummitah wadda babu ranarda zasu sake rabuwar gurin rayuwa daban daban har abada sedai rabuwar kwanaki na tafiya dayake yawan yi sun hadu kenan sai mutuwa insha Allah,

Kallan Sayyid dake cin abinci yayi a natse yana kallan Ummitah yaji zuciyarsa na sake karban Sayyid din cikeda Kauna sbd Aurensa dayake kan Ummitah bazai rabasa da ita ba tinda shi kansa mahaifinsa a hannunsa ya basa amanarsa kuma ya karba har Abada insha Allah.

Yanzu ne yakejin Nutsuwa da godewa Allah da hakan dan Sayyid dinne kadai Ummitah zata aura suci gaba da zama a taredashi,

Ahankali ya bude bakinsa cikin sauti me nutsuwa da rashin sauti yace

"Thank you Sayyid"

Kallansa sukai dukkaninsu dukda ba sauti yayi maganar cikin turancinsa dayake kashe Sayyid.

Mama ce kadai da batasan wani thank you ba bata kallesa ba.

Bai wani ci abincin ba hankalinsa na kan Ummitah wadda ita kuma idan yana tareda ita take cin abincin dama bata saba cin ba sbd jin take komai nata ya bude.

Mama tasan daman indai yana tareda Ummitah ba wani abincin kirki yake ci ba dan haka bayan Ummitan ta gama sai ta kallesa cikin kulawa tace shima yaci abincin.

Tea da chips mara maiqo yaci yana gamawa gaba dayansu suka miqe suka bar dining din.

A shirye yake sbd yasan da kai Ummitah asibitin dan haka ma ya fito da wuri da sai yakai guraren 11 bai fitoba.

Key din mota da wayarsa ya fito dasu a hannunsa sai tsadaddiyar Hular fcap ta fendi daya sako ya fito.

Daga shi sai Ummitah din suka fita sai sayyid mama a gida suka barta yace ta koma bacci ta huta.

Shine yake driving a hankali Sayyid na zaune a gaba sai Ummitah din dake baya tana kallan garin cikeda shaawa da burgewa.

Sayyid dayake yana fitowa sosai suna tafiya gurare daman can sai baya wani kalle kalle sosai sbd ya saba ganin ire iren hakan.

Wani babban private clinic me tsada sosai yakaita suna isa babu wani jira ko bata time a asibitin sbd kyanta akai mata registern Prenatal visit da zata ringa zuwa.

Wani Dr Ken ne ya dubata dakyau cikeda kulawa ganin Yanda ABDULAZIZ sam tsananin kaunarsa akanta bata boyuwa duk da bai saniba ko shine mijinta ko yayanta koma waye a gunta kaunarsa a bayyane take.

Scanning akai mata bayan angama diban jininta da sauran samples na aune aune da zaa mata.

Cikin kulawa da sake fuska sosai yana tayasu murna ya kalli ABDULAZIZ daya dawo dakin bayan angama Scanning din yace

"Congratulations Sir its a baby girl"

Kallan Tvn yayi Ahankali kafin ya dawo da kallansa kan Ummitan da itama shi ta kalla suka kalli Sayyid a tare wanda farin cikinsa shima yake a fili sedai a duk lokacinda ABDULAZIZ yake kusa baya zaqewa akan Ummitah dama cikinsa dayake jikinta sbd kawaici da nauyin ABDULAZIZ din.

"Thank you dr" Yafada yana karban result din suka fito yana rasa yanayin dayake ji a zuciyarsa duk da abu daya ya sani shine kome Ummitah zata haifa ya fito a cikinta,jininta zai kaunacesa kaman yanda yake tsananin kaunarta.

Sun dade a asibitin sbd formalities din da daukan time da kuma aune aunen,

Suna baro asibitin kai tsaye shopping mall ya biya dasu aka siya fruits masu yawan gaske suka wuto gida sbd bayason yayi yawo da Ummitan dan yanayinta.

Suna isowa gida barwa Sayyid ita yayi ya wuce bangarensa dan Amsa waya da kuma fitowa sallah dan time yayi na laasar sunyi azahar already acan.

Dakin Mama suka nufa sayyid da Ummitan.

Zaunawa tayi gefen mama tana dan kwantawa jikin maman tana cewa

"Mama harna dan gaji"

Murmushi mama tayi tana shafa fuskanta da kulawa tace

"Ummitan Mama Allah dai ya nunamun kin haihu lafiya dan ki samu hutawa kema"

Murmushi tayi tana dafa cikin sbd motsawa da yayi tana cewa

"Amin Mamana"

Sayyid zainawa yayi yana fadawa maman duk abinda akai dama abinda dr yace cewan mace ce

"Kai jamaa har yasan abinda zaa haifa kenan shi likitan"

Dariya sayyid yayi yana cewa

"Ba gashi mun saniba kuma nasan Shima hamman daya sani yasan 'ya zai samu irin Ummitah ba namiji ba dan bansan tayaya zai sake dashi ba amma macen ita ya saba yasan yanda zai tarairayeta kamar mamanta da haryanzu taqi sanin ta girma"

Harararsa Ummitah tayi tana sake kwantawa jikin maman tace

"Maman Ummitah kina jinsa dai ko?
Yanzu ina cewa zan fadawa hamma zai fara kama kansa amma ita mama ka renata kana fada mata hakan"

Dariya yayi yana daukan ruwan sanyin da Fiddausi ta kawo ta ajiye musu ya bude yasha yana cewa

"Mama kinji zata lauye zance na ko??

Dariya maman tayi tana cewa

"Ai ku duka indai hakan ne kun renani sam bakwa jin kunyata ko kadan"

"Mama shine dai bayaji tinda shine sirikinki nikuma ai bazanji kunyan mamana ba"

Katseta yayi da cewa

"Nima ai Maman tawa ce shiyasa banajin kunyarta"

Dariya maman take musu tana cewa

"To ya isa naji ni na hakura tinda babu wanda yakejin kunyar tawa a cikinku
Nima kuma banason aji kunyar tawa tinda maman taku ce kaman yanda kuka fad"

Bata fuska Ummitah tayi tana sake hararsa tana cewa

"Gaskia Ni mama saiyaji kunyar mamana tinda a gidansu inajin kunya sosai fa"

Dariya yake mata datake qarawa Kyakkyawan fuskansa shima kyan ganin yace

"Bafa zaki sakani jin kunyar mamana ba tinda dai nima na zama dan gaban goshinta nama kusa kamoki"

Tashi tayi daga jikin maman tana kallanta zatai magana maman ta katseta da cewa

"Kyalesa fada yake dan kiyita fitinar rashin dalili,
Banda kamarki a rayuwata kinji Ummitan mama"

Murmushin jin dadi tai tana harararsa shima dariyar yake mata.

Miqewa yayi yana ficewa sbd sallah da ake kira.
Chapter 26 · 0% Book details