← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 120

Sashe 4

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haihuwar Jannah zadeens itace babban Farin cikin daya cike gaba daya rayuwar ahalin gabaki dayanta dama duk wanda yake muaamala da huldan business dasu,
Duk wanda yake aiki a karkashinsu ma yayi farin cikin samun jannah sbd tayasu farin ciki dan haka tin tana jaririyarta duniya tasan da irin tsananin son da Ake mata,
Duniya ta sheda jannah zadeen itace hasken idaniya da rayuwar ZADEEN's.

Rayuwarsu ta dawo kamar sabuwar duniya da suke barewa a leda yanzu,
A baya komai ma wasa ne a yanzu ne ZADEEN's ke sake zamowa ZADEEN's da kowa yake shakka gashi daddy mahmoud ma ya dawo da familynsa sun hade sun sake bunqasar datake bawa mutane tsoronsu amma har lokacin matarsa shi bata haihuba amma bai wani damuba sbd yayan 'dan uwansa da Ammar dan zayneb sun ishesa.

*******A DAYA BANGERN KUWA CAN BAYA.

Kauyen Bondi Ruwa akeyi sosai tsakiyar dare guraren karfe daya da rabi gari yayi tsit babu kowa babu komai bayan ruwan da suke sauka sosai da karfi.

Qaramin gidan ne sosai wanda rabinsa yake a zube katangar ruwa ya zubar tintini.

Dayan bangaren da bai fadi ba daki daya ne sai qaramin ban daki wanda shima rabinsa ya zube buhu ne a rufe da rabin,

A cikin dakin macen datake kwance tana hada wani irin zufa me tsananin gaske duk da sanyin ruwan da akeyi yana zubowa cikin dakin daga sama sbd gefe daya langa langar dakin ya bude.

Dan ta dake gefenta idanuwansa sunyi jajir sbd tsananin dacin ganin mahaifiyar tasa a hakan.

Tsohon cikin dayake jikinta ya kalla idanuwansa suka sake kadawa sbd damuwa da dacin a halinda mahaifiyarsa zata haifo masa kaninsa ko kanwarsa.

Hannuwansa ya miqa ahankali ya janyo zanin da bayada sanyi ya rufawa Umman tasa ya bude bakinsa da muryansa me sanyi yace

"Umma sannu"

Kasa magana tayi sbd wani tsananin azababben ciwon marar daya taso mata tanaji jini na balle mata amma ta danne cikin tsananin azabar da bata taba jinta ba sbd batason daga hankalin 'danta dayake shi kadai hasken rayuwarta da batada kowa sai shi hakama batason ya gani ya duk da tasan duk ayita a qare shine zai tayata haihuwar kila tinda batada me taimakonta a rayuwar nan yanxu bayan shi data haifa.

Daqyar ta iya bude idanuwanta da sukai tsananin nauyi ta kalli farar fuskansa ta asalin fulani da dasashiyar murya tace

"ABDULAZIZ"

kasa dagowa yayi ya kalleta sbd hawayen da suka ciko idanuwansa yanajin duk duniya babu abinda ya tsana kamar dangin mahaifinsa da suka kasa taimakon mahifiyarsa bayan rasuwar mahaifinsu.

Numfashi take kokarin saukewa cikin azaba sbd sanin taurin zuciya irin ta ABDULAZIZ har abada bazai taba so da kaunar ko mutum daya a cikin dangin mahaifinsa ba dan duk da abinda ya tsana da gaske yake tsanarsa.

Jini ne ruwan dayake zubo musu ya gangaro daga karkashin Umman.

Jajayen idanuwansa ya dago cikin duhun daren zaiyi magana sai kawai umman ta masa wata irin riqo me qarfin gaske tana rintse idanuwanta cikin azabar gaske tayi wani irin nishi take ta haifo abinda yake cikinta.

Hawayen azabar ne suka gangaro musu shida umman a tare sbd irin riqon datai masa amma jin kukan jaririyar ya sakasa bude idanuwansa duk da baya ganin komai sosai ya sunkuyar da kai yana Godewa Allah cikin hawaye duk da ba wasu shekaru ne dashi ba sosai iyakacinsa shekaru goma sha hudu.

Batason abinda zai saka Abdul din yasan meyake wakana dan haka ta dade da tanadar rezanta dan haka da kanta ta yanke cibiyar ta dauki yar hannunta na rawa da hannu ta shafa gabanta taji mace ce dan haka yaye zanin daya rufa mata ta saka yar a ciki ta miqa masa tana numfashi daqyar sbd jinin dayake neman bugar da ita.

Hannuwansa rawa sukeyi sosai ya karbeta tana bude idanuwansa sosai a cikin duhun dan yaga halinda umman take ciki amma baya ganin komai.

Shiru dakin ya sake dauka yana rungume da yar yana jin wani irin tsananin so da kaunarta da yakejin ko rayuwarsa zai iya badawa dan bata kariya itada ummansa.

