← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 120

Sashe 43

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Did you just call my daddy tsoho?
Daddyna shine yafi duk mazan dake koina kyau da komaima ko kyansa ma ke bakiyiba ai"

Murmushin takaici jannah ta sake tana kallan bakin falaq din dayake rashin kunya ba tsoro amma sbd takaicin maganar tata wayarta ta ciro tana miqawa gaban fuskan falaq tana cewa

"Kin taba ganin me kyau da class din wannan a qaraman rayuwarki??

Kallan hoton kan wayar falaq tayi wanda Kyakkyawan fuskan Ammar zad take bayyane yana zaune sanyeda suit farare yayi kyau sosai da murmushi akan fuskansa.

Kallansa ta sake yi kafin ta dago ta kalli jannah din ta sake mata wata dariyar data saka jannah din itama dariyarta sbd ta dauka dariyar ta sakar mata ne.

Dariya sukai sosai kafin falaq ta dena dariyar ta kama hannunta zuwa gurin Daddynta dayake nesa dasu sosai yana waya har lokacin.

Kwace hannunta jannah tayi sbd sauri takeyi ita bata time din batawa daman biyowa tayi ganin wata a gurin.

Cikin sakewa Falaq tace

"Kin nunamun naki zan nuna miki nawa"

Kin tafia jannah tayi dan haka sbd tai mata wayo taje ta karba rigar sai tace

"Kije kizo dashi gani nan ina jira ina kallanki kada tsoron ganin Best Man ya sakaki guduwa dan bazaki iya nuna daddy dayake tsoho ba"

Matse fuska falaq tayi tana cewa

"Bestyna baya zuwa kiran kowa saina Falaq Aziz and bazan kirasa sbd kowa ba sai sbd kaina dan haka bazan kirasa nan ba amma wait and see...

Nufarsa tayi da gudu tana kusan kaiwa gurinsa ta kira sunansa ya juyo a natse gaba dayansa yana kallan yanda take tahowa da gudu.

Jannah dataso falaq din na tafiya ta juya ta karbi rigar ta tafiyarta
Juyowansa ya sakata tsayawa a gurin tana kallan fuskansa dayake kallan Falaq da dukkanin kulawansa batareda ya kashe wayar dayake ba.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
34
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

************
Falaq riqo hannunsa tayi cikin farin ciki da murmushi tana janyosa dan ya siya mata rigar da kansa.

Tinda suka tinkarota taji numfashinta na fita da sauri bugun zuciyarta na qaruwa ahankali idanuwanta na kasa daukewa daga kansa,

Aura dinsa ce gabaki daya ta cike ganinta harma da hanci da bugun zuciyarta dayake tsananta ahankali ahankali,

Waya yake har lokacin a cikin nutsatsiyar turancin da muryansa datake fita ahankali a kame ba hayaniya cikin wani irin steez.

Suna kawowa daf da ita qamshinsa me tsananin sanyi da nutsuwa da tsadar gaske na Tomford ya sauya iskan datake shaqa da gurin datake tsaye.

Ta gefenta ya wuce batareda ma yasan da akwai rai a gurin tsayeba yana nufar inda Falaq ke jansa wadda itama suna wucewa juyowa tayi ta kalli Jannah din wadda take tsaye a gurin batareda ta motsa ba bare juyowa ta kallesu..

Sayd da already ya biya kudin suna isowa ya miqa mata jakar da aka saka kayan Ta karba tana murna batareda ta saki hannun daddynta ba suka bar gurin batareda ta juyo ta kalli jannah ba sbd batason ta sake kallan Daddynta sbd tanada kyau.

Jannah kuwa daga inda take tsaye bata juyoba wucewart tayi ta nufi motarta datai parking ta bude ta shige tareda barin gurin tana dan dafe setin zuciyarta dayake bugawa da karfi ahankali tana dora idanuwanta akan titi kuru ta nufi gidan Daddy mahmoud datake zaune acan.

Falaq kuwa daddynta ta bi yana waya har lokacin ya zauna kujeran hutawa da Sayd ya hada masa da rumfa tareda table da abubuwan falaq din suke kai sau ipad da roban ruwan dayasha ya rage akai.

Wayarsa yaci gaba da yi a natse bayan ya zauna kenan.

Farin goggles dinsa ya zare ajiye gabansa yana dago fararen idanuwansa ya zubawa falaq dake wasa sosai a gabansa tana tsalle tareda abokanta da teachers dinsu uku da suka shiga cikinsu suna sake karfafa tsallen da farin cikin wasan.

Sayd dayake busy mutum ne dan kusan shine office din AZIZ da kansa kokuma yace shime computer dinsa dan hakanne ya saka shi baida wani hutu koyaushe aiki ne kawai da handling abubuwa.

AY na gama wayar ajiyeta yayi tareda sakata do not disturb sbd bawa 'yarsa cikakkiyar time da nutsuwansa dan haka a hankali cikin nutsuwa ya dora kafarsa daya akan daya ya jinginar da bayansa a kujeran yayi relaxing yana folding hannuwansa a zuba mata ido yana kallan yanda take dariya.

