← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 120

Sashe 32

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
25
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

*********A ranar da Ummitah tabar duniya ana ficewa da gawarta asibitin a lokacin aka shiga aikin JANNAH ZAADEN wadda aka shiga da ita iyayenta na kofar dakin tiyatar suna hana kunnuwansu daukan sautin ihu da karar kukan yan uwan Ummitah dake cikin tsananin quncin rashinta
Suna maida dukkanin hankalinsu da nutsuwarsu tareda fatarsu akan samun nasarar da zata bawa Jannah sabuwar rayuwar da suketa gwagwarmaya akai.

Dukkaninsu basu taba shiga tsananin lokaci irin wannan ba a rayuwarsu na jiran dayake saka zuciyoyinsu muguwar bugawan da babu wanda jininsa bai iya hawaba a lokacin.

Securities ne a zagaye da gurin amma sam basu bari hakan ya zama obvious ba amma kwata kwata ko motsin komai bakaji a gurin.

DZAD,DADDY MAHMOUD,MIMI,MOMMY(matar daddy Mahmoud),LUBNAH(yar riqon mommy) sai Maheer wanda ya kasa zama time kawai yake calculating yana jin maqoshi nsa na bushewa,sai Saleem wanda shima yake jin kaman ya shiga dakin tiyatar ya ganowa idonsa ko zai samu sassaucin abinda yake ji.

Dukkanin familyn suna zaune ne babu wanda zuciyarsa ba bugawa takeyi ba da sauri da kuma faduwar gaba.

Su mimi basusan meya faruba kawai abinda suka sani shine an samu donor wanda yayi a lokacinda suka cirewa Jannah rai dan haka suke fatar a dace sbd daga baa dace dinba shikenan wannan karan jannah zata zaka tarihi a rayuwarsu sbd ta lokaci da ake tinanin nata yayi yayi din.

Wutar kofar dakin da aka kashe ce ta saka dukkaninsu miqewa tsaye idanuwan Mimin na gangarowa da wasu hawaye masu dumi.

Dzad kuwa jajayen idanuwansa ya dago ya kalli kofar kirjinsa na wani irin nauyin daya sakasa dafe kirjinsa har Maheer na saurin riqesa.

Daddy mahmoud ne yayi karfin halin bude bakinsa yana kallan Ammar daya fara fitowa idanuwansa jajir wasu hawayen farin ciki na gangaro masa,

Kallo daya yayiwa Mimi hawayensa suka qara gudu baice komaiba ya ware Hannuwansa ta fada jikinsa ya rungumeta da Qarfi.

Dr Abraham ne da Anny suka fito a tare tana zare maska dinta tana kallan mijinta itama cikin farin cikinta dayake bayyane.

Dr Abraham cikin sauke numfashin shekarun fama ya zare mask dinsa Yana kallan Dzad yace

"It was a success atlast sir"

Kuka Mimi ta fasa me sauti tan qanqame Ammar wanda shima yake hawaye yana dariyan farin ciki.

Maheer Anny ya warewa hannuwansu ya rungume yana cewa

"ALHAMDULILLAH"

Dad Zuciyarta kusan kasa daukan farin tai ya zame ya zaune kirjinsa na masa nauyi.

Daddy Mahmoud dr Abraham ya miqawa hannu fuskansa cikeda farin ciki yana masa godia tareda kyautar data saka dr Abraham din sake miqa masa hannu cikin farin ciki.

Saleem ma Dad ya rungume yana cewa

"ALHAMDULILLAH Dad"

Dad kasa magana yayi kirjinsa ya riqe dole akai gaggawar nufar dakin hutawa dashi dr Finn zai dubasa.

Fitowa akai da Jannah a gado ana turawa cikin nutsuwa ahankali dukkaninsu suka miqe tsaye yana zuba idanuwansu akanta zuciyoyinsu fal farin ciki da fargaba tinda ba ganinta sukai ta miqe ba.

Kyakkyawan fuskanta data rame sai dogon hancinta dayake a tsaye dukkaninsu suke kalla suna godewa Allah da ganin wannan rana.

Bayanta suka dunguma zuwa private dakin da aka nufa aka kwantar da ita dr Abraham da Ammar suka qarasa dukkanin abinda zasuyi da rubuce rubuce da komai Dr Abraham ya fice shima Ammar wucewa yayi ya nufi gida sbd kwanansa biyu a asibitin bai fitaba.

Gida ya nufa dan wanka da cin abinci da samun nutsuwar dayake jin a shekaru bai samuba.

Suma Mimi godia suka ringa yiwa Allah Mimi nayiwa Wanda zuciyarsa take jikin Jannah din tareda danginsa kaf da fatar zata samu damar saninsu tayi alkhairin da bata taba yiba arayuwarta dan kuwa zata tattara duka gwalagwalanta ta basu koda kuwa sunada arzikin to su qara sbd batada abinda zata biyasu dashi duniya da lahira.

******ABDULAZIZ duk yanda yaso yayi magana dasu Ummitah abin ya gagara sbd wayar Ummitah bata shiga,ta mama tana ringin baa dagawa ta sayyid ma bata shiga,

Alh saad yace masa suna nan lafiya hakama anty maryam idan ya kirata akan yanason magana dasu magana daya take fada masa data Alh saad din.

