← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 120

Sashe 111

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ticket din ta zare ahankali daga cikin passport din ta yagasa cikin sanyi ta zubar a tsakiyarsu ta rintse idanuwanta hawayen dake ciki suka gangaro tace

"AZIZ LIMBA na zabi ahalina,
Na bar limbas,
Na hakura da auren Limbas dayake kaina,
Na zabi rayuwa batareda kaiba na zabi familyna a kowane hali suke ciki zan tsaya tareda su ina fatan kowannenmu ya samu abinda rayuwa zata daidaita masa a gaba"

Katseta yayi ta hanyar kama hannuwanta duka biyu da nasa hannuwan yana buki zaiyi magana ta zame hannunta daya ta rufe masa baki da tafin hannunta tana girgiza masa kai sbd har cikin zuciyarta ta ciresa ta hakura ta zabi familynta sbd har abada shi da ahalinta bazaa taba zamowa daya ba dan haka gwara kowa ya zaba nasa yayi rayuwarsa.

Hannunsa ya dora akan nata yana bude baki Ahankali da nauyi a muryansa sosai yace

"Nayiwa falaq Alkawarin bazan taba tirsasaki ba har abada,
Alkawarinta ne akaina wanda bazai taba barin nayi miki dole ba hakama na alkawarine akaina na cika miki zabinki batareda tilastawa ba,
Karki zabi abinda zai kawo karshen rayuwarda baa riga ma anfaraba,
Ki......."

Katsesa tayi ta hanyar girgiza kanta hawaye masu zafi na tsananta gudu akan fuskanta ta bude baki muryanta na bayyanarda tsananin radadi tace

"Na zabi ahalina har a yanzu,
Bazan taba barinsu na bika ba AZIZ LIMBA,
Na zabesu,zan kuma sake zabarsu,zanci gaba da zabarsu har karshen rayuwata"

Qarasa maganar tai kuka me tsananin ciwo na zuwar mata ta soka kanta cikin qafafunta tanayinsa ahankali zuciyarta na tsananin ciwo da radadi me girma.

Shima radadi me zafi da ciwon gaske kirjinsa ke masa idanuwanta na qara wani irin jajir hannuwansa suka fara rawa ya miqe ahankali baice komaiba ya nufi kofa ya fice yana sakawa ransa zai bata yancin datake so na har abada sbd Allah dai ya nufa alaqarsu ta qare daga nan,

Hakama rabuwa da ita a yanzu shine mafi alkhairi garesu su dukan sbd a duk lokacinda ya kalli halin da falaq take ciki jin yakeyi kaman bazai iya hakura da abinda Zaadens sukai masa ba zai iya kashe daya daga cikinsu dan raya tasa 'yar shima dan haka nesantar junan shine mafi alkhairi garesu duka suna buqatan break daga wannan masifar ta rayuwa.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
91
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

*************
Yana ficewa daga palon koda ya isa mota ko gani bayayi sosai kirjinsa tsananin ciwo yakeyi da sauri Sayd ya bude masa mota yana kasa kara kallansa sbd yanayinsa dayake a munane.

Barin gidan sukai yana dafe kirjinsa dake neman bugawa radadin gaske yakeji yana kasa riqe ciwon yafara neman numfashinsa dayake yankewa yana damqe hannuwansa da karfi idanuwansa na kasa riqe azabar kirjinsa nasa...

Itama yana ficewa ta zabe qasa ta zube tana fasa wani irin azababben kuka me kargin gaske tana dafe kirjinta dayake mata tsananin ciwon dayafi na koyaushe tana jin kaman zata mutu....

Har cikin ruhinta take jin azabar da kirjinta keyi tana tsananta kukan da batada me rarrashi,

Batada wanda zai ko tsaya akanta ta samu sassaucin qunci da ciwon datake ji a lokacin na zabar rabuwa da namijin ta jure komai akansa,

Inama tin farkon haduwarta dashi ta jure ta danne sonsa da bata iso wannan matakinba da ayau take jin inama tabar duniya.

Su kuwa suna isa gida kai tsaye bangarensa ya wuce batareda ya bari kowa yaga yanayin dayake ciki ba yana shiga tin a kofa ya zube qasa yana dafe kirjinsa dayake masa azabar dabazai iya daukaba,

Wasu irin hawaye ne suka gangaro daga idanuwansa masu tsananin zafi yana zubewa qasa kwance har lokacin hannuwansa na dafe da kirjinsa....

A daidai wannan lokacin Sayd ya shigo sbd tin a mota ya lura da yana cikin mummunan hali..

Sayd na shigo wani irin jini na fesowa ta bakinsa me karfin gaske idanuwansa na rufewa.....

Cikin matsanancin tashin hankalin daya saka kafafunta Sayd sarewa ya isa garesa da rarrafe hannuwansa na rawa ya ambaci sunansa da karfin daya saka duka jamaar gidan fitowa.

Mama na ganin AZIZ din da jini kasa qarasowa tayi itama jiri ya debeta ta zube a inda take.

Shi kansa Sayd bazai iya tuqi ba sbd mummunan halinda ya shiga dan haka ambulance aka kira babu dadewa sosai ta iso aka kwashesa zuwa asibitin harma da mama wadda itama manyanci da ciwon damuwa suka hade suna neman qarasata.

Fiddausi da Sayd ne a tsaye kawai kaf familyn sai baba alhassan wanda shima dole damuwa ta tada nasa jikin da ake lallabawa.

Se cikin dare aka samu Bugun zuciyarsa da numfashinsa suka dawo daidai sedai shima take ciwo ya qarasa maidasa abin tausayi sbd baisan waye ma yake kansa.