Dariya da farin cikin falaq shine yake sake bayyanarda tsananin kamarta da mahaifiyarta da kamannin dabiunsu shiyasa a irin wannan lokutan zuciyarsa take sanyi da tsananin kewan Ummitah wadda yake kan karban therapy har yanzu da lokaci me tsayi yaja na rashinta amma haryanxu zuciyarsa bata taba dawowa daidaiba sbd ya riga ya samu raunin da ba lallai ya warkesaba har yabar duniya sedai yana iya kokarin hana hakan kaisa qasa sedai da dama wasu lokutan saiya kusan kaiwa kasa kaman bazai iya daurewaba Sayd ne a tsayin dakan ganin hakan bata faru ba,

Babu wanda yake gani ko ya taba sanin rauninsa sai Sayd wanda yasan zuciyarsa rasa jarumtarta takeyi idan ciwon rashin yar uwarsa ya taso masa wanda hakan ya riga yayiwa rayuwarsa illan da Allah ne kadai zai tallafesa.

Itama kallansa takeyi akai akai tana nuna masa abinda suke cikeda farin cikin kasancewansa a gurin..

Lumshe mata fararen idanuwansa kawai yakeyi tareda gyada mata kai a natse yana murmushi a duk lokacinda ta nuna masa.

Ahaka suka jima kafin lokacin sallah yayi ya miqe sayd ya kawo masa ruwan da yai alwala sukaje sukai sallah suka dawo a lokacin ta gaji sosai itama sallan tayi kafin tai lunch tareda kowa har lokacin yana nesa zaune cikin tint yana dan duba sakonni tareda sauraron Sayd wanda ZAADENs suka sake nema yai rejecting nasu kai tsaye sbd bayajin Har abada zasu samu abinda sukeso daga AZIZ LIMBA dan sune sukeson ganinsa kuma suke buqatan ya amsa gayyatarsu zuwa garesu wanda indai hakan ne to kome sukeso garesa bazasu taba samu ba har gwara su su kawo kansu da kansu to akwai yiyuwar su samun dan haka kwata kwata yama qi sake sanar masa request din nasu yake rejecting kai tsaye.

Har dare sosai aketa party da wasanni tareda wasu abubuwan na ilamantarwa ga yara da wanda suka fara zama yan mata da matasa har kusan 9 tukuna aka gabatar da gurin baccin yara da tint masu kyau da kowa iyayensa suka tanadar masa dan haka ba bata lokaci Falaq da aka gama gyara mata komai kaman wadda tafi kowane 'da a gurin sbd Daddynta da uncle dinta babu abinda baa tanadar mata ba da zata buqata.

Daga ita har Daddynta Sayd bai taba wasa da duk lamarin daya shafi buqatarsu ko kulawa ba musamman shi din sbd hakan ne ma yasa babu wanda yasansa duk duniya irin Sayd,

Lafiyayyar tanti da a wadace da nutsuwa aka hada masa shida Falaq din dan haka ba damuwa ko wani rashin jin dadi tayi baccinta shi kuwa bai wani yi baccin ba.

Sayd kuwa nasa tantin daban,

Daurewa sukai washe gari aka qarasa sauran activities din aka sake kwan suka tattaro suka dawo cikin farin ta samu abinda takeso karan farko da daddynta yabarta ta shiga irin wannan activities din kuma ya tafi da itan dan haka koda suka dawo bayan gama gaisawa da mama bai tsaya komaiba ba ya shige bangarensa dan yana buqatan hutawa.

Sayd ma hutun yake buqata dan haka abinci kadai yaci ya shige shima.

Ita kam sbd murna yau shirin takeji da mama dan haka a jikin maman ta kwanta tana bata labari kala kala hardana Kyakkyawar lady din data hadu da ita.

Yanda take yawan fadar Kyau da class din Ladyn ya saka Mama tsokanarta da cewa

"To kodai Wannan karan Falaq Aziz taga wadda zata iya bari uban nata ya aura??

Shiru tayi tana sake tino Fuskan jannah din da yanda take magana muryanta ba hayaniya amma kuma tace wani yafi daddynta kyau dan haka ta girgiza kai sa sauri tana bata fuska tace

"She's good amma No daddyna bazai aureta,baya sonta tace wani yafisa kyau kuma tamun tsawa kuma daddyna yafita komai,bana sonta kwata kwata ma"

Fiddausi dake son shan labarin tace

"To inda batai miki tsawan bafa ai da kilan tanada chance ko??

"Kallan Fiddausin tayi tana jikin maman har lokacin tace

"Eh kila,amma dai No"

Mama da zancen ya fara isarta tace

"To indai kin fara tinanin zaki bari uban naki yai auren ai anyi arziki tinda haka ya zaba na biye shirmen banza da tinanin wadda bama hankalin ne da ita cikakke ba"

Falaq bata fuska tayi tana kokarin tashi ta kalli maman tayi magana
Maman ta hanata tashin tana cewa

"Kina cemun witch ko oldLady zanyiwa bakinki mugun dukan da saiya fashe yayi tsawonda sbd muninsa ma ko Babanki bazai ganeki ba"

Shiru tayi tana sake bata fuska qasa qasa tace
Chapter 43 · 0% Book details