← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 120

Sashe 65

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai suka sake Falaq taji dadin zuwansu sosai duk da basu fita ba sbd Daddynta ya hana sbd jikinta dayaso tashi dan haka a gidan suka shaqatansu jannah ta saki jiki da ita suka sake kulla kauna me tsafta da karfi.

Sai yamma suka fito zasu tafi falaq na maqale gefen jannah din tana cewa tazo gobe da Allah su tafi inda zasu tafin.

Gate aka bude motarsa ta sako kai a harabar gidan,

Janye kallanta daga gurin jannah tayi tana cewa

Falaq insha Allah idan har Daddynta zai bari goben zataxo ta dauketa su fita.

Janta falaq tayi da karfi zuwa gurinsa daidai latif na bude masa motar yana fitowa.

Kadan ya rage su fada masa ya tare Falaq da hannuwansa biyu yana kallanta fuskansa na sauyawa a natse yace

"Ba na fada ki dena wannan gudun ba?

Kan jannah ya maida kallansa a natse yace

"Are you crazy or wat?
Yarinya qarama kike sakawa wannan gudun?

Dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta dake sauyawa cikin mutuwar jiki da tsananin nauyin kirji sbd tinda take a duniya ko kallan banza batajin ta taba samun wanda ya mata ta sani bare ambatar mata kalma mara dadi bare me munin kiranta crazy dan haka taji kalman har zuciyarta amma bata iya cewa komaiba ta juya zata bar gurin Falaq tayi saurin riqeta tana dawo da ita tace

"Daddy nice na jawota fa,inason ka bari gobe muyi fitan tinda yau ka hana pls pls Daddy"

Bai kalletaba yana wucewa gaba yace

"No"

Binsa falaq din tayi da sauri tana rokonsa.

Jannah kuwa ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa ta nufi motarta.

Anny kuwa Sayd ne daya gama shirinsa akanta yana fitowa mota daman ita ya nufa kai tsaye ya miqa mata envelope dake daukesa dollars masu yawa yace gashinan from LIMBA su qara mai a mota.

Karba tayi tareda cewa thank you batareda ta nuna damuwa da kudinba.

Mota ta bude tana shiga ta bude kudin ta duba batasan lokacinda ta furta

"Hell yeah the great LIMBA"

A lokacin ne jannah ta iso motar ta shigo ta tada tareda tadawa taja suka bar gidan ranta a bace.

Suna isa gida kai tsaye dakinta ta wuce tan wurgi d handbag dinta akan gadon.

Anny kuwa kudin da aka basu ta fadawa Maheer.

Se dare ta fito cin abinci sanye da riga da wando masu dan kauri da hula suna gama cim abinci ta koma dakinta.

Washe gari tinda safe falaq ta kirata t sanar da ita daddynta yabari su fita amma tareda Latif zasu ba itace zata tuqasu ba.

Taso tace batada time amma jin farin cikin falaq din sai bata fada ba.

Da rana Falaq din ta iso gidan tareda Fiddausi Latif ya kawosu suka dauketa suka fice.

Basu dawoba sai dare,

Duk da ta gaji saida ta ringa basa labari kafin taje tayi shirin bacci ta kwanta sbd sunyi sallolinsu acan.

Washe gari ma sake fita sukai sbd falaq tace tanason kayan da jannah ta saka a fitansu na jiyan waton native wear dan haka kaya sosai Jannah ta siya mata suka bayar dinki wasu kuma ready to wear ne na daidai ita masu tsada sosai.

**********Shaquwa a tsakanin Jannah da falaq yawa yafara sosai a cikin qanqanin lokaci,

Duk yanda zai hana falaq ya saka mata qin Jannah din yayi amma kwata kwata hakan shine abu na farko daya kasa cire mata a ranta,
Sosai take tsananin kaunar jannah,
Sun zama kaman saanin juna sbd jannah sosai take biyewa falaq din wanda hakanne yake saka falaq jinta sosai aranta,

A bangaren jannah kaunar datakewa falaq ta sirku ne da tsananin son dayake zuciyarta nasa,
Fuskansa take gani koyaushe akan ta falaq,
Murmushisu daya,
Hancinsu da lips dinsu daya wanda so da dama zata kira Falaq video call ta zauna ta zuba mata idanuwanta tana kallan hancinta da lips dinta da kammaninta gaba daya da suke irin nasa.

An saka falaq din school dan haka sun rage haduwa a maimakon dan lokacin da kusan kullum suna tare ko anan gidan idan tazo kokuma idan falaq da Fiddausi drivern falaq din ya kawosu.

A bangaren mama ta bude masa wuta aure takeson ya fidda mata yayi kokuma ta nema masa matar da kanta wadda ba kowace take hari ba bayan jannah din.

