← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 120

Sashe 15

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummitah datake jikinsa gyara zamanta tayi a jikinsa yana share mata hawayenta da handkerchief dinsa me qamshi yana kallan idanuwanta da hancinsa dasuke sak nasa kaman shine ya haifeta,
Tayi haske sosai tama kusan kamosa a haske gata fes fes kusan ta banbanta da yan kauyen sosai sbd ya tsaya sosai akansu yana musu aike sam baya wasa da duk abinda ya shafi cinsu da buqatansu.

Mama sakina kuwa sosai take kulawa sa Ummitan harma mantawa takeyi da ba itace ta haifeta ba sbd so da kulawa da tattali dan hakanne ma Ummitah ta banbanta sosai da duk yaran garin ko yayan me gari va abinda suke nuna mata,
A bangaren gata da sakartawa kuwa kusan kaf garin babu kamarta sbd mamah ta sakartata sosai gata take nuna mata sam bata mata fa kuma Allah bai saka tafara lalacewa hakama sam bata barinta wani fita wasa ko yawo koyaushe tana killace daga makarantar boko da aka sakata ABDULAZIZ din na aiko kudin me mashin din dayake zuwa kaita ya daukota wanda shima da maman ake zuwa a kaita a dawo da maman gidan hakama idan zaa daukota sai anzo an dauki maman aje a daukota a dawo dasu tare sbd sam bai yadda a ringa daukanta ita kadaiba sbd tsaro da kiyayewa.

Dan hakan ne daga makarantar bokon sai Islamiya bata zuwa koina,
Kitso da lalle ma idan zaayi mata mamanta ce take kaita ta dawo da ita daga baya ma kudi ABDULAZIZ din yake aikowa idan zaayi sai azo gida ayi mata duk da tana yarinya qarama sai hakan ya saka gaba daya garin Ummitah ta koma kaman wata 'yar sarki.

Fira yakeyi da mama wanda kusan itace da inna masu maganar shi kuma sbd bai cika magana ba sai maganarsa take a taqaice gashi gaba daya hankalinsa yana kan Ummitah sbd wani irin kallan nutsuwa da kiyayewa yakewa koina nata sbd ganin tabon rauni daya a bayan hannunta ya sakasa bin koina nata da kallan nutsuwa a natse batareda  kowa ya lura da hakan ba.

Mama ta lura da hakan sedai tasan irin tsananin son dayakewa Ummitah bazai nutsuba ganin rauninta dan haka taji shima ta qara tsananin kaunarsa.

Ummitah ma dogayen yatsin hannuwansa dake farare tas kaman wanda yake cikin tsananun hutu take wasa dasu tana basa labarin duka abubuwan datake da baya nan da yanda mamanta ke sangartata da tsananin sonta.

Inna ce basa shiri sosai sbd yanda Maman ta daurewa Ummitah tana girma amma batada aiki sai kukan banza idan taso dawowan ABDULAZIZ din.

Wani irin sanyi zuciyarsa da jikinsa yayi ya dago idanuwansa da suka dan sauya ya kalli mama wadda tai qasa da kanta cikin taushi da muryansa me nutsuwa yace

"Mama Allah ya saka da mafificin khairi ya saka da gidan Aljannah"

"Amin" inna tace tana jin kaunarsu dukansu kaman jikokinta na jini da sakina ta haifa.

Mamar kuwa ajiyar zuciya ta sauke tana bude baki tace

"ALLAH yai muku albarka ya baku kariya da arzikin da bayajin kashewa yai maka budi ya daukaka rayuwarka ya baka duk abinda kake nema duniyar nan yaji qan iyayenku ya tsareku daga sharrin duk me sharri"

Amin" ya amsa dashi a sanyaye yana dorawa da godia.

Abinci lafiyayye maman tayi masa tabarsa yana fira da Ummitah datake ta faman yamutsashi tana basa labarai kala kala yana saurarenta sbd sautin karatun Al'qurani ne kadai yafi masa dadin muryanta da labaranta dan haka wani sanyayyan murmushi ne da babu me gani a fuskansa yake mata yana kallan bakinta yana tina ummansu wadda ita mama ta maye mata gurbinta sbd yanda ya lura tsananin so takewa maman nata shi kuwa har abada bayajin gurbin dayake zuciyarsa na kewan ummansa zai cike sbd yanada qawa zucin mahaifiyarsa duk da mama sakina maye gurbi me yawan gaske a rayuwarsu da kusan yake jinta kaman uwar data haifesa.

Kiran magrib da akai ya sakasa fitowa sukai alwala tareda Ummitah tukuna shi ya fice zuwa masallaci ita kuma tayi sallah tareda mamanta.

Yana dawowa aka jere masa abinci a tsaftacen guri tareda sabuwar tabarmar da maman ta siya sbd zuwansa kawai dan haka ya zauna.

