← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 120

Sashe 109

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

Miqewa jannah tayi ta fice daga dakin tabar asibitin ma gabaki daya tana zuwa gida.

Tin daga nesa taga gurin a tsananin cike sosai da sauri ta qaraso tana ratsa mutane harta isa gate din gidan wanda yan media da jamian tsaro sukaiwa mummunan kawanya aka fito da Dad dinta daure da cuffs wani irin mugun daurin daya sakata tahowa da gudu kansa Maheer na bayansa shima a daure idaniwansu jajir.

Da gudu tayi kansu tana fasa wani irin kukan dayake neman fasa zuciyarta tana kiran sunasu.

Kallanta Dad yayi idaniwansa cikeda wani irin ciwo me radadi yace

"Jannah kiyi hakuri na kasa zamowa gatanki a lokacin da bakida kowa kike buqatanmu"

Girgiza kai takeyi tana kuka me tsanani tana jin kamar ranta zai bar jikinta.

A mota aka sakasu aka tafi dasu anata musu hoto mutane wasu harda jifansu.

Ana barin gurin dasu zubewa tayi a gurin qasa tana wani irin kuka me tsanani da tsima rai.

Miqewa tayi kamar zararra tayi cikin gidan taje dauko file dinta ta fito ko gani batayi ta hau mota tayi asibiti tana isa gaban AZIZ ta tsaya tana masa wani irin kallon dayake cikeda wata irin tsanar gaske.

File din hannunta ta daga ta kunnawa wuta ta jefar a gabansa ta dago ta kallesa hawayen idaniwanta na gangarowa tace

"Ayau inason Ka cire zuciyar kirjina ka bawa falaq zuciyar mahaifiyarta sbd ayau ni Jannah Zad banason bana kaunar duk wani abu dayake na Limbas,
Ayau ni jannah zad na zabi barin duniya na baka abinda shine ya hadani dakai,
Idan zuciyar Ummitah zata cire maka fushi da fansar datake cikeda ranka ayau na baka damar ka cire banaso na gaji,
Na gaji,
Na gaji,
Inason hutawa....

Zubewa qasa tai tana kukan daya saka dukkanin su mama dake gurin yin tsit banda Falaq datake kukan itama tanajin indai sai raba jannah da zuciyar dake kirjinta ita kam ta hakura da rayuwa..

AZIZ file din data kona a gabansa wanda shine zai bawa tasa yar samun sabuwar rayuwa a duniya sbd a cikine manyan bayanan da zasu saka a iya bawa falaq zuciyar daya daga cikinsu suke,

A ciki manyan original bayanan da zasu saka a wa Zaadens hukunci daidai abinda sukai amma a gaban idonsa ta tarwatsa wannan damar sbd samarwa yan uwanta sassaucin da baya musu fata ko kadan.

Tafasa da wani irin zafi kirjinsa ya dauka ya dago ya kalleta kallon dayake jin tana ficewa ransa shima kaman yanda take jin tsanarsa.

Miqewa tsaye yayi yana kallanta da jajayen idanuwansa yace

"Tinda da bakinki kin fada bakya buqata babu amfanin barin Zuciyar a kirjin naki tabbas zaa cire a sakawa wadda ta cancanta,
Daman kashe wata akai dan rayaki kema ba illa bane dan kin tafi wani ya rayu"

Qarasa kalaman yayi suna yankar zuciyarsa yanka me tsananin ciwon gasken daya sakasa dauke idanuwansa daga kallanta tsananin fushinsa da bacin ransa na bayyana.

Zuba masa idanuwanta tai hawaye ba tsiyaya tana jin kalamansa har cikin zuciyarta sbd ayau ya gama bayyyanar mata da girman qin dayake mata da jininta,

Numfashi ta sauke ahankali tana share hawayenta ta bude baki tace

"Wallahi tallahi ni Jannah na Amince da yaddata ba tirsasawa ka cire Zuciyar dake kirjina ku dauki abarku"

Mama data kasa cigaba da sauraron wannan kalaman na zallar baqin ciki da qunci ficewa tayi daga dakin tanajin duniyar na futa kanta itama gabaki daya hakama zuciyarsa na jin zafi da rashin kaunar ganin jannah wadda taketa kokarin hana zuciyarta qinta sbd ba laifinta bane amma zuciya batada kashi hakan na neman gagararta.