Kanwarsa ce uwa daya ta haifesa hakama daga tsotsan uba daya suka fito kuma batada kowa bayan shi da umman,
Hakama ummansa batada kowa sai shi,
Shine zai zama gatanta itada umma koda kuwa zai rasa ransa to tabbasa zaiyi gwagwarmaya dan inganta rayuwar su biyun nan.

Guraren asuba ruwan saman ya dauke dan haka ya ciro yarinyar daga jikinsa ya kwantar gefen umman ya fita cikin duhun ya nufi can karshen kauyen gurin macen da ita kadaice aminyar mahaifiyarsa duk kauyen kuma ita kadai take taimaka musu.
#MAMUH
#AZIZ AY LIMBA
#BESTLOVE
#BESTSTORY
#HEARTTRANSPLANT
#JANNAH ZADEENS
#UMMITA LIMBA

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar

4
*ZUZEAMVENTURES*
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

*************
Duk duhu da tsit din daren baitaba jin tsoronsu ba dan a haka ya taso komai dare haka yake ratsasa gurin nemowa ummansa Abincin da zata sakawa cikinta sbd ita da babyn datake cikinta su rayu.

Tafiya yayi mai nisa kafin ya isa gidan da zashi din,

Kofar gidan ya tsaya idanuwansa da sukai jajir ya dago ya kalli kofar gidan yana jin zuciyarsa na quna sbd baida ikon buga kofar bisa ga dokar mai gidan,

Ya saba komai dare haka yake zuwa ya buga kofar gidan idan mahaifiyarsa bata lafiya sbd Mama Sakina taje ta taimaka mata,
Mama sakina kuwa komai dare yaxo ya buqaceta bata taba fashin xuwa komai fadan da mijinta zaiyi kuwa,

Duk masifarsa da tsanar da yayiwa Abdul din da mahaifiyarsa sbd sun hanasa kwanciyar hankali da masifar rayuwarsu amma hakan bai taba saka sakina janyewa daga garesu ba sbd kauna ce sosai a tsakaninta da Fatimar da bazata iya barinta a mummunan halinda take ciki ba itada Abdul.

Ba so daya ba mijinta ya saba yiwa Abdul din dukan tsiya sosai akan zuwar masa gida tsakiyar dare.

Zafafan hawaye ne suka cika idanuwansa yana kallan kofar gidan kaman zuciyarsa zata fashe da ciwo da radadin bazai iya kiran Mama sakinar ba dan yana taba kofar gidan baba ilan dukan da bazai iya bawa ummansa kulawa ba a yanzu datake tsananin buqatansa zai masa shikuma bazai iya barin komai ya samesaba a yanzu dayake son kulawa da umman da 'yar data haifo musu.

Gefen kofar gidan ya koma kadan ahankali ya durqusa yana sunkuyar da kansa qasa dan jiran ayi kiran asubar da yasan lokaci yayi insha Allah.

Wani irin sanyi ake kadawa sosai
Sauran ruwan da aka dan dauke suna yayyafowa akansa ahankali suna ratsasa amma bai ko matsaba bare alamar tashi bakin kofar gidan.

Jiran kusan awa daya da mintina yayi kafin masallaci daya kwal dayake kauyen suka rangada kiran sallan daya sakasa miqewa da dauri kafafunsa da sukai wani irin riqewa suka kasa daukansa ya zube a gurin cikin ruwa da lakar datake lalace sosai da kofar gidan.

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa data fara bushewa tin yana karamin nasa ta masa wani irin nauyi yana jin kirjinsa na masa ciwo.

Hawaye masu dumi ne suka gangaro masa ya dafa yana kokarin miqewa aka bude kofar gidan.

Baba ila ne da babban dansa dayake uztaz wanda shi yake sako uban nasa gaba zuwa masallaci lokutan asuba a gida yake sallan baya zuwa masallaci da asuba.

Bude kananun idanuwansa masu kama da kamar an kashe kwarkwata ya waresu akan Abdul din duk da akwai duhu sosai har lokacin amma baya buqatan wahalarda kansa gurin sanin waye dan kai tsaye yasan baida tsohon dan iskan dazai zuwar masa gida bayan Abdul din wanda yake fatar Allah ya nuna masa sunbi duniya sunbar kauyen ko gidansa zai huta da maitar Abdul din.

Cikin zafin rai ya harbi Abdul din da kafarsa yana cewa

"Uban waye a kafar gidana cikin duhun nan??

Cikinsa daya harba ya dafe da hannunsa daya yana dagowa cikin tsananin azaba ya dafa hannunsa daya ya miqe yana kokarin bude baki zaiyi magana Baba ilan ya rigasa da cewa

"Nace uban waye ne a gurin?

Gali dayake gefen baban fitilar hannunsa ya kunna yana haske Abdul din da ita cikeda mamakin ganinsa duk da yasan yana zuwan amma a cikin ruwa da sanyin nan me yakeyi a kofar gidan wanda da alama ya dan jima.
Chapter 4 · 0% Book details