← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 120

Sashe 74

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka jannah din ta fasa wanda ta rasa na menene amma dai tasan tsananin tausayin Ammar bazai taba barintaba har abada da kuma kaunar da suka taso a cikinta ta kusanci da shaquwa.

Anny da maheer ma basu samu cewa komaiba sbd ganin Mimi ta daure fuska sosai suka juya suka bar gurin zuciyar Anny fes.

Acan palo kuwa Sun fito sun fice sunbar zaadens din zuwa gida wanda Falaq ta matsu daddynta ya dawo sbd yau itace ta tayasa shirin daurin aurensa ta rakasa har mota tana jin kaman ta hanasa zuwa gurin daurin auren ya wuce ya dauko mata Jannah din kawai ya fara kawowa nan.

Suna isowa Falaq ta fito da gudu Fiddausi tayi saurin riqeta tana hanata gudun sbd kada matsala ta biyo bayan gudun.

Yana fitowa motan da sauri ta qarasa gurinsa ta fada jikinsa tana cewa

"BestDaddy ya zama nawa nida Jan"

Dariyar zancenta Baba alhassan yayi yana cewa

"Wannan baturiya bata da hausa ko kadan sai iyayi da surutu"

Sayd ma dariyar zancen nata yake yana cewa

"Aa daya a cikinku dai zai daukesa"

Sake qanwamesa tayi tana cewa

"No,Tin farko har karshe nawa ne ni kadai yanzu ne dai na yadda ya zama namu mu biyu da My jan sai kuma babies biyu da kawai nakeso ta haifo mana sun isa banason na bawa Daddyna da yawa"

Kallanta AZIZ din yayi da idanuwansa yana mamakin yanda haryanzu ta kasa wayo duk da girmanta.

Sayd tsokanarta zai sake yi AZIZ ya kallesa saiya fasa fadan abinda zai fada yana dariya yace

"6 mukeso"

Da wani irin tsalle ta kallesa tana dawowa da kallanta kan Daddyn zatai magana ya girgiza mata kai ahankali alaman Ba haka bane kafin ya kalli Sayd din yana cewa

"Zaka rikitamun ita ko?"

Dariya sosai Sayd ya sake yana shigewa palo yana cewa

"Ba ruwana a bakin mama naji,
Kuma ashe da gaskiyan mama wata a gidan nan batada wayo sam"

Jin sunan Mama ce ta fada hakan kallansa tayi da sauri sbd tasan baya wuce umarnin mama daidai suna shiga palon tace

"Daddy d gaske kanne har 6 zaka mun??

Mama dake fitowa dakinta cikin mamaki tace

"Ke bakinki komai fada yake ko??
Uban naki kikewa wannan tambayar?

Tura baki tayi tana son amsarsa sbd jin tayi kaman ma batason ko guda daya zatai magana magana

Mama tayo kanta da gudu tayi bayansa tana cewa

"Ni banason ko daya ma na fasa abarni daga ni sai Jan mun isa"

Mama sake kallanta tayi zatai magana ya bude baki yana janyota gabansa yace

"Babu wanda zai zo ya dameki da daddynki,
Amma karki sake maganar nan kwata kwata ok??

Gyada masa kai tai tana dawowa mood dinta na baya tace

"Daddy yaushe Jan zata taho?
Yau?
Anjima?
Wat time?
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
60
*TALK WITH SIDDEEQAH*
Operation Ciniki Dole
08149588205
Ni Olayyah na shiga uku na kwashe kudi na saro kaya domin in fara kasuwanci online, na gaji da zaman sai Yallaɓai ya bani kudin kashewa, kullum ni ce koma baya cikin danginsu, dukda yana kokarin sa, amma dai gwara in nemi na kaina kodan yan uwa da iyaye.

Amma bari in kira Besty nah Huriyyah nasan zata samu maganin wannan damuwar tawa.
Tunda na kira Huriyya na faɗa mata abunda ke hanani Bacci ta faɗa mun wani sirri da ya girgizani.

Wato ashe itama da ta fara business online kuma bata ciniki amms tunda aka bata number din Coach Saddiqah komai ya fara tafiya daidai a kasuwancin ta ( Talk with Saddeeqah).

Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba, gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.

Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.

Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan 90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.

*************
Kallan fuskanta yayi yana sake ganin doki da murnan dabai saba ganinta dashi ba idan baa kansaba,

"Meyasa take tsananin kaunar wadda bai kamata ta kaunata din ba" shine tambayar da zuciyarsa take masa yana kallan Falaq din.

Sake riqe hannunsa tai tana cewa

"Daddy pls yaushe ne zata taho?"
Kaine zakaje ka daukota?
Ka aikani na dauko ta yanzu pls BestDaddy"

Numfashi ya sauke yana shafa fuskanta yanajin kaunarta na sake ratsasa,
Ayau zuciyarsa cikin tsananin qunci da daci take sbd kaddarar auren daya shiga tsakaninsa da familyn da bai hada tsanarsu da komaiba amma ganin farin cikin dayake fuskan Falaq wanda daga zuciyarta yake fitowa saiyaji ya dan samu sassaucin tsananin dacin dayake ransa.

