← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 120

Sashe 77

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Asuba wayar falaq dinne ta tadasu bacci.

Cikin bacci jannah taji ringing din wayar a cikin kunnenta sbd tana ta gefenta akan bedside dan haka hannu kawai ta miqa tana jin bacci na sake cike idanuwanta.

Dauko wayar tayi batareda ta duba sunan me kiranba tai rejecting ta ajiye tana dake qaramar tsoki sbd tama manta kwata kwata da ba ita kadaice ba ayau din so ta dauka tata wayarce.

Sake kira akai kai tsaye sbd a nasa bangaren tinda yarinyarsa ta fara wayo yake koya mata sallah akan lokaci shiyasa ya sabar mata duk asubar duniya yana nan ko baya nan saiya tadata sallah akan lokaci, tin bata saba ba harta saba yana kira take tashi tayi sallanta a lokaci ta koma ta kwanta,

Ayau karo na farko na rayuwarsa da akai rejecting call nasa kuma daga wayar 'yarsa shiyasa kai tsaye ya sake saka kiran.

Wannan karan kiran na sake shigowa Jannah ta sake motsawa tana miqa hannu a fusace ta dauka ta batareda ta duba sunanba dan ko gani batayi sosai sbd baccin dayake idonta ta saka handsfree kafin tai magana muryansa ce mai kauri da sautinta yake bada wani irin sexy vibe din da zai iya juyar da kan da yawa wasu idan suka ji sbd a lokutan da ake tashi bacci a lokacin muryan mutane da dama sautinta komawa yake na tada hankalin wasu,

So tasa muryan a koda yaushe hakan take idan har ya tashi bacci yayi magana to zai iya daga hankalin me sauraronsa dan haka ahankali muryansa ta bayyana a cikin wayar a natse yana cewa

"Why did you reject the call???

Bude idanuwanta dake rufe jannah tai tana kallan sunan dayake kan wayar jikinta na wani irin mutuwa ta tashi zaune tana kokarin hana sautin numfashinta shiga wayar amma saida ya shiga cikin wayar ahankali ya sauka a cikin kunnensa.

Cire wayar yayi daga kunnensa yana saka handsfree ya ajiye gefensa yana sake jefa tambayarsa

"Why did you reject the call?

Yasan ba yarsa bace sbd har abada Falaq bazata taba rejecting kiran Daddyntaba.

"Numfashi me dumi ta sake sauke ahankali bugun zuciyarta na dan qaruwa ta bude baki Ahankali da muryanta dake cikin sauran yanayin bacci tace

"Sorry na manta na dauka wayana ne"

Takaici da mamaki ne ya kamasa lokaci daya kamar bazai tankata ba sai kuma yace

"Tarbiyan yarinyana dana gidanku ba daya bane,
Tana tashi sallah in time bata taba tsallakewa ba sai ayau karan farko data kwana a inda bai kamataba,
Ke baa koya miki sallah kan lokaci bane?
This is unbelievable" ya fada yana kashe wayarsa cikeda damuwan abinda yasaka Falaq zuwa zaadens da bai yadda da komai nasuba.

Shiru jannah tai da wayar a hannunta tana kalla idanuwanta suka ciko da hawaye masu dumi amma bata bari suka saukoba ta sunkuyar da kanta zuciyarta na daci sbd tinda take a duniya bata san komaiba bayan gata sai ciwon da Allah ya jarabceta dashi,

Bata taba sanin ya daci da ciwon fada,zagi ko baqar magana yakeba a rayuwanta,
Ta samu tarbiya duk gatanta iyayenta sun tsaya sun bata tarbiya daidai gwargwado hakama itama ta taso da sallah din akan lokaci bisa koyarwan iyayenta da yan uwanta musamman Ammar bai taba tashi sallah da asuba bai kirata ba ta tashi sunyi kusan lokaci daya.

Kalamansa ne suke mata radadi amma batasan ma metake ji ba akansu,
Ya kirata mara tarbiya ne ita kadai kokuwa harda Familynta??

Falaq ce ta fara motsawa alaman zata farka sbd indai lokacin sallan yayi sbd sabo to sai Allah ya bata ikon tashi.

Kallan falaq din tai kafin ta ajiye wayar hannunta ahankali jikinta a sanyaye hawayen idanuwanta n gangarowa ahankali ta zira kafafunta qasa ta sauko tana miqewa ta nufi toiletta shige.

Tana fitowa wayart na nuna haske alaman shigowan kira.

Falaq ce data tashi zaune idanuwanta suka fara sauka akan wayar taga qatuwar heart ce kawai da kiss take tasan Ammar ne ta sauko gadon tana tura baki tana magana qasa qasa harda buga qafa ta fada toilet.

Jannah kuwa mamaki ne ya kamata sosai na ganin kiran sbd ta dauka bazai dake kirantaba tadata sallah.

Jikinta dayake mace ta zaunar bakin gado tana daukar wayar ta dora a kunnenta cikin sanyi ta furta sunansa.

Ajiyan zuciya ya sauke da numfashin daya kusa barin kirjinsa sbd harga Allah bazai iya rayuwa babu jannah ba,
Bazai taba iya moruwa ba idan babu jannah a rayuwarsa,
Bazai iya barwa kowa jannah ba,
Yana mata wani irin mayen so da bazai taba jin zafi ko ganin laifintaba dan hakanne ma zuciyarsa ta kasa hanasa cigaba da sonta da nemanta tinda auren ance na wata uku ne ya yadda zai jira indai zata dawo garesa ya yadda ya zama wawa mahaukaci mara zuciya ya jirata.

