← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 120

Sashe 69

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruwan sosai sike sauka jikinsa jikin nasa na sake daukan jijjiga idanuwansa sunyi wani irin jan da idan da wani zaigansa a lokacin tsoro zaiji.

Azaba ce sosai yake ji a cikin kansa yafara buga kan a jikin bango da karfi kafin qafafunsa suka kasa riqesa ya silale a gurin qasa yana qanqame jikinsa har lokacin ruwa na sauka akansa.

Tsawon lokaci yana matse da jikinsa qasa kwance jikinsa na rawa sosai ruwa na sauka akansa ahankali ahankali harya nutsu yayi shiru idanuwansa a rufe wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwansa ya budesu ahankali yana ganin kamar Ummitansa na gabansa ya qurawa gabansa ido kaman itada mahaifiyarsa suna tareda shi.

Ya jima a hakan zuciyarsa na karairayewa kafin ya lumshe idanuwansa yana fatan duk suna cikin rahamar ubangiji.

Daqyar ya iya kai hannunsa ya sauya zuwa ruwan zafi ya miqe ya zare kayansa yayi wanka da tsadaddun shower liquids dinsa kafin ya zari daya daga cikin towels din dasuke jere a toilet din masu yawa sa laushi ya daura a jikinsa ya fito fararen idanuwansa da suka sauya sunyi wani iri kaman sexy dan da akwai macen da zata gansa a lokacin tabbasa zata iya kasa riqe kanta dan kallo daya zai maka dasu ka nema zarewa da neman nutsuwarka ka rasa.

Tin daga lokacinda ya Ummitah tabar duniya tabarda da wannann trauma din babu daren da baya samun kansa a wannan yanayin batareda da kowa ya taba saniba,
Shi kadai yakeshan azabarsa ya gama ya fito batareda kowa y saniba sai dr Nico wanda shine likitansa,

Azaba sosai yakesha sbd zuciyarsa haryanzu ta kasa fita daga radadi da ciwon rashin yar Uwarsa wadda sai ranar daya bar Duniya zai huta daga wannan ciwon.

Ko Sayd baitaba saniba sai daga baya bayan shekaru ya sani a wani tafiya da sukai ya samesa dakinsa da daddare akan wani issue ya tararda yana bathroom wani irin kuka da nishin dayake jine ya sakasa nufar bathroom din wanda ya tarar dashi a wannan halin,

Tim daga wannan lokacin ya san ashe AZIZ din bai warke daga trauma dinsaba sai tsananin data qara amma tsawon shekaru basu taba saniba sbd ya zabi ya boye ya ringa jin radadinsa shi kadai.

Tin daga wannan lokacin Sayd ya tsananta kaunarsa da kulawansa akan AZIZ din,
A lokuta da dama shine yakan rungumesa idan yanayin yazo masa dan sassauta masa ciwon yana hawayen radadin ganinsa a cikin wannan yanayin.

Dr Nico na iya kokarinsa akan hakan sbd shine therapist dinsa dan haka sauki yake samu sosai ana samun cigaba sosai sai gashi kwatsam Maganar kashe Ummitan akai ta bayyana wanda ya dawo da komai baya dan kwata kwata yanzu ya dena karban kokarin da akeyi akan yanayin nasa.

Tsananta yanayinsa yayi sbd yanda aka kashe Ummitah shine kisa mafi tsananin ciwo da rashin tausayi,
Abinda yake Tsananta yanayinsa a koyaushe shine yasan Ummitah zataso inama ace Allah zai bata ikon ganinsa yazo gareta,
Inama zasu tausaya mata su barta ta koma ga dan uwanta da mijinta da abinda ta haifa da mamanta,
Ya sani a wannan lokacin da suke kokarin rabata da duniya tayi hawayen azaba,tayi na rashin sanin ayau zata bar duniya,tayi na tausayinsa sbd tasan zai shiga tashin hankalin da babu ranar fita...