Tareda Ummitah yaci abincin kusan ma duk ita ya tsaya kalla tana cin abincin saida ta koshi kafin shima yaci wanda ta rage sbd ragin nata yakeson yaci sbd son dayake mata irin wadda ko qazantarta abar tsananin so ce garesa,

haka kawai wani lokutan idan ya zuba mata ido yana kalla sai yanajin idanuwansa na sauyawa zuciyarsa na sanyi sbd jin kaman ya maidata cikinsa ya adana daga sharrin duniya dana mutane,
Tsananin So ne me tsafta da babu sirki irin wanda uwa da uba kewa 'dan dasuka haifa yake mata sbd jin yake kaman a tsatsansa ta fito tinda shine uba kuma uwarta,
A hannunsa aka haifeta,shine ya reneta,shine wankanta,fitsarinta da kashinta ma,shayarwa ne kadai mahaifiyarta tai mata dan haka bai sauke kansa daga uwa kuma ubanta ba.

Har dare sosai yana gidan saida tayi bacci a jikinsa tukuna yayi musu saida safe yabar gidan yakoma local government da daman yariga ya kama gurin bacci kayansa ma nan dan baima da niyar zuwa garinsu.

Wanka kawai yayi ya sauya kaya ya saka wayarsa caji ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya take yayi baccinsa hankali kwance.
#MAMUH
#BESTLOVE
#AY LIMBAS
#UMMITAH LIMBA
#JAN ZADEEN
#DONOR

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
12
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

**********
Washe gari bai tafi gurinsu ba sai bayan azahar ya biya ya siya musu kaji lafiyayyu guda biyu da fruits ya taho.

Koda ya iso Ummitah tanata yawon kofar gida da jiransa sbd tana tashi bata gansa ba taso daga musu hankali inna ta tashi tsaye akanta akan karma ta fara musu borin data saba.

Mamanta ce ta ringa lallabata har suka samu ya iso bata rikice musu ba.

Yana zuwa tayi kansa da gudu ta maqale dan ita shi take damuwa dashi ba kayan dayazo dasu ba.

Ciki suka nufa ya miqawa mama kayan hannunsa yana dauke da Ummitan da hannu daya mama na mamakin yanda bayajin nauyinta ko kadan.

Abinci sika ci tare tareda fruits daya saba da cinsu sbd sune suka fara zama abincinsa acan sbd farko farkon zuwansa yayi fama da yunwa da dan rashi kafin ya samu abinyi dan haka su yake siya na kudi kadan yasha ruwa ya kama kansa shikenan shiyasa suka shigesa.

Suna gamawa aka sauya mata kaya tarin kayan daya siyo mata ta saka hijab me kyau da takarmi da turare suka fita.

Suna fita mama sakina ta fidda kayan ta sakawa Ummitah nata a akwati dakyar ya rufe itama nata sakawa tai a akwatinta daya siyo musu ta rufe inna ma takarma da atampa biyi da tirare ya siyo mata dan haka tsofin kayansu da tarin sabulai da omo daya siyo musu ta ringa rabawa yan gidan da moqota tsarabar Hamman Ummitah wanda take aka ringa jin kaunar Ummitah da hamman nata.

Yawo suka tafiyarsu can local government yaje da ita masaukinsa ya siya mata kayan ciye ciye sukaita yawo harda saloon ya kaita akai mata harma da wankin kafa.

Se yamma sosai sika dawo bema zauna ba ya juyo.

Naman kajin ma da mama ta soya tai masa abinci baici ba yace su cinye kawai fresh sabon nono me hade da madaran shanu kawai ya karbo ya tafi dashi ya sha da dare yayi shirin bacci ya kwantawarsa.

****satinsa biyu a garin babu ranar baya fita da Ummitah ya kashe musu kudi sosai ya sake sangartata
Kaf garin babu wanda bai jinjinawa girman kauna da shaquwar dake tsakaninsu dan dole ma aka shafa musu lafiya gashi yanada alkhairi sosai sam baida rowa yan garin sun lasa arzikinsa sosai dan haka kowa yanzu kaunar Ummitah yake sbd farin jinin da ABDULAZIZ din yayi a cikin kwanakin kalilan kowa adduar arziki da budi tareda nasara yake masa.

Da zai tafi saida akai rigima da Ummitah sosai kafin ya tafi cikeda kewanta yabarsu da kewansa suma.

Bayan dawowansa abubuwa sunci gaba da tafiyar masa cikin wani irin nasara da budi dan tini yafara tafiye tafiyen kewayen lagos.

Ahankali rayuwa taci gaba da tafiyar masa hakama karatunsa sosai yake tafiya daidai sai gashi har ghana yafara zuwa harkan business din computers.

Acan ghana ma yayi mutane sosai,
Chapter 15 · 0% Book details