← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 120

Sashe 50

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad ma kallansa yayi cikin kulawa yana sake masa sannu ya tattara ipad dij sayd din da qasu abubuwan da suka zube ya sauke ya dauka a table dayake tsakiyar dakin yana kallan time yace zai tafi yaji da office tinda yau daga shi har Ogan kwata kwata bame shiga office din.

Cikin nauyin muryansa datai kauri sosai sbd nauyin dayakeji a kirjinsa na tsoro da tashin hankali tareda wani irin masifaffen tiriri da zafi ya bude baki yakira Fahad din.

Dakatawa yayi tareda juyowa yana dawowa cikin girmmawa ya bude baki zaiyi magana Sayd ya katsesa da cewa

"Dr Abraham a wane asibiti yai aiki a Nigeria??

Ipad dinsa ya koma motarsa ya dauko ya dawo yana bude duka bayanan daya samu akansa na fili dana boye ya fara karanto masa

"ZAADEN HLTH CEN/SPEACIALIST,
Yayi aiki tareda Dansa kaman yanda na fada maka,
Yanada kusanci da ZAADENs sosai coz sun zama tamkar family"

Shiru Sayd yayi yana shiga tinani kafin ya sake bude baki yace

"Alaqar menene a tsakaninsa dasu da suka samu kusanci? I mean wane hulda ne tsakaninsu?
Is he a business man apart from being a Doc??"

"Nope" fahad ya fada yana sake duba profile din Dr Abraham din dakyau wanda aka hada aka turo masa.

Dagowa Sayd yayi ya kalli fahad yana sake shiga tinanin dayake nauyaya kansa ya bude baki yace

"Shine family doctor na ZAADENs kenan?

Yes"

"Meya hadasu da likitan zuciya da iya aikin zuciyar ya sani dazai zama family doc dinsu wanda har suka taho dashi qasarsu?

"I don't know that Boss Amma akwai yiyuwar sunada patient me heart problem din shiyasa ya zama family but.....

Katsesa Sayd yayi cikin Wani irin sautin daya saka fahad din kallansa da sauri..

"Inason full background details na ZAADENs tin daga Kakansu asalin Zad din har zuwa yanzu,
Inason medical history da health status dinsu da komai,
Idan nace komai ina nufin har wanda bai kamata a saniba inason full dets,
Ko nawa zaa kashe ina son samun wannan bayanin komai kada a bari kota yaya koda hakan na nufin kidnapping wani ne i mst get the dets"

Shiru Fahad yayi sedai kuma yasan komai zaiyi saiyayi ya samo bayanan da Sayd din ya fada sbd AZIZ LIMBA idan yace yanason details to yana nufin yana sonsu by all means dan haka tinda ya fara aiki dasu babu wani details na sirri da wanda bana sirrinba da baya iya bi ya binciko sbd Allah ya basa wata irin naci da baiwan iya bin sirri ya nemota.

"Yes boss insha Allah zan hada duka bayanan"

Gyada kai sayd yayi yana rufe idanuwansa sbd nauyin da kansa keyi sbd tinanin dayake sake rikita kansa.

Fitowa fahad yayi yana daga wayarsa dan kira yafara bincikensa ayau din duk da ayyukan sun masa yawa ga office ma ana jiransa.

Harabar gida ya fito yana nufar motarsa bayan ya kashe wayar dayayi yana kokarin bude motar sako ya shigo wayarsa.

Saida ya shiga motar ya zauna zai tada motar yaga sunan SIR LIMBA ne ya turo sakon.

Saurin bude dakon yayi yana karanta layi daya daya rubuto masa.

"In my office"

Kashe wayar yayi ya bude motar yana fitowa dauke da ipad dinsa da wayarsa sbd yasan aikine so dole kila akwai yiyuwar buqatar ipad din tinda komai na ayyukansu da ita sukeyi.

Office dinsa na cikin gidan ya nufa yana dan daidaita nutsuwarsa.

Knocking yayi a natse so daya kafin ya bude kofar office din wadda qamshin AZIZ dinne ya fara kado masa cikin sanyi da nutsuwa,

Yana zaune akan sofa ta hutawa dake office din wayarsa na kan table din gabansa fuskansa fresh ba yanayin komai akanta sai aura dinsa data cike gurin ba hayaniya.

Qarasowa fahad yayi yana dan kallan AZIZ din cikin girmmawa da tsananin kaunarsa dayake.

Cikin girmmawa yace

"Gani"

Idanuwansa ya dago ya kalli fahad din dasu ya sake dan karantar yanayinsa kafin ya bude baki yace

"Meyake faruwa?
Wane doc ne Sayd yake neman qarin bayani akansa?

Ipad dinsa ya dago ya nemo profile din Dr Abraham da komai daya hada yake ciki ya qaraso gaban AY din ya basa cikeda girmama yana cewa

"Dr Abraham,daya daga cikin manyan kwararrun likitocin Zuciya da muka binciko sbd Matsalar Falaq Aziz,

Yayi aiki a Nigeria dan lokaci kafin ya baro,
Close family friend ne na ZAADENs wanda kuma a Nigeria dinma a asibitinsu yayi aiki,

A yanzu cikakkiyar bincike da bayanin asalin alaqar data tsakaninsa da ZAADENs Sir Sayd yace a binciko masa,sai kuma idan ya taba zama gynecology doc wanda kuma tin a gurin binciken namu babu inda ya taba zama gynecologist........

