← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 120

Sashe 68

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallansa dad yayi yana kasa riqe abinda yake ransa,
A matsayinsa na mahaifin da zai iya zubar da mutuncinsa akan yarsa indai zata samu farin ciki baya duba komai da kowa dan haka ya ajiye maganar auren da zaa daura a goben nata yace

"LIMBA a matsayina na uba ina maka tayin auren 'yata sbd son da kukewa junanku.....

Kallansa AZIZ ya juyo yayi yana bayyanar da mamakinsa kadan yace

"Kanada wata 'yar ne?
Ban taba son kowace mace ba a duniya bayan mahaifiyata d mahaifiyar Falaq sai mama da falaq,
Su kadaine matan da AZIZ LIMBA ya taba so yake kuma so,
So bansan wace 'yar kake magana ba coz i thought you only had one daughter wadda zaa daurawa aure gobe."

Kallan Maheer yayi lokacin dayake qarasa maganarsa alaman ko akwai wata yar?

Wani rikitaccen numfashi dad ya sauke hakama maheer rasa abin fada yayi sbd basu taba sanin akwai wanda zai iya fadar magana kai tsaye haka ba akan fuskansu.

Rikicewa maheer yayi zuciyarsa na tsananin zafi da baqin cikin cin fuskan da maganar AZIZ din dan haka ya bude baki zaiyi magana Dad da jininsa yake dan hawa ya dakatar dashi sbd basuda zabin daya wuce daidaitawa dashi ya karbi auren rinda jannah na tsananin sonsa kafin gobe farin cikinta ya lalace idan ta rasashi gaba daya.

Daidaita kai dad yayi cikin nutsuwa da nuna mahimmancin zancen yace

"Duk da hakan ni a matsayina na ubanta na baka aurenta idan har zaka amsa sbd kaunar datake tsakaninmu"

Dan gajeran murmushi me kyau da nutsuwa ya sake kai tsaye cikin steez yace

"No,thank you"

Wani irin zufa ne ya tsinkowa dad din yana kallan AZIZ din wanda kai tsaye yake maganarsa hankali kwance ba kawaici ko daya.

Maheer kuwa kirjinsa yaji ya toshe y kasa furta komai.

Qamshin jannah dinne me shegen dadi da nutsuwa yafara shigowa palon kafin ta sako kai palon cikin riga da skirt na wani plain lace mara nauyi d tsada ya zauna daidai jikinta komai nata ya fito d kyau.

Batasan yana palon ba dan haka ko dankwali babu a kanta dayake daure amma y dan yamutse kadin sbd falaq dake shafa mata shi tin dazu.

Magana zatai idanuwanta suka sauka akansa daidai lokacin shima ya dago amma sam idanuwansa basu sauka akanta ba wayarsa ya daga.

Cak maganarta ta dauke kirjinta ya buga da karfi ta kasa cewa komai saidata hadiye wani nauyin kirji kafin ta bude baki tace

"Dinner Dad"

Gyada mata kai yayi sbd shima ya kasa iya maganar.

Miqewa dad din yayi yayi gaba jikinsa duk a mace sbd sedai a daga daurin auren nan zuwa gaba amma bazaa iya daurasa ba tausayin yarsa yakeji sbd ko yanzu shi kadai yasan meya gani a idanuwanta lokacinda taga AZIZ din.

Maheer dayake jin yan suffocating da sauri ya wuce dad ya fice dad na bayansa.

Itace a bayansu tana kokarin bin bayansu ba tsammani abinda bata taba jib taji an riqo hannunta ta baya.

Cak zuciyarta da dena bugawa numfashinta na kokarin daukewa sbd tsananin shock da mamaki.

Kasa juyowa tayi sbd gap take da samun attack sbd qamshinsa dayake shiga hancinta direct daga jikinsa.

Attack yakeson bata sbd bayason barin gidan ayau sai yasan waye asalin likitan dasuke son sani sbd idan ba sauri yayiba aikinsa zai dade akansu gashi plans na sauyawa aurenta yana neman shigowa ciki bayan babu wannan banzan tsarin ko kadan a cikin plans nasa dan haka samun attack dinta a yanzu shine daidai lokacinda ya kamata ya san abinda yakeson sani.