Sake ambatar sunansa tai a natse tana danne damuwar datake ranta.

Cikin nutsuwa shima ya bude baki yace

"Time na sallah yayi"

"Na tashi already"

Shiru sukai kafin tace

"Thank you"

Kashe wayar tayi bayan ta fada hakan ta ajiye tana miqewa ta saka kayan sallah sukai sallan tareda Falaq daketa jin haushin kiran Ammar din.

Suna gamawa sun dan jima suna Adhzkhar kafin suka koma suka kwanta sbd dukkaninsu yayan hutu ne da basusan wahalarda kai da tashi da wuri ba.

Fiddausi kuwa a dakin data kwana gari na wayewa ta fito ta nufi kitchen ta gaisa da masu aikin gidan da chiefs dinsu suna yar fira tana aikin breakfast din falaq dana zuwa school dinta duk da tana SS1 sbd yanayin karatun can dana nan daba irin tsarin wanda tayoba bane sai aka sakata a ss1 sbd tagane na nan din yanda ya kamata amma tana zuwa da abinci sbd yanayin hygiene na abincin school da hankalinsa bai kwanta duka dashiba duk da tsadar school din da abincinsu da kamanma a makarantar qasashen wajen duk da haka na nata take zuwa.

Fiddausi na gama hada komai ta jera a tray ta nufi dakin Jannah.

Tana isowa knocking tai so daya kafin ta bude dakin ta shiga ta maida ta rufe ta nufi table ta ajiye kayan hannunta tukunta ta zagaya bangaren Falaq ta durqusa bakin gadon tana kama hannun falaq din tareda ambatar sunanta a natse sbd baa tadata bacci cikin tashin hankali koyaushe kaman zaa sakata wani baccin ake tadata.

Sake ambatar sunanta Fiddausi tai tana gyara mata rufa.

Motsin gyaran rufar ya sakata motsawa Fiddausi ta sake kiran sunanta.

Bude idanuwanta tai ahankali tana kallan Fiddausi tace

"Banson school bazaki bari na hutaba kafin Mama da Daddy su dawo"

Murmushi Fiddausi tayi tana yaye mata abin rufa tana cewa

"Ki bari kije yau tukuna sai muyi wannan shawaran daga baya"

Bata fuska tai tana miqewa zaune tareda saukowa gadon tana cewa

"Fada kawai kikai bazaki yaddaba na sani"

Toilet ta nufa Fiddausi tabi bayanta da towel ta kai mata daman already tin jiya aka jere mata kayan wankanta da dauran amfaninta a cikin toilet din duk da koina tsadaddun kayan amfanin jannah dinne masu kyau da tsada amma dai haka itama aka jera nata.

Brush da wanka tai ta fito daure da towel lokacin jannah ta farka ta sallami Fiddausi dan haka itace ta tayata shiryawa tai breakfast suka fito.

Itace takaita school tareda Fiddausi da baa barin falaq zuwa ko gate ba tareda itaba.

Suna zuwa kafin ta shige saida tai waya da Daddynta kafin ta bawa Fiddausi wayanta ta shige suka juya.

Suna dawowa gida jannah bacci ta koma sbd duka mutan gidan babu wanda ya tashi.

Fiddausi ma komawa masaukinta tai sbd ta gama aikinta na dole waton kulawa da Falaq.

Sai guraren 10 suka fito daya bayan daya suna haduwa a dining.

Cikeda kulawa da kauna dad ya kalli jannah data zauna kusa dashi tana kama hannunsa tai masa ina kwana yace

"Ina Falaq Aziz?

"Tana school"

Maheer ne ya kalleta yace

"Waye yakaita?

"Nice na kaita"

Shiru sukai dukkaninsu cikeda tausayinta da kaunarta.

Breakfast suka fara ci Maheer na cewa

"Gobe xan sanar da driver na yaxo tinda safe ya kaita sbd sanyi zai shigeki idan kina wannan fitan na tinda safe"

Dagowa tai ta kallesa zatai magana sai kuma ta fasa.

Suna gamawa ta koma dakinta tana wayoyinta da chats har kusan 1 da wasu mintina ta tashi tai sallah.

Fiddausi dataga lokacin dauko Falaq din yayi ta samu jannah din ta sanar mata.

Fitowa tai zuwa daukota Maheer yace ta koma ya aika driver yaje daukota batareda anje da Fiddausi ba.

Ko kafin driver yaje school din saida Maheer ya aikesa office ya karbo masa wasu takardun ya dawo gida ya basa tukuna ya koma daukota.

Zuwa lokacinda ya isa an dade da tashi daga school din falaq da tinda take a rayuwarta bata taba fitowa daga class ba tareda driver da Fiddausi na gate suka jirantaba sai ayau kuwa,

Galabaita da tsoro ne sosai suka shigeta wanda ya saka idanuwanta fadawa sosai sbd sai 3 zuwa 4 aka daukota.

Koda aka iso gida da ita duk ta fita hayyacinta daman Fiddausi tinda lokacin daukota yayi taga baa kawotaba bata dake zamaba taketa yawon xuwa gate hankalinta a tashe zuciyarta na tsinkewa gashi tana tsoron kiran sayd ta fada batasan hukuncin da mai gidan zai dauka ba akan hakan.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
63
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Chapter 77 · 0% Book details