Bude baki yayi cikin kulawa da nutsuwa yace

"Karkiyita murna da yawa tareda tsalle tsallen nan banason wasa da lafiyanki kin sani so ki kula sosai okay?

Gyada kai tayi tana cewa

"Zanyi amma daddy pls when zata taho?

Bai amsa tambayarba ya wuce palonsa yana jin mama na kiranta.

Yana shigewa cire babban rigan jikinsa yayi tareda zame kayan duka sbd ya samu sakewa.

Wani wankan ya sake yi ya sauya kaya zuwa qananun kayan D&G bai fitoba ya kashe wayoyinsa dan hutawa.

Su mama kuwa bikinsu sukeyi cikeda farin ciki da kwnaciyar hankali sbd su anty maryam duka da iyalan Alh Saad din dana Alh Ahmed duka suka gidan anata taya mama murna.

Sayd ma shigewa yayi dan hutawar sbd Uban gidansa na hutawa ba wani aiki.

Dayake Fahad ma a mansion din ya sauka shi kam yana cikinsu mama da mutuniyarsa falaq kafin daga baya ya fita zuwa wani guri.

***Karfe 4 da mintina Ammar ya farka yana fara motsawa Mimi da jannah dake dakin har lokacin sukai saurin yi kansa mama na ambatar sunansa tareda kamasa ya tashi zaune ta rungumesa da sauri hawaye na gangaro mata na tsananin kaunarsa me karfi da tausayinsa.

Jannah ma hawayen ne suke gangaro mata tana kasa dagowa ta kallesa tana jin tsananin tsanar zuciyarta data kasa riqe amanar shekara da shekaru,
Ammar bai cancanci hakan daga gareta ba,
Taci Amanarsa taci amanar kanta sbd ta sani har abada wanda aka aura mata din bazai taba sonta kamar Ammar ba wanda zai iya vada rayuwarsa akanta.

Kansa da yayi masa tsananin nauyi da zafi ya dan dafe kafin ahankali ya bude idanuwansa da sukai jajir alamar baccin dolen da aka sakasa zuciyarsa bata hutaba ko kadan.

Akan jannah ya saukar da idanuwansa ya kafesu akanta yana mata wani irin kallo zuciyarsa na karban wani azababben yanayi me tsananin ciwo da radadi,
Tinda Allah ya saka masa tsananin son jannah tin tana cikin mahaifiyarta har isowanta duniya da gwagwarmayar neman lafiyarta zuwa yanzu bai taba kawowa ko a mafarki ko tinanin Jannah zata iya zamowa matar wani ba duk duniya bayansa,

Da ransa da lafiyarsa da hankalinsa da tinaninsa aka daura auren jannah da wani yana kwance yana baccin Asara da baqin cikin da aka sakasa sbd cimma buri batareda an dubi nasa halinda zai shiga ba a rashinta....

Rintse idanuwansa yayi sbd wani irin radadin daya yanki zuciyarsa da kirjinsa yana kasa riqe radadin ya rintse idanuwan.

Mimi jin saukan hawayensa masu wani irin tsananin zafi taji a bayanta wanda tajisu tamkar sun sauka a zuciyarta ne dan haka bata san lokacinda ta fasa qaramin kuka me sautiba dan tasan babu a duniya abinda zaa fadawa Ammar din akan wannan lamarin ya sassauta radadinsa,

Anyi masa illar da har abada bazai warke ba sedai samun sasssauci,

Jannah ganin hawayensa zubewa tayi qasa tana fasa kuka itama tana son ambatar sunansa amma baqin cikin kanta datakeji ya hanata fada.

Gangarowa hawayensa keyi ahankali akan bayan Mimi datake rungume dashi kafin jikinsa ya fara rawa ahankali yana kakkarwa ta sake qanqamesa da karfi tana girgiza masa kai tana cewa

"Ammar no pls,
No pls, karka bari ka shiga wani hali zuciyana bazata iya daukaba"

Dad ne ya bude kofar dakin ya shigo Maheer na bayansa suna ganin ya farka suka qaraso kowannensu idanuwansu na kansa.

Yanayinsa ya saka Maheer saurin isa garesa ya janyosa jikinsa ya qanqame yana kokarin hana jikinsa jijjigan dayake yana jin zuciyarsa na karyewa.

Dad ma qarasowa yayi daidai lokacinda Ammar din ya rikice gabaki dayansa komai na jikinsa rawa yake idanuwansa a rintse yana sake qanqame Mimi maheer kuma na sake qanqamesa.

Cikin sauri Dad ya kalli saleem daya shigo dakin yace ya kira dr.

Da sauri saleem ya ciro wayarsa yana kokarin saka kiran.

Daddy mahmoud ma qarasowa yayi dakin cikin damuwa da kulawa yana kallan Ammar din yace Maheer ya cire masa Cardigan din dake jikinsa.

Mimi da maheer dinne suka cire masa a lokacinne jikinsa ya sake gaba daya.
Chapter 74 · 0% Book details