Tina irin wannan ne yake sakasa hawayen tausayin kansa dana yar uwarsa a kowane lokacin da yanayinsa ya taso.

A yanzu dayakeson yi musu tsanar datafi komai karfi da muni a yanxu dinne kuma zuciyarsa ke jin tsananin kaunar Zuciyar tata datake bugawa da tsananin sonsa da kaunarsa amma a wani kirjin da bana Ummitanba,
Ta tafi tabar masa bugun zuciyarta dayake tsananin son jinsa a hannunsa,
Ya tsane Jannah amma yana kaunar bugun zuciyarta tayaya zai iya barin kansa ya hada wainnan feelings din guda biyu?
Tsananin tsana da kuma tsananin kauna...
Wannan tinanin ke sakasa tsanar kansa tsana me tsananin gaske,

Amma duk da hakan bazai taba samun nutsuwa ba saiya tabbatarda Jannah bata sake dandanar farin cikin duniya ba,

Zaadens suna kallo zai mayarda rayuwar da sukafi so fiyeda komai ba komaiba,
Suna kallo zai maidata abar tausayi da baqin cikin kallo bazasu iya komaiba sbd sun riga sun daura aurenda bazasu iya rabawaba sai lokacinda ya gama da ita zai jefa musu ita a lokacinda batada amfanin komai a duniyar dan haka Auren a goben ba fashi ya karba sadakarta hakama ya bawa falaq abinda takeso itama mama ya cika mata umarninta na son yayi auren.

Su Mama kuwa hankali kwance sukam sunga hidimar farin ciki gabansu,
Baba alhassan Alh saad ya kira ya sanar masa maganar auren da babu shiri dan haka ya sanar masa goben dai sune wakilan ango.

Bayan ya kira Alh saad Alh Ahmed ya kira abokin aikin Baban AZIZ din wanda shine ya kawosa gurin su Alh saad tin lokacinda mahaifinsu ya rasu.

Shima sosai yayi farin ciki dan haka da shirinsa ya kwana yace shine zai biya sadaki Baba alhassan yace aa shine zai biya,shima Alh saad cewa yayi shine zai biya baba alhassan yace sam shine zai biya sadakin.

Qin yadda sukai sukace aa yabari su biya,
Ganin kowannensu nason ya kasance shine ya biya sadakin auren wanda sukejinsa har cikin ransu tamkar sune suka haifesa dan haka suka yadda akan kowa ya bada 500k su biya sadakin 1.5.

Baba alhassan ne yace aa sbd albarkar aure baa son sadaki me yawaba 100k kowa zai bada ayi sadakin 300k ma ya isa.

Amincewa sukai sa hakan dan haka kowannensu a cikin daren yafara kokarin buga wayoyin gayyatar jamaarsa da manyan mutane.

A cikin daren Sayd yasa aka buga wata lafiyayyar invitation ta waya a cikin daren aka fara yadawa manyan mutanensa dake kusa harma da wanda basa kusa bazasu samu damar zuwaba sbd kurewan time amma a cikin daren kafin safe maganar Auren AZIZ AY LIMBA da JANNAH ZAD ta fita anata mamakin lamarin amma dayake already Zaadens sunyi gayyata tin kafin yanzu sai ya zama mutane da yawa da manyan kasashe da dama da zasu halarta already suna abuja sun iso a ranar sbd goben sai gashi a daren suke samun kuma AZIZ LIMBA ne wanda zaa daura dashi goben.

**********
A ZADEENs kuwa AZIZ da familynsa na barin mansion din shiru sukai kowa ya kasa motsi sbd ya bude aikin da basu shirya tarbansa yanxuba.

