← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 120

Sashe 86

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin mama data shige tini ta fito duk suna palo cikin damuwa Fiddausi idanuwanta sunyi jajir sbd Kauna ce me karfi da shakuwa kamar uwa da 'ya itama a tsakaninta da falaq sbd shayar da ita ne kadai bataiba amma duk wata dawainiyar falaq itace meyi tin falaq na zanin jariranta.

Jannah ma a zaune take sanyaye zazzabi me karfi ne itama yake cinta na walaha.

A gidan dr Sameera ta kwana Sai Falaq ta farka.

Dr Sameera kwararriya akan aikinga kuma mace ce Kyakkyawa mai kyan jiki da tsari tareda ilimi sosai kuma tin ganin farko Allah itama ya jarabceta da kaunar AZIZ LIMBA wanda bai taba mata kallo biyu xuwa uku ba ko yau din datake cikin gidansa sbd 'yarsa.

A dakin Falaq dr Sameera ta kwana ya hana jannah kusantarta kwata kwata wadda ta kwana cikin damuwa da zazzabin da batada maganinsa.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
70
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*****************
Washe gari tinda safe Jannah ta nufi dakin Falaq kafin ya fito ta dubata bayan sun gaisa da dr Sameera wadda ke bin jannah din da kallo sbd sanin itace matar AZIZ LIMBA din.

Ta jima a dakin bayan ta dan tambayi dr Sameera din yanayin jikin falaq din ta bata tabbacin zata iya farkawa kowane lokaci.

Kasa komawa dakinta tai ta nufi dakin mama tai mata ina kwana mama ta sakata tai zamanta anan tai baccin safenta wanda bata samu tayiba da dare sbd cikin tsananin zazzabi da yunwa ta kwana.

Karfe goma da mintina ta farka ta sake zuwa dakin Falaq ta dubata kafin ta wuce dakinta tai wanka ta shirya ta fito tana waya da Maheer kafin ta kashe tana isa dakin falaq ta tarar da tana farkawa dan haka da sauri ta qarasa gareta tana zaunawa gefenta shima a daidai lokacin ya shigo a karo na babu adadi.

Falaq na ganinsa idanuwanta suka ciko da hawaye suna gangarowa..

Jannah ta zari tissue tana share mata hawayenta cikesa kulawa da kauna.

Dr Sameera ficewa tai a dakin aka barsu su kadai.

Miqewa jannah tai ta basa guri zata bar dakin Falaq ta kalleta tanason kiran sunanta amma bata iya bude bakinta sbd she's very weak.

Sake yunqurawa takeyi na son dawowan jannah din amma batada karfin hakan...

Ba tsammani jannah taji ankama hannunta cikin nutsuwa batareda ance komaiba.

Cak ta tsaya batareda ta juyoba sbd sanin shi dinne tinda basa tareda kowa a dakin hakama girman hannun da yanayin yanda dumin tafin hannunsa ya shigeta ya tabbatar mata da ba Falaq bace.

Shiru sukai dukansu kafin ta juyo ahankali tareda dagowa ta kallesa shi kuma bai juyo ya kalletaba falaq dake zubarda hawaye har lokacin yake kalla zuciyarsa na susa da kukan datake faman yi.

Sake mata hannu yayi Ahankali ganin ta fahimci abinda yake nufi ta koma dayan gefen Falaq din ta zauna tana cigaba da share mata hawayenta.

Zaunawa yayi Ahankali a sofa yana kallansu su duka biyun kallan nutsuwa kafin ya bude baki kai tsaye yace

"Falaq meyake damunki?
Meye kikewa wannan kukan?
Akwai abinda yake miki ciwo ne?

Girgiza kai tayi ahankali tana kallansa a marairaice.

Tea da abinci tareda ruwa me dumi Fiddausi ta shigo dashi ta ajiye a table wanda jannah ta zaunar da ita ta fara bata tanasha ahankali sbd akwai yunwa sosai a tareda ita.

Shiru yayi yana kallansu harta gama bata abincin tana goge mata baki kafin ta kamata suka shiga toilet shikuma ya dan fita sbd amsa waya a natse bayason hayaniya komai kankantarta a dakin falaq din sbd tattalin samun lafiyanta.

Ko tsayuwa Falaq din bata iyayi sbd idan aka samu collapse irin haka a ciwonsu dukkanin karfi da kuzarinka tafiya yake gaba dayansa sai bayan dan lokaci yake dawowa.

Wanka ta taimaka mata tayi wanda ya sakata jiqewa gabaki dayanta kayan jikinta suka jiqe sosai dan haka dole daga can itama rigar wankan falaq ta sako wadda tai mata kadan sosai duk da tayi mata amma tai mata guntuwa sosai dan kadan ta sauko a cinyoyinta hakama daga saman bata wani rufeta sosaiba amma bata damuba suka fito sbd ba kowa sai su kadai.

Falaq ta samu dan karfin jikinta sbd wankan ya dan sake mata jikinta dan haka itama rigar bathrobe din ce a jikinta amma ita sbd tata ce daidai tai mata ta rife mata yanda ya kamata.