Fitowa Jannah tayi idanuwanta jajir suna sake bushewa tabar asibitin tabi hanya tana tasa gurin zuwa ta nema bakin hanya ta zauna tana saka kanta a cikin qafafunta ta fasa kukan da batasan rayuwar da zataiba gwara ta zuciyar Ummitah ta huta itama da wannan masifun.

Har dare tana gurin zaune bakinta da idanuwanta sun bushe qayau ta miqe ta nufi gidansu wanda yayi tsit ma kowa duka familynta dake rayuwar jin dadi da wadata a cikinsa yau an wayi gari babu kowannensu.

A palo ta zube qasa kwance tana rintse idanuwanta sanyin tiles na ratsata,

Bazata iya barin mahaifinta da dan uwanta da Ammar dasuka rage mata ba a duniya su shiga mummunan halin da zasu rasa rayuwarsu ba suma.

Zata tsaya da duk abinda ya rage musu suke dashi ta yaqi AZIZ LIMBA akansu,
Zata tsaya sai ta fidda yan uwanta a wannan masifar sbd bazata taba barin ya samu abinda yakesoba akansu,

Ya samu iya fansarda dan haka ta isa haka sun biyasa harda qari dan haka lokaci yayi dazaisan tsananin qiyayyarta tinda iya soyayyarta ya sani.

Miqewa tayi ta dakinta ta shige ta nufi toilet ta fada tana rufo kofar.

Acan asibitin kuwa da zafin da radadin zuciya tabarsa...

Sayd ma baisamu cewa komaiba kaman yanda mama takasa cewa komai sai jin datai tana son barin qasar ma gabaki daya ba asibitinba.

Karfe goma sha biyun dare falaq ta bude idanuwanta ta saukesu akansa yana zaune gabanta ya zuba mata idaniwansa dukkanin sarewansa tana bayyana a fili.

Lumshe idanuwanta tayi ahankali kafin ta miqa masa hannunta cikin rashin karfi ko kadan da karfin hali tana rufe ido ahankali.

Miqewa yayi ya zauna bakin gadon nata yana dagota ahankali ya kwantar jikinsa yana rungumeta ahankali yana lumshe nasa idanuwan da sukai jajir yana sauke numfashi me dumi yana jin hutun da jannah ke fada shima shi yake buqata daga wannan rayuwar.

Lafewa jikinsa falaq tai cikin sanyin ciwo da jiran lokaci ta bude bakinta ahankali itama tana fatar inama ace rayuwarsu ta baya duka ta dawo da bazata bari kudirin daukan fansa yayi consuming mahaifinta ba zasu barwa Allah komai allah yaji qan mahaifiyarta.

Hawaye ne masu dumi suka gangaro mata suka sauka a gefen wuyansa yaji saukarsu har cikin ransa.

Da muryan data ratsasa sbd sanyi da laushi da nutsuwa tace

"Daddy karka manta a koyaushe babu abinda yakai zuciyar datake da yafiya da tawakkali nutsuwa da samun kwanciyar hankali,
Ka kasance me banbanta kanka daga zama abinda wasu suka zama na rashin alkhairi,
Ummitah rayuwarka ce a baya,
Kafin Ummitah ka rasa mahaifinka ka tsaya kayi gwagwarmaya da rayuwa,
Ka rasa mahaifiyarka ka tsaya kayi gwagwarmaya da rayuwa,
Rashin Ummitah ya tabaka amma ka tsaya kayi gwagwarmaya da rayuwa dan haka a yanzu ma ka kasance me tsayawa kayi gwagwarmaya da rayuwa batareda ka gurbata jininka ko hannuwanka da jinin kowa ba,

Zaadens sun cutatar da kai amma ni bazan taba so nawa mahaifin ya bari zuciya ta rinjayesa ta sakasa aikin da rayuwa zatai masa qunci a gaba kaman yanda taiwa zaadens,

Banason ka bari kaunar dakake mun ta hallakar da kai,
Ni na karbi kaddarata da hannu biyu zan jira kwanakin da suka ragemun su cika batareda kayi yunqurin komaiba da zai hallakar dakai.......

