← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 120

Sashe 88

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sayd na hangosa ya nufi waje da sauri kafin su iso ya tada mota tareda zuwa daf da kofar fitowa main palo ya tsaya Latif ne ya bude motar da sauri shima jikinsa na rawa.

Da mugun speed Sayd yabar harabar gidan da mota bayan securities sun bude musu gate tini.

Dr Sameera falaq tabi sbd yanda ta daga hankalinta ko anbarta kuka zataita yi.

Suna barin gidan Mama na isowa da sabon driver dinta yaje ya daukota Airport.

Cikin mamaki take tambayar Su jannah din da falaq Fiddausi ce ta sanar mata komai cikin mutuwar jiki.

Itama maman damuwa ta shiga tana fidda waya kiran AZIZ sedai harta yanke bai daga ba.

A asibiti suna isa da gaggawa akai emergency da jannah din wadda aka fara kokarin dawo da numfashinta da baya fita sukeyi.

Zaune yake a gurinda aka tanadar masa na jira Sayd na tsaye a bayansa yana kokarin neman hanyar da zasu samu history record na ciwonta sbd dole sai dashi zaa samu damar sanin yanda zaa bi da yanayinta.

Falaq na gefen Daddyn nata idanuwanta sunyi zuru na jiran tsammani.

Zaman awa kusan biyu zuwa uku sukai kowa da abinda yake zuciyarsa kafin Dr Sameera ta fito tareda wani dr Ashir
Ya kallesu yana jiran abinda zasu fada.

Numfashi sauke suna kallansa kafin cikin girmamawa da bayyanarda yanayin da ake ciki Dr Ashir dinne yace

"Numfashinta ya dawo hakama bugun zuciyar ya dan samu sedai ga dukkanin alamun da muka gani shine bugun zuciyarta is very weak wanda hakan na nuna Alamar heart patient ce so for now saita farfado munsan komai akan yanayinta zamu iya dubata dakyau,

Sai kuma hannunta da shima anriga an dubasa anji dashi insha Allah dan haka yanzu muyi fatan farfadowanta a lokaci"

Numfashi mara sauti sosai Sayd da Falaq suka sauke a lokaci daya yana kasa cewa komai.

Shi kuwa dago idanuwansa kadai yayi ya kalli Dr Ashir din a tsanake ya furta

"Thanks Doc"

Shiru sukai dukkaninsu kowannensu da tinanin dayake zuciyarsa sedai babu wanda yace komai sai falaq data lafe gefen jikinsa idanuwanta da jikinta sunyi sanyi.

Har dare bata farka ba dan haka ya buqaci su koma da ita gida a hakan aci gaba da bata kulawan a gida sbd babu yanda zaayi abarta asibiti ita kadai gashi har lokacin Zaadens basu saniba.

Ambulance ce ta dawo da ita gida a daren.

A dakinta aka kwatar da ita ya dauki nurses kwararri guda biyu dan kulawa da ita duk da ga mama ga Fiddausi amma dai nurses din sune zasufi sanin abinda ya kamata.

Saida aka gama mata komai aka falaq ce ta rufeta ta abin rufa me taushi ta zagaya ta kwanta gefenta sbd bazata taba iya kwana daban tabar Jannah a wannan halinba.

Shi kansa saida Falaq din tai bacci a gefen Jannah din kafin ya same sauke numfashi me dumi da gaba daya ayau din sai yanxu ya samu daman sauke numfashi.

Jannah ya saukarwa idanuwansa ya xubawa idanuwanta dake rufe ido yana kallan yanda sukai zurfi....

A bakinta daya bushe ya gangaro da idanuwansa ya zuba musu suma kafin ya dauke su ya maidasu akan hoton dayake bedside dinta a qaramin flame guda uku ajiye.

Hoton Daddynta ne na farkon shi kadai cikin Kamala da cika ido kaman asalin mutumin kirji..

Dauke idanuwansa yayi yana saukarwa akan dayan frame din hoton Mimi da Maheer da saleem ne da Ammar Dukansu da fararen shirts da blue jeans sai Ammar daya saka fcap.

Zubawa hoton karshe ido yayi wanda shine hoton Ammar Zad shi kadai sanye da Black Armanis.....

Tsayar da idanuwansa yayi akansa yana masa kallo biyu masu qarfin gaske na farkon shine kallansa a matsayin wanda ya kashe masa tasa yar uwar da hannuwansa ya zare zuciyarta daga kirjinta ya sakawa tasa macen wadda take matsayin Matarsa a yanzu amma hotonsa ne a gefen gadonta tana kwana dashi tana tashi dashi.

Miqewa yayi tareda ficewa a dakin yana bawa nurses daman su shiga su sake dubata kafin su wuce dakin da aka saukesu.

Kai tsaye hanyar palonsa y nufa yana sako kai ciki Fiddausi na ajiye tray din tea da zuman data kawo masa ta juyo ta fice cikeda girmamawa.

Kai tsaye Bedroom dinsa ya shige yana zare rigar jikinsa ya nufi hanyar toilet yana zare wandon yaja towel ya qarasa cikin toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa hannuwansa na dan yin rawa alaman yanayinsa zai motsa amma yana kokarin hana hakan.

