← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 120

Sashe 57

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A natse ya shigo dakin dr Nico na gaba sai Sayd dayake bayansa sai nurse data shigo tana rufe dakin kuma matar Dr Nico dince.

Dago fararen idanuwansa yayi da suka sauya yayiwa Dr ismail kallo daya yana daukesu daga kansa sbd jin yake qinsa na tasowa tin daga qasan zuciyarsa yana mamaye dukkanin jininsa.

Shiru dakin yayi kafin ya sauke numfashi mara sauti kafin ya tako ahankali ya tsaya akansa

Sayd ne ya janyo kujera ya ajiye masa seti da ismail din ya zauna yana dora kafarsa kan daya...

Ahankali cikin tsanani na nisan ciwo dr ismail ya bude idanuwansa da sukai jan ciwo ya saukesu akan AZIZ wanda babu kamannin kowa akan fuskansa sai kamannin Ummitah wadda yana kallo ta cika a gabansa...

Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro gefen Idanuwansa yana kasa dauke idanuwansa daga AZIZ da shima yake kallansa yana hadiye radadin dayake yagar masa kirji da zuciya.

Kasa tsayuwa hawayen dr ismail sukai nadamarsa na bayyanuwa tareda quncin dayake cin ransa,

Wani abu me radadi AZIZ ya hadiye kafin ya bude bakinsa ya kalli ismail din da idanuwansa da suka qame yace

"Marainiya ce batada uwa batada uba,
Cikine a jikinta,
Jaririyar 'ya ta haifa,
Banda uwa banda uba a duniya itace uwa,uba,'ya,yar wa,
Itace tafi mun komai da kowa,
Itace kuzarin danake dashi a duniyata,
Miji ne da ita da uwar dasuke tsaye kofar dakin suna jiran fitowanta da abinda ta haifa...duka wannan abubuwan kuka take kuka rabata da zuciyar da *fuckin bastard din daya bata ita a cikinku Allah ne ya halitta mata ita kaman yanda ya halitta muku,
Meyasa baku cire ta iyayenku kona matanku kun sakawa ita wadda ke buqatan zuciyarba......

Jajir idanuwansa sukai tsananin zafi da ciwon zuciyansa na qaruwa,

Tsit dakin sukai babu me magana sai kukan dr ismail din daya fara fidda sauti kadan..

Numfashi AZIZ din ya sauke yana rintse idanuwansa ya hadiye wani dacin zuciya yana controlling kansa cikin sauti me nutsuwa da samun daidaita kansa da sanyi yace

"Tirsasa akai,i know you did it coz you don't have a choice,
Da saka hannunka aka kashe rai,
Kana danasani sbd kayi abinda har abada bazai dena damunka,

Ka sani akwai rayuka da dama a duniya irin Ummitah dake neman wata damar ta rayuwa sedai su bazasu iya kashe rai ba,
Nema suke sbd Allah batareda cutatar da kowace irin rai ba,
Likitoci sun gano ciwonka bazaka taba warkewaba sai wani ikon Allah wanda koda ka warke monsters din da sukai maka wannan abin bazasu taba barin ka rayu ba zasu nemeka duk inda kake su tabbatarda sun kammala aikinsu akanka,
A yanayinka yanzu kai kanka kasan bazaka taba moruwa ba idanma ka tashi kenan sbd daga yau na gama biyan sisi a neman lafiyarka zaa maidaka Nigeria su qarasa,

Dan haka daka mutu a banza kanada damar gyara kuskurenka ta wani bangaren ta hanyar bawa wani zuciyarka ya rayu,
Kodar datake jikinka ma bazata tafi a banza ba zaka iya sadaukarwa wani me tsananin buqata ya rayu,

Zaka saka families da dama farin cikin da harsu mutu bazasu dena maka addua da fatar rahama ba sbd sun samu sabuwar rayuwa sbd kai,

Karka manta yanda suka kashe Ummitah zasu iya kashe kowama sbd hana sirrin fita...."