A zaadens kuwa Anny da Sayd ya gama kuncewa kai da barin kudi tini ta gama sauyawa Maheer tinani kwata kwata akan auren Jannah da Ammar sbd Tabbas ya yadda Jannah ba son aure takewa Ammar ba to amma ya kasa yadda da Cewan Da Anny tai Jannah da LIMBA suna son juna amma dai dole wannan karan yafadawa Dad sbd anfara maganar fara hidiman bikin Ammar da jannah din.

Duk abinda zai hada jannah da LIMBA ta janye sbd ganinsa rikita tinani da nutsuwarta yake gaba daya gashi sun samu shaquwar familyn guda biyu sbd kusan yanzu sun zama tamkar family dan shaquwan tayi yawa.

Ammar gabaki daya ya fara sauyawa sbd yawan ziyartar therapist dinsa yayi yawa sbd jannah dayake jin kaman zai iya rasawa dan haka ya bude wuta kawai auren yakeson ayi.

Mimi ma auren take jira dan haka ana fara kokarin shirye shirye ta shiga farin ciki da murna.

Jannah kuwa tinda aka saka lokacin auren wata daya me zuwa rasa sukunin zuciyarta tayi wanda duk yanda take boyewa tana kokarin nuna tsananin soyayyarta da auren love of her life jikinta ya kasa nuna hakan sbd sanyin datake yi hakama Anny tagama illata duk wani kuzari da karfin zuciyarta da zancensa da nuna mata irin soyayyar da zuciyarta ke masa ta hanata sukuni da zancensa duk yanda ta hada karfin hali ta danne abinda takeji akansa Sai Anny ta wargaza mata dan haka gabaki daya t sake zama abar tausayi.

Maheer ganin lokaci na zuwa sosai ga jannah din tana wani irin rama kasa boyewa yayi ya tinkari dad da maganar jannah batason auren Ammar soyayyar dan uwace take masa irin wadda take musu su da suke uwa daya.

Dad jin zancen yayi wani iri kuma ya kasa yadda da hakan dan haka ya kira jannah din sbd wannan zancen kunnowan tashin hankali da masifa ne sbd Ammar zai iya mutuwa idan ya rasa jannah hakama suma idan da gaske ne bazasu iya mata auren da batasoba dan haka akwai tashin hankali me girma a wannan lamarin.

A bangaren LIMBAs kuwa falaq ta shiga damuwa sosai sbd Falaq bata farin ciki da auren da zatai dan haka ta koma musu kaman mara lafiya itama ta shida damuwa karshe gurin daddynta ta nufa a lokacinda ake maganar saura sati biyu bikin.

Da Anny ta gama waya ta zauna ta kasa motsi sbd abinda Anny ta fada mata akan Jannah daddynta takeso akansa ne batason wanda zata aura batason ta bata mata rai ne tinda batason daddynta tayi aure taqi barin kowa ya sani.

Shiru falaq din tayi cikeda mamakin kanta da bataji haushin hakanba amma kuma tanajin kaman bazata iya barin daddynta aureba amma kuma yayi mata alkawarin auren duk wadda ta kwanta mata a matsayin uwa indai batada illar da addini y sharadanta.

Tan tsananin kaunar jannah da bazat iya barin tayi auren wanda bataso ba dan haka koma yaya take kishin daddynta zata bari Jan dinta ta zama matarsa kuma ita kadai ta yadda ta haifa mata kanne.

Take taji ta gama samun nutsuwa da hakan sbd kaunar datakewa jan din duk ta gama rufe mata ido daman batason Ammar din nan ko kadan haka kawai.

Kallanta yayi a lokacinda tazo ta zauna gefensa suna kan dining dukkaninsu gidan cin dinner.

Fara cin abinci akai ta ajiye spoon dinta ta dago ta kalli Uncle sayd daya kalleta yana shirin tambayan lafiyanta ta ajiye spoon din hannunta idanuwanta na cikowa da hawaye tace

"Daddy ka hana auren da zaayiwa Jan bataso Ina son ka aureta ita kadai karka kara auren kowa bayan ita kadai,
Ita kadai nakeso as mum and ita kadai nakeson ta zama maman kanne......

Sarkewa Say yayi da white rice da egg sauce din dayake ci yafara tari da karfi.

Mama ma sauran kadan din ta sarke Fiddausi data rude itama tana kawowa Falaq din yankakken pineapple ajiyewa tayi da sauri tana bawa mama ruwa hannuwanta na rawa kowa ya kasa dagowa ya kalli reaction dinsa gurin yayi tsit.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070
Chapter 65 · 0% Book details