Ya dade sosai a ciki yana fama kafin ya fito ya shirya cikin kayan bacci masu santsi da tsada ya haye gadonsa ya kwanta batareda yasha tea din da aka kawo masa ba sbd kansa dayayi nauyi.

Washe gari har 10 bai fito ba sbd ciwon kan daya tashi dashi dan haka sai guraren 11 ya fito kuma kai tsaye dining ya nufa.

Mama dake palo tareda fadilah kallo daya tai masa ta fahimci yanayinsa dan haka cikin kulawa ta amsa gaisuwansa batareda wani dogon zancen ba da zai iya kara masa ciwon kai.

Fadilah kuwa itace ta miqe tabisa har Dining tayi serving dinsa abinci cikin kulawa sosai da kokarin nuna kamun kanta.

Bai cika kallo ba dan haka bai wani yi mata kallan Arzikiba yafara breakfast dinsa a natse.

Falaq na dakin Jannah data farfado sedai kwata kwata ba karfi ko kadan a tareda ita hakama ga hannunta daya a daure bata iya komai dashi sedai da dayan.

A karo na kusan biyar falaq ta fito tana kokarin nufar palonsa sake dubosa Mama tace mata

"Ya fito yana dining room,yaya jikin jannah din??

Juyawa zuwa dining tayi cikin farin cikin son sanar dashi jan din ta farka tacewa mama

"Taji sauki wanka ma zatayi"

Hamdala mama ta sake yi sbd tin safe itama take yawon dakin har bayan farfadowan jannah din,

Dining room din take kokarin nufa sai gashi ya fito a natse kwarjinsa na sake cike idanuwan Fadilah da Fiddausi harma sa maman.

Kama hannunsa tayi cikeda murna tace

"Goodmorning Besty,
Albishirinka,My Jan ta farka tin dazu fa"

Kallanta yayi a natse batareda nuna mahimmancin zancen garesaba ya bude baki yace

"Hakanne ya sakaki farin ciki sosai haka???

Gyada kai tai da sauri tana sake riqesa tace

"Wanka ma takeson yi tin dazu sbd ta samu karfi kadan amma ta kasa cire kayanta sbd hannunta daya nima nayi na kasa tin dazu banason taci gaba da wahala so Muje ka tayata Daddy banason ta fama hannunta"

Tsit palon sukaj hadda Sayd dayake zaune gefen mama bai dagoba yaci gaba da duba abinda yake dubawa cikin ipad din hannunsa.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
72
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

***********
Mama dagowa tayi ta kalli falaq din kaman ta janyota ta bude kanta ta saka mata sanin ya kamata sbd kai tsaye take maganar komai bata tsayawa sanin me take fada ba ruwanta.

Fiddausi silalewa tayi ya koma kitchen,
Fadilah kuwa AZIZ din ta sata kallansa zuciyarta na harbawa sbd bata fatan ya ya tafi taimakawa jannah din sbd a sani da fahimtar dataiwa auren nasu da kyau da kyau bai taba kallan Jannah din a matsayin matarsa ba dan haka ba lallai sun taba samun intimacy ba.

Muskutawa ta dan yi kadan tareda kallan Falaq tana dan sake fuska tace

"Ayya ai duk bamu saniba da duka gami xamu taimaka mata,
Bara naje na taimaka mata din"

Miqewa take kokarin yi Falaq tai saurin cewa

"No,Daddy ne zai tafi ni banason kowa ya taimakawa Jannah daga ni sai Daddy se Fiddausi"

Da sauri fadilah tace

"To bari na kira Fiddausin taje ta taimaka matan"

"I said no banason kowa a yanzu,
Daddy ne zaije ai daman bai dubata ba yau da safen"

Mama da zancen yake neman sakata kunya kallan AZIZ din dayake barin palon xuwa hanyar nasa palon tace

"Kaje ka dubata mana AZIZ taji jiki fa yarinyar kuma ya kamata a sanar da iyayenta duk da zanji kunyar su ganta a yanda take yanzu"

Falaq da tini tai raurau zata fara masa kuka ya kalla yana juyawa zuwa hanyar dakin Jannah din da baida niyar sake shigansa.

Yana shiga dakin ta bude idanuwanta dake rufe ahankali ta kallo kofa tana motsawa kadan.

Ganinsa ya sanyata fara kokarin tashi zaune daga jinginen datake a tsakiyar gadon tanajin gabanta na dan faduwa da fargaba.

Kallo daya yayi mata ya dauke idanuwansa akanta yana Nufota.

Ganin ya nufota ya sakaya yaye rufanta tana ziro kafafunta kasa ta miqe hannuwanta na dan rawa sbd fargaba da shakkarsa data riga ta shigeta.

Yanda kafafunta ke rawa yasaka tsayuwar ta gagara tana neman zubewa ya sake riqota a karo na biyu yana kallan idanuwanta da itama shi ta dago tana kallo cikeda fargaban ko fada zaiyi mata.
Chapter 88 · 0% Book details