← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 120

Sashe 114

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sbd kanwarsa dad dinsa ya rabu dashi ya kuma amsa hakan dan haka shima dan gwagwarmaya ya tashi sbd kanwarsa wadda bata taba sanin ba uba dayane ya haifesuba sbd dad dinsa ya rasu shima daga baya kaman yanda itama nata ya dade da rasuwa,

Ya taso vaida buri baida fata saina ingata rayuwar Nicki,
Ya samu daukaka daci gaban rayuwa bayan hardships da dama,

Nicki ta taso cikin tsananin gatan daya reneta a cikinsa,
Bata san komaiba bayan jin dadi da gata da tsananin kauna daga yayanta wanda yake komai sbd ita,

Tayi karamin karatunta a italy kafin daga baya ta tafi America cigaba da karatu,

Acan ma rayuwar jin dadi da hutu takeyi tareda gata me yawa duk da bata tareda yayanta wanda itama da sunansa take amfani,

Nicki ta taso da wani irin yanayi na idan tanason abu bata yadda ko kadan wani ya rabesa,

Bata yadda duk abinda takeso wani ya samesa ko ya tabasa,

Tin tana yarinya take da wannan halin wanda ya saka yayanta yaqi sosai akan hakan sbd kaman yana taba kwakwalwanta dan hakanne ya tsaya sosai akanta sedai kuma hakan ya riga ya zama a jininta da cikin kanta ne,

Tanada wani irin kishi akan komai nata koda kuwa abin wasa ne harta girma,

Aurensa biyu yana rabuwa da matan sbd Nicki wadda ta kasa iya rayuwa dasu,

Sbd tsananin kasa yadda da kowa ya rabi abinda yake nata ko take so Nicki zata iya attempting kashe kanta batareda tinanin komaiba wanda wannan shine babbar matsala da dr Nico yake fuskanta a tasa rayuwar sbd Nicki,

Asalin mahaifin Nicki musulmi ne dan haka tana girma Nico ya sakata a musulunci batareda cutatarwa ko qyama ba kuma itama ta zaba hakan sbd akwai son musuluncin a zuciyarta dan haka ta tashi dag Nicki sai ta koma AYSH NICKY NICOLAS,

Aysh nicky tana karatun likitanci kamar yayanta kuma tana gap da kammalawa dan haka dawowan yayanta Germany ya sakata dawowa gida daya dashi tinda ta kusa kammalawa sai tana zuwane tayi kwanaki ta dawo gida gurinsa.

****Kwanan Limbas daya da sauka a Germany Dr Nico ya iso gidan sbd duba AZIZ wanda har lokacin bai warware yanda y kamata dan haka a lokacinda AZIZ LIMBA ya fito palon da dr nico din yake tareda mama da Aysh Nicki suna gaisawa da mama
Kaman a mafarki Aysh Nicky ta dago idanuwanta masu haske ta sauke akan AZIZ LIMBA wanda baisan da ita ba kwata kwata a gurin tana jin hankalinta na zarewa ahankali ahankali yana barin jikinta tareda dukkanin abinda yake zuciyarta batareda ta dauke kallanta akansa ba.

A daidai wannan lokacin ne shi kuka sayd kiran saleem zad ya shigo wayarsa da Saleem yaje gurin latif ya samu yana dauka babu abinda saleem din ya fara fada masa sai

"Zan zama donor din da kuke nema akan zaku kashe case din zaadens su samu freedom dinsu su samu damar gina wata rayuwar me tsafta"

Cak komai na jikin Sayd ya dena aiki yana shiga shock din jin zancen wanda yasan har abada AZIZ LIMBA bazai taba yadda karban rayuwar wani kai tsaye bawai donor din daya cancanta ba wanda yake na wainda sun riga sun mutu a gangar jiki ne hakama bazai taba iya karban Zuciyar saleem ya rabasa da duniyaba sbd raya tasa yar to amma kuma falaq na tsananin buqatar zuciyar......

Shiru yayi yana kasa cewa komai sbd abune da baima isa yajewa AZIZ dashiba amma kuma koma menene yana buqatan Saleem din a kusa dan haka kai tsaye ya saka latif yayiwa saleem din komai na tahowa Germany batareda sanin AZIZ ba amma shima kansa bazai taba iya taba zuciyar Saleem ba sbd raya tasa 'yar amma dai zaiso zuwansa din idan har zai zama donor din dayake fada din.

*****************
Jannah kuwa yau daga kotu da aka fito tafiyar kafa takeyi me tsananin tsayi cikin rana harta iso inda wata qaramar kasuwa datake kamar tasha a cike mutane kala kala da baqi da wainda ba baqin ba.

Neman guri tayi a nesa da hayaniya ta zauna ahankali tana rufe idanuwanta da sukai jajir ta budesu tana hadiye yawu maqoshinta daya bushe.

Ruwa takeso batada kudin siya dan haka ta sake saka hannunta a cikin aljihun doguwar rigar dayake jikinta ta taba ko zata dace da canji tinda haka take tana mantawa da canji a jikinta sbd damuwa da rashin sabo da rayuwar.

Nera hamsi ta samu wadda ta sakata sauke ajiyan zuciya da sauri tana miqewa ta isa gurin me ruwan pure water ta siyo guda daya 50 naira ta dawo ta zauna inda ta tashi ta fasa ruwan zata saka a bakinta wata mata datake tsananin son ruwan itama ta zauna gefenta tana jan numfashi daqyar bakinta a tsananin bushe idanuwanta sun qanqance.

