← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 120

Sashe 66

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
53
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC (kayan mata)
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4200
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 6k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Na Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 6k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

************
Zubawa Daddyn nata idanuwanta duka falaq tai tana kallansa cikeda nutsuwa da tsananin son amincewansa duk da tasan bazai taba iya qin mata duk abinda ta furta tana so ba.

Cikeda wani 'daci me tsananin gaske ya hadiye abincin dayake bakinsa batareda ya kalli kowa dayake gurinba sbd yanayin bacin rai mai tsananin daya shiga amma ya hanasa bayyanuwa dan haka baice komaiba kamarma baiji abinda ta furta dinba.

Mama ce ta fara dagowa ta kallesa tana karantar yanayinsa sedai batace komaiba sbd tasan sarai yaji sedai zancen garesa kaman abune da bazai yiyu ba sbd ba auren yakeso ba baya gabansa.

Sayd ma dagowa yayi a hankali ya kallesa yana karantar yanayinsa dayafi kowa iya sanin kowane yanayinsa meyake nufi,

Zallan asalin bacin rai da zafi me tsanani ne yake hangowa a yanayinsa wanda ayau da ba Falaq ce ta furta zancenba tabbas da zaaga fushi da bacin ransa amma kwata kwata ya nade komai yabarwa zuciyarsa.

Hawayen da Falaq din ke riqewa tinda Anny ta fada mata Jan son daddynta takeyi ta sake sbd ta wani bangaren da gaske kishin daddynta ya kawo wata a rayuwarsu take sosai hakama har ranta kishin Daddynta ya haifi wasu yayan dazai raba musu tsananin kaunar dayake mata take amma kuma ta wani bangaren yanda takejin Jannah a ranta bazata iya barin ta auri waniba bayan daddynta takeso dan haka duk kanta baya komai daidai kawai Daddyn ya auri jannah din.

Gangarowa hawayenta sukai wanda na daddynta zai hada kaunarta da wani ne sai kuma kaunar datake wa jan sune suke fada a zuciyarta.

Kuka kawai ta fasa wanda ya sakasa ajiye spoon din hannunsa batareda ta juyo ya kalletaba sbd nauyin da kirjinsa ya qara akan maganarta da kukanta dayake shiga kunnensa.

Yana ajiye spoon dinsa Sayd ma duk suka ajiye nasu sbd yanayin ya sake daukan zafi.

Kuka takeyi sosai mara sauti sosai wanda ciwo ne takeji a ranta amma amincewansa kila ta rage mata ciwon datakejin.

Hannu ya miqa ya zari tissue ya goge bakinsa tareda miqewa yabar gurin sbd zuciyarsa zata iya riqe komai na duniya bazata iya riqe sauraron sautin kukantaba.

Miqewa Sayd yayi yabi bayansa yana zarar tissue shima ya goge baki.

Suna ficewa mama dawo da kallanta tayi kan falaq din dake kuka sosai wanda kwata kwata rayuwartama batasan kukan damuwaba indai ba kafin ta girmaba datake kukan daddynta idan yayi tafiya.

Fiddausi ce ta shigo tana rarrashinta tareda lallabata taci abinci amma taqi ci sam.

Mama ma lallabata tayi sosai akan taci din ai zai aura jannah din insha Allah dan itama tanason jannah sosai a matsayin sirikarta.

Miqewa tayi tabar dining din tana kuka sosai tana cewa gurin Jannah zata.

Mama na jin hakan ta kalli Fiddausi dake kokarin bin bayanta tace

"Shirya kuje tinda tace zata gurin jannah din kila ta samu acan ta rarrasheta taci abinci,
Ku tabbata taci kada abarta da yinwa"

Gyada kai Fiddausi tayi tana bin bayan falaq din da sauri tana ambatar sunanta cikeda tsananin kulawa da kauna.

Fitowa tayi bayan ta sako mini hijab akan riga da skirt din tsadaddiyar atampar datake jikinta.

Fiddausi daman doguwar riga ce a jikinta ta abaya me kyau da hula dan haka dakinta ta nufa da sauri ta dauko veil din rigar ta fito tabi bayanta.

Sayd dayake tareda AZIZ a palonsa ya kasa cewa komai kiran latif ne ya shigo wayarsa yana dauka latif din yace

"Ga Ms Falaq Aziz nan tace zaa kaita zaadens,a tafi din? Da izinin Sir LIMBA??

Kallan AZIZ din sayd yayi yana bude baki a tausashe da girmamawa zai sanar masa AZIZ din dayaji abinda aka fada dakatar da sayd din yayi da alamar a kaita sbd tashin hankali zataita yi idan aka hanata taxo ta samu wani ciwon.

Mayar da wayar kunnensa sayd yayi yacewa latif

"A kaita amma kada takai dare a dawo dasu"

"Ok insha Allah"

Shiga motar yayi ya tada aka bude musu gate suka fice daga gidan zuwa zaadens.

Koda suka isa a zadeens komai ya fara daukan zafi sbd a daidai wannna lokacin Dad ya kira jannah palonsa daga shi sai ita cikeda kulawa ya zaunar da ita kusa dashi ya dafa hannunta cikin kulawa yana kallan yanayinta na sanyi da rasa walwala da duk tayi.