Suna fitowa daga toilet taji sanyin Ac ya kado musu sosai har saida tsikar jikinta ta tashi ta kalli inda remote din yake tana dan sakin falaq ta nufesa dan rage sanyinsa sosai kodan falaq din da babu lafiya duk da itama bata wani son sanyin sosai.

Vibrating na waya taji daga bayanta wanda ya sakata juyawa da sauri tagansa a zaune yana kallan rigar dake jikinta a natse.

Kanta taji yayi mugun sarawa ta saki falaq gabaki daya tana kokarin juyawa daga ita har falaq din suka zame sbd da sakinta da yanda taja kafarta da sauri zata juya lokaci daya ta ja da kafar falaq din wadda batada karfi ko kadan dan haka baida zabin daya wuce taresu su biyun sedai ita yana tareda kofar toilet din ya koma da ita gabaki dayanta yana barin falaq wadda ya tsayar jikin bango sbd Sayd daya sako kai dakin tareda dr Sameera.

Falaq dake kusa kofar toilet din ta janyo tana kallan Sayd da Dr Sameera dake kallanta.

A cikin toilet din cikin zafi ya dago xai mata magana idaniwansa suka sauka akan gaban rigar data bube kadan Tabon aikinta seti da zuciyarta ya bayyana baro baro wanda ya saka zuciyarsa Skipping bugawa idanuwansa na kasa daukewa daga gurin har lokacin suna hade da junansu.

Yanda zuciyarta ke bugawa kirjinta na sama yana kasa ya xubawa dinkin setin zuciyarta tasa zuciyar na bugawa idanuwansa sunyi jajir.

Jin tai bugun zuciyar nata itama yana tsananta ta dago idanuwanta ahankali ta kallesa a lokacinda ba zato taji saukan tafin hannunsa akan zuciyarta wanda ya saka kirjinta bugawa da karfin gaske..

Bugun farko na zuciyar Ummitah dayaji a tafin hannunsa baisan lokacinda ya rintse idanuwansa ba yana sake matseta jikinsa hannunsa dake kan kirjinta yana wata irin rawa me sanyin data sakata kasa tsayuwa kafafunta na sanyi tana neman zubewa a gurin ya sake riqeta ajikinsa ruwan wankan jikinta na shigewa jikinsa.

Qwacewa tafara kokarin yi wanda ya sakasa bude idanuwansa da sukai jajir suka sauka akan fuskanta yana mata kallo tsanarta na gauraya zuciyarsa sbd Jin bugun zuciyar 'yar uwarsa a kirjinta ya dawo masa da radadin rashinta sabo a zuciyarsa.

Sakinta yayi batareda y dauke idanuwansa akantaba ta fadi qasan toilet hannunta na buguwa sosai amma bata dagoba ta kallesa duk da radadin datake ji hannun.

Rigar jikinsa ya zare ya jefa mata ya juya yabar toilet.

Sayd da baisan yana ciki ba yana ganinsa ko kofar toilet din bai sake kalla ba ya juya yabi bayansa batareda ya sake cewa komaiba akan maganar dayake yi da dr Sameera akan ciwon falaq dayake gabatar mata da record dinta na komai.

Dr Sameera itama kasa cewa komai tayi tabi bayansa da kallo Bugun tata zuciyar itama yana qaruwa sbd ganin lafiyayyar farar fatarsa dake daukan ido da kakkarfan jikinsa daya gama budewa sbd geamin.

Falaq kuwa kofar toilet ta xubawa ido tana jiran fitowan Jannah wadda hannunta ke mata tsananin azaba.

Hawaye ta fara sharewa kafin ta miqe ta iya saka rigar da kyar ta fito.

Juyowa dr Sameera tai tana kallanta da sauri sedai ta boye mamakinta har Jannah din taje ta dauki wani abu a cikin kayan falaq ta daura a jikinta ta fice ta nufi dakinta hannunta na mata wani irin ciwo.

Tana isa dakinta kayan jikinta ta cire daqyar ta iya saka wasu kayan sai kawai ta zauna ta fasa kukan azaba da damuwan datake ranta.

Sai datai sallan azahar ta fito jiki a mace taje ta sake duba falaq ta gaida mama ta koma daki.

Bata fito cin abincin rana ba sedai Fiddausi takai mata daki.

Bata iya cin komaiba kwance taje tana fama da wani irin azababben ciwon hannu da zazzabi.

Sai yamma ta fito taje gurin falaq data warware ba laifi.

A gurinta ta zauna duk da tana jin jikinta bata nuna ba ta jin dadi ba ta ringa kulawa da Falaq din har dare ta lallaba ta koma daki ta kwanta.

Washe gari falaq ta tashi lafiya kalau kaman batai ciwoba sedai fushi take da daddynta tace saiya shirya da Jannah.

Jannah ahankali ciwon yafara cin karfinta har lokacin ita kadaice take wahalanta a daki bata iya bacci kwana takeyi tana kukan azaba da damuwa batareda sanin kowaba.

A haka su anty maryam suka taho gidan duba falaq itada babbar yarta Fadilah wadda ta gama service dinta aiki mamanta keso tayi a karkashin AZIZ wanda baa riga anfadawa ba amma dai ta saka Alh saad ya masa magana.
Chapter 86 · 0% Book details