Ammar wani irin ja idanuwansa sukai yana jin kansa da tinaninsa na toshewa kasa cewa komai yayi bayani yake jira daga duk wanda Allah ya bawa ikon fara samun dawowa hayyacinsa a cikinsu sbd yasan suma shock din suke ciki na jin zancen haukan da LIMBA yayi.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
56
Falaq farin cikine ya ciketa gabaki daya na jin Daddynta zai aura Jannah dan haka a mota qanqame hannunsa tayi tana bayyanar da farin cikinta ta kalli fuskansa da babu alamar farin ciki ko kadan a kanta tace

"I love you Daddy"

Juyowa yayi a hankali cikin nutsuwa ya saukar da idanuwansa akanta yana karantar asalin farin cikin me tsanani dayake bayyane akan fuskanta tana murmushi tana jin kaman tin yau ta tafi da jannah din gidansu.

Sayd dayake gaba shiru yayi yana sauraransu ta wani bangaren kuma shima hakan shine abinda yake tsananin so wato rabo zuciyar Ummitah daga zaadens sbd kada ta gurbata kaman yanda duka zuciyar familyn take a gurbace,
Babban fatarsa kafin su illata familyn ya zama zuciyar Ummitah tana tareda su dan haka shi wannan hukuncin shine daidai garesa kuma abinda yake jira dan haka daga lokacinda akai auren ta gama shigowa hannunsu komai ya nutsu to lokacin tarwatsa familyn zai fara duk da suna nan suna tsananin neman Dr ken wanda shi sukeson ya shiga hannunsa kafin komai sbd shine ya basu Ummitah,
Sunason Farawa Dasu dr Abraham amma kuma dole saisun fara kama dr ken sbd shine komai ya fito ta hannunsa dan haka nemansa suke sosai saidashi komai zai tafi yanda akeso.

Mama kuwa jin tayi zuciyarta kaman ta zuba ruwa a qasa tasha dan haka koda suka isa gida kasa shirin bacci tayi ta zauna tahau wayoyi.

Anty maryam ta fara kira akan lefen datakeson a hada mata na gani na fada a qanqanin lokaci.

Anty maryam na jin maganar auren farin ciki me tsanani da mamaki me girma suka rufeta lokaci daya da kuma Acikin yayanta dataita kwadayin ya auri daya amma duk da hakan farin ciki sosai tayi ta matsu goben tayi su isa LIMBAs din.

Baba alhassan ma daman yana nan har lokacin dan hana mama na sanar masa Sayd ya kira yaji komai daga bakinsa sbd AZIZ din ya shige ya hana kowa sake ganinsa sbd tsananin zafin kansa dayakeji yana jin kaman hakan bai kamata ba ga UMMITANSA to amma yana tsananin buqatan zuciyar Ummitah a kusa dashi.

Ruwa ne ya sakarwa kansa batareda ya cire kayan jikinsa idanuwansa a rufe ya qanqame jikinsa yanajin kaman kansa zai juye sbd tsananin zafin dayake tashi a cikinsa,

Yana tsananin qin Zaadens da jannah din kanta tsana me tsananin gaske da zai iya komai dan faduwarsu koda hakan na nufin su fadi tare,
Ta bagare daya yana tsananin Kaunar duk abinda ya shafi Ummitah koda qazantace indai ta Ummitah ce sonta yake da gaske,
Baitaba qi ko gudun abinda ya shafi Ummitah ba,
Ta bar duniya bazata taba dawowa har abada amma zuciyarta na duniya taba bugawa tayaya zai tsani kirjin da zuciyar Ummitah take bugawa a cikinta????

Zuciyarsa ta kasa hakan,
Ya tsani jannah tsana mafi muni a lokaci day kuma yana tsananin kaunar zuciyar datake bugawa a kirjinta....

Rawa jikinsa yakeyi sosai yana wani irin jijjiga yana sake qanqame jikinsa da karfi sbd trauma dinsa da shima babu lokacinda bata tashi idan ya samu kansa a cikin wannan tsananin ciwo da radadin tinanin kauna da tsana dake cinsa lokaci daya wanda babu wanda ya taba sanin da hakan.

Ruwan sosai sike sauka jikinsa jikin nasa na sake daukan jijjiga idanuwansa sunyi wani irin jan da idan da wani zaigansa a lokacin tsoro zaiji.
Chapter 69 · 0% Book details