Wani irin kuka ne yakeyi a jikinta yana qanqameta yana jin kalamanta na ratsasa suna kakkaryasa daga jarumtarsa ta shekaru,

Itama kukan takeyi sosai mara sauti zuciyarta na karbawa ba daidaiba sbd baason kowane yanayinda zai taba zuciyar ta rasa sauran karfin daya rage mata na kwanaki.

Sayd ne dayake bakin kofa yana jinsu ya silale qasa shima yana kuka tareda dafe knsa yana rufe bakinsa.

Hawayenta ne suka qara gudu tana jin ciwon kukan da mahaifinta yake ayau me girma a jikinta basuda abinda zasu iyawa kansu sai yanda Allah yayi dasu.

Tace

"Daddy kamun Alkawarin zamu barwa Allah ikonsa,
Kamun Alkawarin bazaka tirsasa jannah ko takurata ko saka kuka a fuskantaba,
Kamun Alkawarin mun bar mata zuciyar Ummitah sbd Allah ne ya tsara zuciyar baa kirjin Ummitah zata rayu ba a zuciyar Jannah ne,
Jannah na cikin tsananin quncin datake buqatan break daga wannan damuwar da babu ranar fita,
Dan Allah inason kamun Alkawarin zatabarta ta zabi abinda take so da kanta wanda zai bata nutsuwa da kwanciyar hankalin zuciya,

Ni nawa haqqin duka dayake kansu na yafe suji dana tsakaninsu da ubangijinsu,
Inason Ayau Daddy kamun Alkawarin zakai freeing raka zuciyar daga dukkanin wannan quncin ka samu nutsuwar zuciya,
Daddy dan Allah kada bari qunci yasake dabaibaye raywarka ko bayan tafiyana........

Karfin da kukansa yayi ne jikinsa na wata irin rawa da jijjiga ya saka nata kukan karfi itama tana jin zuciyarta na gazawa.

Tari tayi me ciwon daya saka jini fesowa daga bakinta tana bata jikinsa da nata.

Sayd ne ya shigo dakin da sauri yana yowa kanta Sbd AZIZ ya fita hayyacinsa kuka yakeyi sosai a jikinta kaman yaro a jikin uwarsa yana rokonta kada ta tafi tabarsa yayi mata dukkanin Alkawarin datakeso,
Bazai sake waiwayan zaadens ba,
Bazai sake tirsasa jannah ba koda rabuwa dashi ta zaba tabbas zai rabu da ita har abada.

Sayd ta zubawa idanuwanta dake lumshewa tana bude baki zatai magana wani jinin ya sake zubowa wanda ya saka sayd din saurin rungumota jikinsa yana ambatar sunanta.

Fiddausi ce data shigo taga yanda jaruman biyu ke kuka a jikin 'yarsu da kowannensu yake shirye da basa zuciyarsa akanta ta fita da gudu ta kira likita.

Da gaggawa likitoci suka iso dakin aka janyeta daga jikinsu aka futar dasu.

Mamace ta rungume su duka biyun a jikinta tsam tana rokon Allah ya kawo musu agajin gaggawa daga wannan musibar.

Acan gida kuwa Jannah itama kwanan qunci tai idanuwanta basu samu bacci ba ko kadan mahaifinta dasu Maheer kawai take gani a idanuwanta tanajin tsoro na rufeta na yanda rayuwa zatai da ita.

Washe gari tin 7 ta fita tafara yawon neman headquarters din da aka kaisu Dad.

Har dare tana yawo bata gane komaiba ta dawo gida ta zube tana jin bazata sanyaya ba zataci gaba da nemansu.
#MAMUH
#BESTLOVE
#BEST ROMANCE
#BEST STORY
#PATIENCE PLS MUTANENA
#HOT LOVE IS COMING

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
maZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee
Chapter 109 · 0% Book details