"UMMINAH ZAN RUWA NIMA"

juyowa jannah tayi da wani irin yanayi na faduwar gaba sbd sautin muryan da haka kawai ya saka gabanta faduwa ta saukar da idanuwanta akan matar.

Tsakiyar idanuwanta matar ta kalla itama idanuwan matar ne suka saka ruwan hannunta subucewa tana jin kallan matar na sake saka gabanta faduwa.

Ganin numfashin matar na neman barin kirjinta yasaka daukan ruwan da sauri tayi kanta ta saka mata a baki tana tallafota jikinta.

Shan ruwan matar tayi tana dafe cikinta dake tsananin ciwo kafin me sai amai sosai tafara yi a jikin jannah din wadda tsananin tausayinta ya sakata tsayawa kallanta.

Tana gama aman jannah ta wanke mata fuskanta ta miqe zata tafiyarta matar ta saka hannunta daya ta riqe jannah din tana cewa

"Umminah karki barni,
Umminah"

Dakatawa Jannah tayi tareda juyowa idaniwanta na cikowa da hawaye taji tana kasa tafiya tabarta sbd kaman yanda matar ke neman umminta itama Miminta take nema a wannan gararriyar rayuwar datake ita kadai dan haka ta durquso ahankali ta bude baki tace

"Ba ummi bace"

Riqeta matar tayi da karfi tana girgiza kai a wahalce sbd karfinta daya qare tace

"Ummina,karki barni ummina,
Ki kaini gurin hamma,
Umminah karki barni har abada bazan dake barinki ba duk wuya"

Hawaye ne suka gangaro daga idanuwan jannah din tanajin zuciyarta na tsananin karaya tanajin bazata iya barinta dan haka ta kamata suka miqe taja hannunta dik da dukkaninsu babu me karfi matar ta qanqame hannun jannah kamar zata maidata cikinta suka bar gurin batareda ma sun san ina suka dosa ba.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
94
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

***********
Hanyar gida suka nufa Jannah na sake bude fuskan matar da kyau daga hijabin dayake rufe fuskanta sbd ko akwai wanda zai ganta daya santa ya tafi da ita gida sbd tana tsoron tafiya da mahaifiyar wasu gurinta azo ana nema karshema aga laifinta da daukanta.

Tafiya suke sakeyi me tsayi matar na sake riqe hannun Jannah cikin nata sosai kamar itace karamar yarinya jannah kuma uwarta,

Yanda take qanqame hannun jannah din cikeda tsananin kauna da kasa iya barinta ya saka jannah juyowa da jajayen idanuwanta ta kalleta tana jin inama hannun tata mahaifiyarne take riqe dashi a hakan da tabbas dukkanin quncinta da baqin cikinta ya yaye.

Gap da magrib suka isa gidan zuwa lokacin dukkaninsu sun tsananin gajiya dan haka zaunawa jannah tayi a tsakiyar dakin bayan ta shiga toilet ta debo musu ruwa a fanfo tafara bawa matar wadda tasha sosai itama sha tai ta xauna tana hutawa ahankali kafafunta na wani irin radadin gajiya.

Sallah akai har aka fito masallaci tukuna ta iya tashi ta nufi toilet ta shige tayo Alwala ta kama matar itama takaita toilet da taimakonta tayi komai suka fito tare suka tada sallah sai yazamana kamar itace take jagorantar matar sallah sbd yanda ta ringa binta.

Suna gamawa abincin data bari na cin darenta kafin ta fita ta janyo ta ajiye musu a gabansu ta kama hannun matar ahankali ta saka mata a ciki tana bude baki Ahankali tace

"Kici abinci"

Zuba mata idanuwanta masu tsananin kama dana 'yayanta matar tai cikeda kaunar jannah din da batasan ta inda take kwararo mata ta bude baki da muryanta me bayyanarda batada cikakkiyar lafiyar kai tace

"Umminah kici,
Umma tace kici"

Dagowa jannah tai da idanuwanta dake sauyawa sbd yanda tai maganar kaman Mimintata take taji kewar uwarta idanuwanta suka ciko da hawaye suna gangarowa ahankali.

Hannuwan Umman rawa suka dauka ta dorasu akan fuskan jannah tana goge mata tana cewa

"Umminah bata kuka"

Tsananta gudu hawayen jannah sukai tana rife idanuwanta ahankali tana tana share mata hawayen hankalinta na tashi jikinta na rawa sosai.

Rikicewa Umman ke neman yi kanta na juyewa wanda ya saka Jannah bude idanuwanta tana dago hannunta ahankali ta dora akan na Umman dayake kan fuskanta tanata goge mata hawayen ta bude baki Ahankali tace

"Jannah ce,jannah ce ba ummi ba,
Ummi bata nan........

Bata qarasa ba Umman tayi baya da sauri tana kama kanta da hannuwanta biyu tana buga sosai tana girgiza kai da karfi koina jikinta na rawa tana cewa

"Umminah zata kaini gurin hamma,
Idan ba Umminah bace ki kaini gurin hamma,
Gurin hamma nakeson zuwa,
Ina hamma Abdul dinmu nida Umminah,
Hamma yana can yana fada kullum mun fita yawo,
Ya hanamu yawo,
Ki kaini gurin hamma na fada masa Umminah batanan..."
Chapter 114 · 0% Book details