Hannu ya miqawa Sayd wanda yayi saurin matsowa ya dora masa takardun dasuke hannunsa yana komawa baya.

Takardun AZIZ ya budewa ismail yana nuna masa yana cewa

"Daga ranar daka bar duniya nayi maka alkawarin daukan nauyin 'yayanka da matarka harsu gama karatu zan bawa mazan aiki matan zan bada dukkanin dukiyar aurensu sbd sadaukarwanka"

Kuka ne me sautin da basui tsammani ba yazowa dr ismail din yana rintse idanuwansa cikin tsananin radadin zuciya me zafin gaske.

Miqewa AZIZ yayi yana miqawa dr Nico takardun yace

"A sanar da familynsa yayi nisa yana son ganinsu da kansa idan harya amince."

Juyawa yayi zai fice Dr ismail ya ringa kyafta idanuwansa cikin tsananin kukan da babu sauti ba motsi sai tsananin quncin dayake kokarin saka zuciyarsa neman bugawa.

Da sauri dr Nico yayi kansa yana cewa matarsa ta kira familynsa da dr Ayyan.

Fita tayi da sauri Sayd kuwa AZIZ daya rintse idanuwansa cikin jin quncinsa na qaruwa kafin ya bude idon ya nufi kofa ya fice batareda ya juyoba sayd yabi bayansa suna barin asibitin gaba daya.

Matar dr ismail din kuwa da qaninsa ana kiransu da gudu suka qaraso jikinsu na rawa matarsa kallo daya tai masa ta fasa kuka tana neman shidewa tana qanqame hannunsa.

Qaninsa ma tashi hankalinsa yayi idanuwansa sukai jajir.

Doctors kuwa kansa suke kokarin rufa amma rikicewa jikinsa yake sake yi...

Takardun hannun dr Nico ya qurawa idanuwansa dake neman juyewa yana motsa hannunsa cikin wani irin karfin hali yakeson nunawa matarsa da qanninsa takardun Alamar da yardarsa sedai sam basu lura va sbd tashin hankali.

Fiddasu akai da sauri sbd ana buqatan shiga aiki dashi da gaggawa..

Takardun shiga aiki aka basu suka saka hannu aka wuce dashi da gaggawa suna gani matarsa na wani irin kuka shikuwa kanin sunkuyar da kai yayi yana maida hawayensa dake cika idanuwansa duk da sunsan aikin zuciya zaai masa basusan bazai fito da raiba shikenan ya tafi har abada.

Ana shiga shigewa da ismail dr Nico da badashi zaayi aikinba ya kira AZIZ ya sanar masa tareda godiyar wanda suka samu donor din dan musulmi ne ma kuma me iyalai dan haka hakan ba qaramin farin ciki da sabuwar rayuwa zai kai a familyn ba.

Sayd kuwa take ya fara shirye shiyen komawar familyn dr ismail din sbd yasan shikenan komai ya qare.

A lokacinda aka isarwa da familynsa Allah ya karbi ransa yanke jiki matarsa tayi a gurin...

Qaninsa ma tashin hankalin ya shiga sedai daman sun riga sun cire rai daga tashinsa dan haka matar aka fara kokarin cetan ranta cikin gaggawa har aka samu ta dawo daidai zuciyarta tai mata wani irin nauyi kukan ma ta nemesa ta rasa sai ajiyar zuciya datake saukewa idanuwanta sunyi jajir.

Washe gari anan italy akai masa komai aka rufesa sedai acan gida aka fara zaman karban gaisuwa cikin jimami na baqin cikin rashinsa.

Kwanansu biyar a hotel da aka sauya musu sayd ya sakosu jirgi batareda sun taba sanin LIMBA ba ko kammaninsa.

Suna dawowa kuka ya dawo sabo a familyn na rashinsa wanda yaransa hudu maza biyu mata biyu suke cikin baqin ciki da qunci.

Acan italy kuwa suma a ranar da familyn suka bar qasar kwana daya suka qara suka tattara suka koma gida.