Juyowa yayi da ita suna fuskantar juna a zuba mata idanuwansa tareda yiwa hannunta wani irin riqon daya saka zuciyarta kasa riqe bugawan ta dago idanuwanta ta zuba masa take taji tana samun attack ta zube a gurin.

Tsallaketa yayi ya fice daga palon daidai nan falaq tazo kiranta kafin tace masa komai ta hango jannah a qasa zube tana neman numfashinta dayake kakarin barin jikinta d qarfi ta kira sunant wanda ya saka kowa dawowa da sauri anayi kan Jannah din cikin matsanancin tashin hankali.

Dad da maheer ne alokacin daya sukacewa Mimi

"Ina Ammar ayi sauri a kirasa da gaggawa...."

Mimi ma cikin tashin hankalin ta saka kiran wayarsa tana cewa

"Ammar kayi sauri jannah is having an attack "

AZIZ da Sayd da sukai mutuwar tsaye suna jiran zuwan Ammar din wanda yazo da mugun sauri daman yana cikin gidan dawowansa kenan yana harabar gidan.

Yana shigowa da sauri ya dauketa cak ya kwantar a kujeran palon ya miqa hannuwansa biyu duka zai bude rigarta dan fara duba bugun zuciyarta aka riqe hannuwan nasa duka biyu cak.

Da wani irin tsananin mamaki da tashin hankali ya juyo.

Sayd ne y riqe hannuwansa yana kallansa.

Kusan kowa dauke wuta yayi a gurin sbd mamaki da tashin hankalin halinda jannah din ke ciki.

AZIZ ne ya tako a hankali cikin isa ya tsaya gaban dad ya kallesa yace

"Idan nace na karba auren daka bani nata kana ganin ya dace shi wannan din ya bude jikinta anan ya tabata?
Dan haka bazai tabataba a nemo likita,
Yana dora hannunsa akanta bazan taba aurentaba har abada."

Cikin wani irin mummunan tashin hankali da shock Ammar ya kalli AZIZ din mimi ma shock din t shiga da tashin hankalin tana kallansa hankali kwance yayi maganar babu damuwar komai aransa dan badan zuciyar dake bugawa a kirjinta ba bazaiqi ta buga a yanzu ta mutu a gurinba.

Sayd sakin hannuwan Ammar yayi yana matsawa baya.

Cikin tsananin fushi da kansa dayake neman juyewa Ammar ya miqa hannunsa zau bude rigar Maheer ya riqe hannunsa da sauri yana Girgiza masai.

Dad kuwa cikin jininsa dayake neman hayewa cikin damuwa me tsanani ya kalli AZIZ yace

"Likatane shi kansa din Dr Ammar Zad
Shine likitanta tin b yanzu ba zai dubata ne a matsayin likita ba wani abinba daban........

Dago idanuwansa yayi ya zubawa dad din sbd daga karshe dai sun fada abinda yakeson tabbatarwa.

Ammar din ya yiwa wani kallan daya saka Mimi zubewa zaune sbd jirim dayake dibanta.

Irin kallan da yayiwa Ammar shi ya yiwa dad da maheer kafin ya hadiye wutar dake cin zuciyarsa ya bude baki yace

"Na karba sadakarka a goben zan aureta a matsayin uwar da Falaq takeso"

Juyawa yayi yabar palon sayd ya kama hannun falaq dake riqe dana jannah din suka bi bayansa daman mama na can palon take Fiddausi na ganin fitowarsu ta kirata suka bar gidan AZIZ din da kansa yace mata ta shirya gobe zaa daura masa auren datake so.

A cikin palon Kuwa wani masifaffen tension ne me karfim gaske ya cike gurin sbd Ammar kasa motsawa yayi idanuwansa akan maheer dayake riqe da hannuwansa.

