← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 120

Sashe 25

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ABDULAZIZ yayi batareda yace komaiba sbd yanda yaji a zuciyarsa a duk lokacinda akace Ummitah batajin dadi wani irin nauyi da daci yakeji ya cike zuciyarsa sbd ganin kaman ya gaza ne har akai mata auren wuri daya sakata a halinda take ciki wanda bata isaba yake gani kwata kwata hakama an sauya masa tsari da burinsa gaba daya akanta dan kuwa duk gwagwarmayarsa da nemansa akanta ne sbd ita ne,

Komai dayake son ya zama a rayuwarsa sbd Ummitah ne,
Sbd ya inganta rayuwarta ya hanata shiga quncin daya taso a cikinsa,
Sbd ya bata farin ciki da gatan da kowanne da zai samu amma a lokaci daya an sauya masa komai an lalata masa rayuwarta ta hanyarda baida zabi bayan karban hakan hannu bibbiyu dan hakan nema ya karbi Sayyid tareda alqawarin inganta rayuwarsa shima kamar qanin dasuka fito ciki daya.

Numfashi me sanyi ya sauke tareda bude baki a natse yace

"Ku shirya gaba dayanku yau komai dare zaa taho a tafi daku,
Karku bari Ummitah tayi komai hakama basai kun tafi asibitin ba,
Zanyi magana da Ummitah"

Da sauri Sayyid din ya bawa Ummitah waya ta amsa ahankali tareda dorawa a kunnanta ta ambaci sunansa ahankali cikeda kewarsa datake tsananin ji da buqatansa a kusa da ita.

Jin sautin muryanta cikin sanyi daya sauka a kunnensa ya sanyasa miqewa ahankali daga inda yake zaune ya nufi bakin window din dakin ya tsaya yana sauke numfashi mara sauti zuciyarsa na sake daukan wani irin nauyi da dacin rashin kasancewansa a kusa da ita a daidai yanzu datake tsananin buqatansa.

"Ummitah" ya ambaci sunata ahankali cikeda nutsuwa da sautinda ita kadai yakewa magana ahakan sbd matsayinta rayuwarsa gaba daya daban yake da komai.

Hawayene masu dumi suka gangaro mata ta rintse idanuwanta kuka mara sauti na zuwar mata a karo na farko tace masa

"Hammah inason ka dawo dan Allah,
Hammah inason na haihu a hannunka kaman yanda aka haifeni a hannunka,
Hammah ka.......

Kasa qarasawa tayi sbd hawayen da suka tsananta mata gudu haka kawai buqatansa take a kusa da ita sbd ita kadai tasan yanda take jin cikin jikinta.

Mama da sayyid shiru sukai jikinsu na sanyi batareda kowannensu ya iya cewa komaiba saima tsinkewa da mama tayi tana ajiye aikin datakeyi batareda ta juya ta kallesu ba.

Acan bangaren shiru yayi tareda kasa cewa komai dan duk abinda zai samu a aikin daya kawosa ko shine zai qarasa sauya rayuwarsa to tabbas saiya bar qasar ya koma gida a goben nan.

Kasa cewa komai yayi ya kashe wayar bayan yace mata ok kawai dan babu me basa umarni yace ok ko yes kawai sai buqatan Ummitah kadai kaf rayuwarsa kuwa a yanzu.

Yana kashe wayar kai tsaye ticket ya kira aka siya masa ya shirya komawa gida.

Yana gamawa wayar Alh saad ya kira ya sanar dashi a samar masa driver yaje ayau din koman dare ya dauko su Ummitah shima gobe insha Allah zai dawo.

Ummitah kuwa tana miqawa Sayyid wayarsa kasa dagowa tayi ta kalli kowannensu sbd sosai takejin jikinta ba dadi.

Sayyid da maman ma jin sukai hankalinma yafi karkata ga tafiyar sbd jikin Ummitan dan haka ba wani bata lokaci suka fara bankwana da mutane shima sayyid din gida ya koma gurin iyayensa tareda Ummitah duk da batajin dadi amma hakan ya lallaba suka tafi sukai bankwana sosai kowa na tausayawa Ummitan sbd duk ta sauya ta fara kumbura sosai irin na masu cikin daya fara tsufa.

Duka kayansu Mama kyauta tayi dasu tin daga kayan sakawa har kayan amfani da komai,

Sayyid ma kusan komai nasa kyautarwa yayi sutaransa kawai ya bari suma basu fi kala biyu ba ya bari.

Ummitah kwata kwata bata cikin walwala sbd yanayinta dan haka sayyid da mama suka matsu driver ya iso su tafi sbd akai Ummitan asibiti.

Karfe uku na yamma driver ya iso da lafiyayyar motar ABDULAZIZ din aka daukesu daga garin gaba daya bayan sun rabu da yan uwa da abokan arziki ana kukan rabuwa na tafiyar da baa san ranar haduwa ba.