Sayd da damuwa take neman kashesa shi kadai tini ya qarasa hada kan komai nasu a cikin kwana biyu ya gama handling komai akai sabbin presidents da chairmans da directors a companies dinsu ya qarasa handing over na komai ga latif,

Securities ma da masu aiki na Mansion din dukkaninsu babu wanda baa bawa manyan kudaden da zai jima bai nemaba aka sallamesu duka kowa da kowa.

Washe gari zasu tafiyarsu subar qasar dan haka a daren Motar Sayd ta tsaya a kofar gate din Zaadens ya fito mota ya bude gate da kansa ya shigo sbd babu securities kamar zaadens din baya sai mai gadi daya wanda shima ya kasa tafiya ne yabar jannah kaman yanda me aiki daya ta tsaya shima tsayawa yayi.

Harabar gidan a kwai haske amma kamar baya ba,
Sanyi jikinsa yayi shima sosai farkon zuwansu Zaadens na dawo masa a lokacinda kowa na cikeda lafiya da kwanciyar hankali da burirrika amma ayau dagasu har su din kowa ya rasa abubuwa da dama da har abada bazasu taba dawowa ba.

A kofar palon ya tsaya ya miqa hannunsa ahankali yayi knocking idanuwansa jajir.

Shiru babu motsin kowa,
Sake bugawa yayi yana dan ja baya kadan...shiru baa budeba dan haka ya sake bugawa yana ci gaba da bugawa a natse cikin sanyi.

Shiru kusan tsawok lokaci me tsayi,
Ajiyar zuciya da numfashi me zafi ya sauke yana juyawa xai bar gidan aka bude kofar ahankali cikin nutsuwa da sanyi.

Me aikice ta bude kofar cikin fargaba a sanyaye.

Juyowa yayi ya kalleta itama shi take kalla cikeda damuwa.

Bude baki tayi tace

"Barka da zuwa"

Amsawa yayi yana sauke kallansa daga kanta yace

"Ms jannah nakeson gani"

Shiru tayi tsawon seconds kafin tace

"Batada lafiya amma bismillah bari na sanar mata"

Shigowa yayi ya zauna a natse a palon kansa qasa idanuwansa har lokacin jajir.

Wucewa tayi ciki ita kuma zuwa dakin jannah dake kwance shiru idanuwanta rufe.

Bude dakin tayi ahankali ta shigo da sallama me sanyi sbd tasan ko tayi knocking jannah bazata iya maganar cewa ta shigoba bare tasowa ta bude din.

Cikin nutsuwa da sanyi tace

"Sir Sayd daga Limba yazo yana son ganinki"

Bude idanuwanta tayi ahankali batareda ta motsaba.

Sake maimaitawa me aikin tayi kafin ta juya ta fice daga dakin.

Shiru shiru bata fito ba tsawon lokaci kafin ta bude dakin ta fito sanye da doguwar hijab har qasa fuskanta ta rame sosai tayi haske sosai.

A hankali ta tako ta iso palon ta zauna a natse batada karfi ko kadan sbd ciwon dayake tattareda ita tsawon kwanakin.

Nunfashi ya sauke ahankali sbd shiru sukai dukkaninsu babu wanda yace komai.

Dagowa yayi Ahankali ya kalleta zuciyarsa na cika da damuwa me tsanani gaske ya zura hannunsa cikin aljihun qatuwar jacket din dake jikinsa ya ciro daguwar envelope din datake sealed ya miqe ahankali ya isa gabanta ya ajiye mata muryansa na wata irin sanyi me tsananin gaske sbd damuwar datake rinjiyarsa yace

"Daga AZIZ LIMBA.......""

Rintse idanuwanta tayi ahankali wani mashi me tsananin zafi na sukar tsakiyar kirjinta ta dora hannunta akan kirjin ahankali tana karban azabar datajin da dukkanin imaninta kafin ta miqa hannunta dayake rawa ta dora akan tanardar ta dauka tareda dago idanuwanta da sukai jajir ta kalli Sayd din ta bude baki Ahankali tace

"Thank you for everything"

Rintse idanuwansa yayi yana juyawa ya fice yana fatar Allah ya kawo musu sassauci su duka.

Yana ficewa damqe takardar tayi a cikin hannunta tana son fashewa da kuka amma sam babusa hawayen sun qafe sai jajayen ido.

Miqewa tayi daqyar tana hada hanya bata gani ta isa dakinta ta daga takardar tana son budewa ta karanta yanda aurenta ya mutu amma idanuwanta ma ganinsu daukewa yayi jin take tana neman mutuwa,

Da rarrafe ta isa gurinda jakarta take ta bude ta saka takardar a ciki tana zamewa qasa....

Idan lissafinta yaje daidai a date din dayake jikin ticket dayazo dashi a ranar gobe ne tafiyarsu tafiya ta har abada ba dawowa kila.

Silalewa qasa tayi yana kwantawa tareda rufe idanuwanta ahankali tana hadiye duk wani qunci da ciwo.

Karfe goma sha biyu saura Ta isa asibiti a lokacin data san babu kowa a asibitin tareda Falaq sai Fiddausi.

Ko data isa itama a cikin ciwo da rashin karfi take amma zuciyarta na tsananin son yiwa falaq ganin karshe..

Tana shiga dakin Fiddausi dake zaune ta gama sallah tana addua tana ganinta ta miqe da sauri suka rungume juna tana fashewa da kuka itama jannah din fashewa da kuka tai tana kallan fuskan Falaq data koma kaman babu nama a cikinta anma rufeta sosai baa wani budewa.

Sosai suka jima a hakan kafin jannah ta isa ga Falaq ta rungumeta ahankali tana shafa fuskanta tana kuka sosai hawayenta na lalata fuskanta gabaki daya.
Chapter 111 · 0% Book details