Mimi kuwa jin tayi numfashinta yana neman daukewa itama
Dad dinma jininsa sama ya ringa yi yana kasa kallan Ammar sbd bai san AZIZ zaiyi magana a gaban Ammar din ba.
#MAMUH
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
56
Falaq farin cikine ya ciketa gabaki daya na jin Daddynta zai aura Jannah dan haka a mota qanqame hannunsa tayi tana bayyanar da farin cikinta ta kalli fuskansa da babu alamar farin ciki ko kadan a kanta tace

"I love you Daddy"

Juyowa yayi a hankali cikin nutsuwa ya saukar da idanuwansa akanta yana karantar asalin farin cikin me tsanani dayake bayyane akan fuskanta tana murmushi tana jin kaman tin yau ta tafi da jannah din gidansu.

Sayd dayake gaba shiru yayi yana sauraransu ta wani bangaren kuma shima hakan shine abinda yake tsananin so wato rabo zuciyar Ummitah daga zaadens sbd kada ta gurbata kaman yanda duka zuciyar familyn take a gurbace,
Babban fatarsa kafin su illata familyn ya zama zuciyar Ummitah tana tareda su dan haka shi wannan hukuncin shine daidai garesa kuma abinda yake jira dan haka daga lokacinda akai auren ta gama shigowa hannunsu komai ya nutsu to lokacin tarwatsa familyn zai fara duk da suna nan suna tsananin neman Dr ken wanda shi sukeson ya shiga hannunsa kafin komai sbd shine ya basu Ummitah,
Sunason Farawa Dasu dr Abraham amma kuma dole saisun fara kama dr ken sbd shine komai ya fito ta hannunsa dan haka nemansa suke sosai saidashi komai zai tafi yanda akeso.

Mama kuwa jin tayi zuciyarta kaman ta zuba ruwa a qasa tasha dan haka koda suka isa gida kasa shirin bacci tayi ta zauna tahau wayoyi.

Anty maryam ta fara kira akan lefen datakeson a hada mata na gani na fada a qanqanin lokaci.

Anty maryam na jin maganar auren farin ciki me tsanani da mamaki me girma suka rufeta lokaci daya da kuma Acikin yayanta dataita kwadayin ya auri daya amma duk da hakan farin ciki sosai tayi ta matsu goben tayi su isa LIMBAs din.

Baba alhassan ma daman yana nan har lokacin dan hana mama na sanar masa Sayd ya kira yaji komai daga bakinsa sbd AZIZ din ya shige ya hana kowa sake ganinsa sbd tsananin zafin kansa dayakeji yana jin kaman hakan bai kamata ba ga UMMITANSA to amma yana tsananin buqatan zuciyar Ummitah a kusa dashi.

Ruwa ne ya sakarwa kansa batareda ya cire kayan jikinsa idanuwansa a rufe ya qanqame jikinsa yanajin kaman kansa zai juye sbd tsananin zafin dayake tashi a cikinsa,

Yana tsananin qin Zaadens da jannah din kanta tsana me tsananin gaske da zai iya komai dan faduwarsu koda hakan na nufin su fadi tare,
Ta bagare daya yana tsananin Kaunar duk abinda ya shafi Ummitah koda qazantace indai ta Ummitah ce sonta yake da gaske,
Baitaba qi ko gudun abinda ya shafi Ummitah ba,
Ta bar duniya bazata taba dawowa har abada amma zuciyarta na duniya taba bugawa tayaya zai tsani kirjin da zuciyar Ummitah take bugawa a cikinta????

Zuciyarsa ta kasa hakan,
Ya tsani jannah tsana mafi muni a lokaci day kuma yana tsananin kaunar zuciyar datake bugawa a kirjinta....

Rawa jikinsa yakeyi sosai yana wani irin jijjiga yana sake qanqame jikinsa da karfi sbd trauma dinsa da shima babu lokacinda bata tashi idan ya samu kansa a cikin wannan tsananin ciwo da radadin tinanin kauna da tsana dake cinsa lokaci daya wanda babu wanda ya taba sanin da hakan.
Chapter 68 · 0% Book details