Sayyid Mahaifinsa har cikin ransa yakejin sanyin jikin rabuwa dansa namiji daya tal sedai kaman yanda ABDULAZIZ yayi masa alkawarin Sayyid zai zama abin alfaharinsa kuma har abada ya riga ya zama yaya kuma dan uwan Sayyid din ya saka yakejin damuwarsa bin iska.

Mama ma tayi kukan rabuwa da yan uwanta duk da batada uwa da uba a garin amma tanajin radadin rabuwa dasu.

Ummitah kuwa nauyi kirjinta yayi mata bata iya ko kukan ba sai jajir da idanuwanta sukai mata tanajin ita kam kamar har abada bazata taba dawowa ba ta tafi kenan,

Wani nauyin ta sake jin ya danne kirjinta ta dafe kirjinta ahankali tana zubawa mutanen dake musu bankwana a tsaye ido tana rasa tinanin yi.

Rufe musu kofar mota akai ta zubawa kofar gidansu idanuwanta da suke sake yin ja...

Ahankali aka tada motar aka tafiya ahankali sai alokacin taji wasu irin hawayen da batasan dasuva suna gangarowa akan fuskanta ta rintse idanuwanta ahankali tana dora hannunta akan cikinta dake motsawa da karfi.

Shiru sukai babu motsin komai a motar sai sanyin ac dayake ratsasu babu wansa zuciyarsa batai nauyiba sbd Allah ne kadai yasan rayuwar datake gaba tana jiransu.

Tafiya sukeyi sosai da gudu akan titi da lafiyayyar motar da basa jin iskar komai bare kuka karfe ko jijjigar karfe sbd lafiyar motar da tsadarta.

Qarfe 11 dare suka isa Abuja kai tsaye gidan ABDULAZIZ din aka nufa dasu wanda yake a tsare kaman bana ABDULAZIZ dinsu da suka saniba,

Dayake dukkaninsu suna cikin sanyin jiki da damuwar rabuwa da gida basu tsaya kalle kalle sosai ba Matar Alhaji Saad Anty Maryam taxo ta kawo musu mai aikin da aka tanadar musu tareda abincin da zasu ci lafiyayye sai dakunan dasuke na kowannensu da aka nuna musu.

Dakin Ummitah shine a can daban palonsa kusa da nasa Master bedroom din
Sai dakin Mama dayake dayan palon shima babba lafiyayye dana mai aiki a kusa da nata sai Dakin Sayyid lafiyayye babba da shima yake palon tareda lafiyayyen toilet aciki.

A cikin gidan babu wanda dakinsa baa zuba masa komai na jin dadi da tsarin masu kudi ba.

Sallolin dayake kansu suka fara yi kafin sukaci abinci ba bata lokaci bacci ya dauke kowannensu har Ummitah dake fama da jikinta gajiya ta sakata baccin dole ciwon na tafiyarsa.

Washe gari me aikin gidan ce Fiddausi ta tayardasu sallah dukkaninsu sbd gajiya da sanyin ac ya sakasu wani irin nannauyan bacci.

Suna gama sallah babu wanda ya fito duk da Ummitah tana dakin mama a tare suka kwana sbd sabo.

Karfe 9 na safe Fiddausi ta gama komai na breakfast da gyaran gidan taje ta sanar musu suka fito cin abinci.

Fiddausi ta kaisu har dining ta nuna musu su zauna suka zauna suna kallan gurin dayake kaman wani shagon saida gilasai da qwan lantarki sbd haske da katon madubin console dayake kallansu a gurin.

Ba wani abincin da bazasu iya ci bane doya ce da egg sauce sai Pepper meat da kunun gyada dayaji madara.

Ummitah ce kuzarinsu da yanayinsu dan haka ganin ta samu warwarewa tana cin abincin ya sakasu sakewa suma sukaci abincin cikin jin dadi da mamakin arzikin da ABDULAZIZ din yake rayuwa a cikinsa duk da bai ragesu da komaiba shiyasa basa cikin yunwa sa kwadayi ko kadan daman can.

Suna gamawa Anty maryam na isowa gidan daukesa kayan sakawarsu da aka tanada tin kafin zuwansu.

Sayyid ne kadai babu kayansa se ta saka haydar danta ya daukesa ya fita dashi dan siyyyar nasa kayan.

Ummitah ta kalla cikeda kulawa da tattalinta sbd sanin wacece Ummitah a rayuwar ABDULAZIZ yasa duk wanda yake kaunarsa to tabbas saiya kaunaci Ummitah ma sosai.

Sannu tai mata tareda wuni a gidan tana nuna musu komai tareda debe musu kewa tinda bayanan ABDULAZIZ din.

Ko aranar ABDULAZIZ bai samu isowaba dan haka dole anty maryam ta taho gidan da yaranta duka suka sake yiwa su Ummitan wuni suna debe musu kewa tareda kokarin ganin sun sake batareda nuna qyamar ganinsu yan kauye ba.

Cikin jikin Ummitah ya saka Anty maryam ringa nuna mata wata irin kauna sosai da kulawa dan hakan ne ma mama taji tana samun nutsuwa da sakewa dasu.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
20/21
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
Chapter 25 · 0% Book details