Kwata kwata yau kwanaki biyar kenan yana wani irin ciwon dabai san meyake damunsa ba haka kawai ciwon kirji da zuciya yake har jiri sai yana dibansa wanda daga karshe dole yaga dr karshe admitting nasa akai likita yace stress ne da damuwa kawai daya sakawa kansa.

Sosai ya kwana asibitin wanda ya saka likita hanasa ko taba wayoyinsa aka kashesu.

Amma hakan kusan hana zuciyarsa samun nutsuwa yayi wanda yake jin yana rasa nutsuwarsa da hankalinsa kwata kwata dole doctors suka basa wayarsa dan yayi magana da familynsa dan samun nutsuwa.

Wayarce gabaki daya ta kasa samuwa yanda yakeso sbd a cikin mutum uku da suke familynsa kwata kwata ya kasa jin ko daya dan haka kai tsaye ya nemo numbern drivernsa Latif wanda yake bayerabe ya saka kira.

Kiran na shigowa wayar latif gabansa yayi mummunan faduwa sbd bai kira yayi masa gaisuwaba sbd tsoro da tausayin halinda yake ciki jin rasuwar Sanyin idaniyarsa dama su gaba daya tinda suna sonsa dole sike kaunar Ummitan sosai.

Tana gap da katsewa ya daga kiran cikin tsananin sanyin muryan data saka ABDULAZIZ din sauke ajiyar zuciya.

Gaidasa Latif ya fara cikeda girmamawa yana rasa ta inda zai fara masa gaisuwa.

Kafin ya amsa gaisuwarsa kai tsaye da muryansa datai kauri kirjinsa a toshe da bacin ran yanda kowa a gida wayarsa ta koma kaman batada amfani a taqaice yacewa latif

"Inason magana da mama,Sayyid or Ummitah ka kaiwa daya daga cikinsu wayar........

Tsabar rudewa Latif da yarensa yace

"Sir you say???

Cikin hade fushinsa yace

"Do i have to repeat wat i said??

Da sauri latif na qarasa ridewa ya nufi cikin gidan yana hada gumi yace

"Yes,no no sir"

Duk ya rikice ya rasa me zaice jin sunan Ummitah dan haka ya qara sauri zuwa cikin gidan yana godewa Allah dabaiyi saurin yi masa gaisuwaba yafara ji daga bakinsa..

Yana knocking kofa fiddausi dake palo tana hadawa Baby madara tanata kuka me qarfi ga mama tana sallah Sayyid ma yana masallaci ta taso ta bude kofar wanda ya bawa ABDULAZIZ saukan kukan babyn kai tsaye cikin kunnuwansa daya sakasa tashi ahankali daga zaunen dayake zuwa tsaye yana dago wayar daga kunnuwansa ya kalla ya sake mayarwa yayi shiru kukan babyn me qara yana shiga kunnuwansa sbd tana hannun Fiddausi data taso ta bude kofar tana kallan Latif daya miqa mata wayar da sauri muryansa har tana rawa yace

"Sir na son magana da Mama or oga Sayyid and......

Shiru yayi yana kallan babyn da sai alokacin ya tina da Sir din zaiji kukanta.

Fiddausi na jin abinda ya fada tayi baya tana qin amsar wayar ta juya da sauri dan kiran mama.

Hanata tafiya latif yayi yana gwale mata idon ta karba kada tai masa haka dan yasan yana saka wayar a kunnensa maigidan zai iya jeho masa kowace irin tambaya.

Fitowan mama tana idar da sallah batareda ta tsaya addua ba sbd kukan babyn ya saka latif saurin jeho qafa palon da sauri ya miqawa mama wayar tana amsa ya juya da sauri.

Fiddausi ma barin palon tayi jikinta a sanyaye.

Mama saida wayar ta shiga hannunta ta gane waye akai take qafafunta sukai sanyi daidai lokacin sayyid ya shigo palon hakama Babyn a lokacin ta sake fasa wani kuka me qarfi na jirirai sabuwar haihuwa ba kakkautawa wanda hake shiga kunnuwan ABDULAZIZ direct yana wucewa zuwa zuciyarsa da bugunta ya sauya ya kasa cewa komai sbd yanda yakejin kukan babyn har cikin tsakiyar zuciyarsa ya tabbatar masa da kukan babyn Ummitah ne.

Shiru dukkaninsu sukai har Sayyid wanda yaga sunan SIR LIMBA akan wayar hannun mama ya san shine take jikinsa yayi mugun mutuwa radadin zuciyarsa na dawowa sabo.

Shirun lokaci mai dan tsayi sukai kafin ya iya bude bakinsa da yayi masa nauyi jin bazasu fada masa komaiba bayan sunsan yaji kukan babyn da sauti me tsananin nutsuwa da sanyi yace

"Ummitah ta haihu ne???

Shiru sukai hawaye na gangarowa mama tana qanqame babyn jikinta.

Shiru ya dan yi yana jiran amsarta kafin ya sake cewa

"Ummitah kece?
Kin sauka dinne?

Kukane yake kokarin kwacewa mama ta miqawa Sayyid babyn wanda yaune ranar farko data shiga hannuwansa.

A tsananin taushin sautin dayake sake qara nauyin zuciyarsa yace

"Ummitah??

Kuka me qarfin gaske mama ta fashe dashi tana kasa riqewa sbd yanda yake ambatar Ummitan da bazata amsaba har abada sai lahira kila..
Chapter 32 · 0% Book details