Suna dawowa kawai shirin baro kasar suka fara sbd sayd ya kai karshen Wani mahaukacin sabon mansion da aka siya har anyi payment da komai Alh Saad ne da lawyers dinsu a cikin siyansa.

Luxuries din da aka zuba gidan saida ya ringa bawa Lawyers din mamaki sbd Yace duk abinda zaa saka yayi daidai da yanayin rayuwar da falaq ta saba ta taso a cikinta dan hakanne ma aka zuba dukiya iya dukiya kaman ba nemanta akeba debowa kawai ake.

Securities din kwarai aka dauka aka zuba a gidan bayan an tantancesu tareda masu aiki wainda Latif ne a wannan bangaren yake wannan aikin dan tini ya rufe shago jin ubangijinsu the great AZIZ AY LIMBA zai dawo Nigeria,

Shine chief officer na gidan duka maaikanta gidan a karshinsa suke hakama qanansa biyu ya dauko sune drivers na gidan daya hajia mama dayan kuma wanda yafi tsananin kiyayewa da taka tsantsan drivern falaq ne.

*********Kusan wata uku suka share suna shirye shiyen kafin suka siya tickets da komai bayan ya nada sabbin presidents da chairmans da directors na companies dinsa dasuke qasar shikuma zai karba na Nigeria din.

Babban tarkon daya dana wanda shine sanadin da komai zai fara shine Siye dukkanin hannuwan jarin businesses din sauran companies dasuke aiki da Zaadens batareda saninsu ba sbd a iya bincikensa ya tabbatarda sunada power me karfi,
To idan zai kaisu qasa su nema hanyar kabarinsu da kansu to saiya fara rabasu da komai daya bayan,
Duk wani abu dasuke so a duniya saiya rabasu dashi akan idonsu......

JANNAH ZAD itace abinda sukeso fiyeda komai kuma suke komai akanta,

Tsanar da yake mata batareda ya san waye ita dinba ta gama gauraya dukkanin wani digon jinin dayake yawo a jijiyoyin jikinsa....

Itace zaiyiwa mummunan illan da suna gani batareda sun iya komaiba kafin ya karbe abinda yake nasa daga jikinta yabar musu gangar jikinta.

Bazai taba nemansu da kansu yakeson su kawo kansu gurinsa da dukkanin yarda da buqatuwarsu dan haka tashik farko hannuwan jarin daya siye da sunayen Alh Saad da Wasu manyan abokan businesses dinsa ya saka suka ringa janyewa suna cirewa daga business din zaadens wanda cikin qanqanin lokaci arzikinsu yayi wata irin girgizan data sakasu tashi cikin mummunan tashin hankali da tsoro sbd kawai companies dinsu qasa suka fara yi kaman saukan ruwan jiki......

Hakama kusan manyan ma'aikatansu da suke ji dasu take suka ringa ajiye aiki bayan sun satar musu manyan kudaden dasuka qarasa Jijjigasu kuma sata irin tsaftatacciya da babu inda suka bar evidence ko record na fitar kudaden gaske.

Neman zaucewa sukeyi take suka tashi tsaye da neman hanyar tsayar da wannan iftilain kwatsam daddy mahmoud dayake can qasar daga fita aka kira ya samu stroke.

Bp din Dzad daya dena tashi tinda Jannah ta samu lafiya ne ya tashi hankalinsu yafara tashi sedai sam basu bari duniya tasan suna yin qasa ba.

Sbd gudin raba hankalinsu biyu a yanzu da suke cikin crisis dawo da daddy mahmoud Nigeria akai suka hade mansion daya ana jinyarsa a gida kawai aka dauki manyan doctors dake zuwa dubasa kullum.

A ranar da aka dawo da mahmoud Nigeria jirgi daya ne ya saukesu a Nigeria da LIMBAS family wainda motaci suka daukesu zuwa LIMBAS mansion.
#MAMUH
##BESTSTORY
#KALBIM

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070
Chapter 57 · 0% Book details