Dagowa AZIZ yayi da fararen idanuwansa daya zubawa Dr Abraham din ya kalli Fahad a natse yace

"Gynecology Doc??
Meyasa yake son sanin hakan?

"I don't know Sir but yanason sanin Medical history na familyn zadeens gaba daya wanda inaga kaman yana tinanin akwai me ciwon zuciya a cikin familyn shiyasa suke tareda dr Abraham din kuma ya dage yanason sanin Meya hada likitan zuciya dana mata"

Shiru AZIZ yayi yana sauraron bayanan suna shiga kansa daki daki yana tinani akansu sbd sanin Sayd baya binciken abinda baida tsananin mahimmanci hakama tareda boye masa wanda hakan ne ya saka tinaninsa tsayuwa akan koma menene yanason confirming nasa ne kafin fada masa,

Idan har sai yayi confirming kafin ya sanar dashi to tabbas mahimmancin abin na tattareda hadarin dayake gudin basa false bayani...

Shiru gurin ya sake dauka kafin Wayarsa dake gabansa ya miqa hannunsa ya dauka batareda yace komaiba ya nemo Numbern Alh Saad ya saka kira kai tsaye.

Ringing uku tayi aka dauki wayar
Cikin kwanciyar hankali a natse suka gaisa tareda tambayar su Falaq dasu mama yace duk suna lafiya shima ya tambaya su anty maryam da sauran yaransa da suka zama yan mata duk suna university.

Kai tsaye bayan gaisuwar ya jefa masa tambayar data saka Alh Saad din Ajiye cup Tea dayake hannunsa yana sha a natse cikim lafiyayyan palonsa dayake katafen gidansa.

"Wane Asibiti ne Ummitah ta haihu???"

"ZAADEN" Alh Saad ya fada cikin tsananin mamakin tambayar sbd tinda akai rasuwar yayi jinya ya warke har yau bai taba tambaya ko fadar magana ko daya akan ciwon datai da rasuwarba shiyasa suma sukai shiru babu wanda ya fada masa irin yanda taita jinya kafin haihuwar sbd ya zabi danne ciwon rashinta a ransa ya mutu dashi batareda yaji azabar ciwon datasha ba wanda zai qarasa dagargaza karfin zuciyar daya sakawa kansa ne.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
40
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.

https://chat.whatsapp.com/IyDlSVdw1rDIlCNNQMel68

Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

**************
"Thank you" AZIZ yace yana kashe wayarsa ya ajiye gefensa ya dago ya kalli fahad dayake jiran umarninsa bude baki yace

"Dukkanin Abinda ka sani na bayanin daya buqata ka hadosa cikin gaggawa inason sanin koma menene daya shafi wannan maganar"

Cikin tabbatarwa Fahad yace

"Angama Sir"

Harya juya zai fice AZIZ din ya kirasa ahankali
yana juyowa yace masa yanason Ipad din Sayd a hannunsa yanzu.

Ficewa fahad yayi ya koma dakin Sayd wanda yake toilet yana sakarwa kansa ruwan dumi sbd sake samun karfi.

Baima tsaya komaiba daukanta kawai yayi ya fice ya kaiwa AZIZ wanda yana karba mai tsaye history na browsers dinsa ya ringa shiga.

Shiru yayi yana bin duka histories din wainda duka bincike ne kawai yake akan Masu ciki da yanda ake cire zuciyar dan adam sai kuma bincike akan scar din da aikin zuciya yake bari wanda kusan shine yafi yawa.

Shiru yayi yana ajiye ipad din gefensa tareda dan rufe idanuwansa yana hana kansa tinanin komai dan baisan me sayd zaiyi da wannan binciken ba seda kuma binciken da zaayi akan zaadens ne yake buqatan sanin dalili ga kuma dr Abraham da shima yake nacin neman bayanin komai akansa wanda duka idan aka hada link daya ne asibiti tinda shima Sayd idan har yasan Abraham a asibitin ne wanda duka kuma dai haihuwan Ummitah ce takaisu asibitin da har akai haduwar.

Nunfashi mara sauti ya sauke yan bude idanuwansa ya dauki wayarsa ya miqe yabar office din zuwa cikin gida.

Kai tsaye dakin Sayd din ya sake zuwa ya dubasa ya tararda ya kwanta bacci ma ya daukesa dan haka ya wuce nasa bangaren bayan ya sanarwa mama ta kwantar da hankalinta b damuwar komai bane may be ma stress ne na aiki da zaman da basu cika yiba.

Yadda mama tayi ta dan kwantar da hankalinta sbd Sayd shima 'da ne gareta tana kaunarsa sosai da sosai.

Falaq bata gida tana school shiyasa gidan yake tsit sai data dawo hayaniyar gidan ta dawo.

Abincin rana gabaki dayansu gidan sukaci a dining kaman yanda suka saba

Sayd ma ya fito dashi akaci abincin sbd bayason yabar kofar da AZIZ zaisan akwai abinda bayason ya sani dan haka ya sake.
Chapter 50 · 0% Book details