Karyewa zuciyarsa tayi yana jin jarabawansa shi kam akan 'yarsa ce,
Allah ya riga ya jarabcesa da mata kaunar datafi komai,
Akan farin cikinta da bata kulawa da inganta rayuwanta babu abinda bazai iyaba,
Itace babban weakness na rayuwarsa data ahalinsa gaba daya,
Ko mahaifiyar data haifeta idan zama da itane rashin walwalan yarsa tabbas zai iya sallamarta batareda second tinaniba bare aura mata wanda zuciyarta bashi takewa son aure b da qarasa rayuwarta sedai kuma bayajin zai iya barinta aure a wani gurin me nisa ko a cikin familyn da basu dace da rayuwartaba sbd itace hasken idaniyar ahalinta dan haka duk inda zataje aure sai inda zaa tattalata kaman yanda ake tattalinta a gidansu ga kuma yanayi na zuciyarta dayake jin tsoron aurenta wani gurin a sakata bacin ran da zata iya samun matsala dan haka a wani bangaren kwata kwata baya kaunar ta auri wani wanda ba Ammar dinba sbd zasu cigaba da zama a cikinsu ne.

Dago idanuwanta tai itama ta kalli dad din wanda yake tinani kafin ya bude baki a natse cikin kulawa yace

"Jan Zad karki boyewa Dad dinki komai,
Banda kowane irin kwanciyar hankalin dayakai na ganinki a cikin farin ciki da walwalwa tareda samun kwnaciyar hankali,
Karki manta you are my one and only princess,
My beautiful and brave girl,
Remember you don't hide anything from your dad tin kina qarama right??

Gyada kai tayi jikinta na tsananin sanyi
Yace

"Jannah kinason auren Ammar kokuwa kina buqatan a baki time ki sake tinani??
Kina sonsa ne kawai as brother bakya masa soyayyar aure??"

Wani irin nauyin gaske dayake danne da kirjinta tsawon lokaci taji yana warwarewa ahankali idanuwanta na cikowa da hawaye sbd kunyar Dad din data kanta akan Zamowant kaman butulu ga soyayyar Ammar data taso a cikinta.

Gangarowa hawayenta sukai tana rufe idanuwanta tana jin soyayyar wanda baimasan tanayi ba mai karfi da ciwon gaske,
Ta laluba,ta shiga tinani,tayi kukan tayi binciken inda soyayyar Ammar ta bace bat a zuciyarta ta rasa ya akai...

Sanyi jikin dad yayi sbd kenan dai ta tabbata da gaske ne ba son auren Ammar din takeba.

Wani sarawa yaji kansa yayi sbd wannan wata sabuwar qaramar masifa ce zata qullu dan tabbas Ammar zai tabu,hakama shi bazai iya barinta aure wani gurinba sedai zaman gidan kenan dan bazai bari taje auren wani guri ba tinda ba lafiyayya bace a kashe masa ita a banza dan haka yaya kenan.

Maheer ne ya shiga tareda rufe kofar palon yana kallan Jannah din dake kuka mai tsima zuciya sosai kan qasa ta kasa kallan dad din sbd kunyar itace take tsananin son wanda ko a jerin mutane bai gama ajiyetaba take ganin.

Zaunawa Maheer yayi gefenta yana tausasa murya yace

"Da gasken kenan bakyason auren??
Meyasa Jan?
Ammar tin kina fadowa duniya yake miki tsananin so,
Meyasa duk wannan shekarun baki bawa zuciyanki daman sonsa ba sai yanzu da komai yazo qarshe zaa muku aure??

Girgiza kai tayi cikin tsananin takaicin kanta da sanyin jikin da batasan itama ya zataiba tace

"Bansaniba,wlh inasonsa ina sonsa sosai inason aurensa bansan meya sameniba yanzu,
Bansan meyasa ba,
Zan auresa bazan iya kasa aurensaba sbd inason nasosa kaman yanda yakeso na amma zuciyana ta kasa hakan,

Kallan dad tayi wanda jikinsa ya qarasa mutuwa tace

"Dad zan auresa,
Shi zan aura bazan taba iya fasa aurensa ba dan Allah kada abari yasan laifin da zuciyana tai masa na kasa saka sonsa a cikinta duk da a baya nasan shine yake cikin zuciyata shi kadai.....

Katse Maheer yayi da cewa

"Idan a baya kina sonsa meya faru da yanzu din Jan??
AZIZ LIMBA ne????

Rintse idanuwanta tayi da karfi hawayen cikinsu na sake gangarowa ta zame qasa tana cusa kanta cikin qafafunta tana kasa cewa komai sbd abin daman ya isheta ita kadai take neman bugawa batareda fidda maganar ciki da zuciyarta ba.

Dad kuwa da sauri ya kalli Maheer lafin ya kalli jannah din wadda ta sakasa sake shiga tsananin shock yace

"LIMBA kuma?
Shi takeso?
Are they inlove with each other ko me?

Numfashi me zafin gaske Maheer ya sauke yana cewa
Chapter 66 · 0% Book details